Ministan harkokin wajen Birtaniya Edward Samuel Miliband ne ya yi tir da hare-haren da yahudawa ‘yan share wuri zauna suke kai wa Falasdinawa da lalata dukiyarsu da kasarsu a yammacin kogin Jordan.
Haka nan kuma ya ce; London za ta haramta shigar da dukkanin kayan da ake yinsu daga matsugunan ‘yan share wuri zauna din da aka gina ba bisa doka ba.
Ministan harkokin wajen na Birtaniya ya yi Magana da miliyoyin mutanen kasar da suke fushi saboda cutar da al’ummar Falasdinawa da ake yi, yana mai cewa; Muna jin kokenku, kuma kuna kan gaskiya.”
Ministan harkokin wajen na Birtaniya Edward Samuel Miliband ya kuma kara da cewa; Wahalhalun da mutanen Gaza da yammacin kogin Jordan suke sha, abin kunya ne ga duniya.”
A farkon wannan matan na satumba ne dai ministan harkokin wajen kasar ta Birtaniya ya yi jawabi a gaban majalisar kasar ta “House Of Common” da ya bayyana cewa: Za a kakaba takunkumai ga ‘yan share wuri zauna da suke a yankin yammacin kogin Jordan, kuma kasar za ta Sanya takunkumi mai tsanani akan sansanonin ‘yan share wuri zauna.
Birtaniya ce dai ta kirkiri Haramtacciyar Kasar Isra’ila akan bagiren Falasdinu a 1948,wanda ya sauya yanayin yammacin Asiya.