Iran Da Burkina Faso Sun Tattauna Kan Aiki Tare A UNGA

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun tattauna kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amura da suke faruwa

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun tattauna kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amura da suke faruwa a yammacin Asia. A tattaunawar Aragchi ya godewa kasar Burkina faso da halattar taron girmama Imam Sayyid Aliyul Khaminaei (q) shahida, wanda Amurka da HKI suka kashe a ranar 28 ga watan Fabray ru na wannan shekarar.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Burkina Faso Karamoko Jean-Marie Traore a gefen taron babban zauren MDD a birnin NewYork.

Ya kammala da cewa JMI tana son karfafa dankon zumunci da kasashen Afirka musamman kasashen kungiyar kasashen Sahel (AES). Ya ce Iran tana goyon bayan yentattun kasashen Afrika, kuma bata goyon bayan shishigin da kasar faransa take yi a cikin harkokin shikin gida na kasashen yankin.

Ya kuma gudewa kasar har’ila yau bisa goyon bayan da ta nunawa JMI a dai dai lokacinda Amurka da HKI suka farwa kasarsa da yaki a farkon wannan shekarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted