Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da allawadai kan mummunan hare haren da jiragen yakin kasar Saudia suka kai kan wasu yankuna a kasar Yemen wadanda suka kai ga shahadar mutane fararen hula da yawa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar Yemen na cewa a wadannan hare hare na baya bayan nan jiragen yakin Saudia sun kai hare hare kan larduna kudancin birnin Ta’iz da kuama KHabb Sha’af inda suka jikata mutane da dama fararen hula.
Labarin ya kara da cewa, kafin haka sojojin Amurka da HKI sun kai hare hare kan wadan nan yankuna, idan an hada da mummunan halin da suke ciki saboda killace kasar wanda Saudia take yi kusan shekaru 12 da suka gabata, wannan zai zama laifin yaki a bisa dokokin MDD.
Ma’aikatar ta bayyana cewa gwamnatin JMI tana fatan bangarorin biyu zasu dawo kan teburin tattaunawa don kawo karshen yakin da ke faruwa a tsakanin kasashen biyu.
Kungiyar Ansarullah ta bayyana cewa akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare hare na baya bayan nan a kan wata kasuwa a birnin Ta’iz a jiya Lahadi.