Jagoran Juyi:  Iran Ta Yi Gaba Ga Za Ta Taba Komawa Baya Ba

" A cikin shekaru goma na cin nasarar juyi, Kasashe masu girman kai na duniya, sun yi kokarin mayar da Iran baya a zamanin kaskanci
jagoran juyi

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Mujtaba al-Hussaini -Khamnei ya bayyana cewa; A matsayina na hadimin al’ummar Iran abar kauna, ina bayyana cewa; Ba za a taba komawa zuwa baya da makiya za su yi fata dawowarsa, abinda ya wuce ba za a sake maimaita shi ba.

Jagoran juyin musulunci na Iran ya fitar da bayani a yau Litinin dangane da “Makon Tsaron Kasa” na yakin shekaru 8 a tsakanin Iran da Iraqi, da kuma zagayowar shekaru biyu da shahadar Sayyid Hassan Nasrallah (r.a). A cikin bayanin jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma ce:

” A cikin shekaru goma na cin nasarar juyi, Kasashe masu girman kai na duniya, sun yi kokarin mayar da Iran baya a zamanin kaskanci da biyayya.”

Jagoran ya kuma ce; Duk da kokarin da makiya su ka yi, sai dai tsarin musulunci ya sake farfadowa da tashi cikin karfi fiye da baya,tamkar tsntsun “ Phoenix”.

Har ila yau jagoran ya kuma ce; A kodayaushe tsarin musulunci yana sake yunkurawa  ya tashi a duk lokacin da makiya su ka kyare shi,musamman ma dai bayan yake-yake biyu na bayan nan da aka kallafawa Iran.

A baya, tekun kudancin Iran ya zama wurin da makiya suke karakaina, amma a wannan lokacin saboda bugun da suke sha daga mujahidai masu jarunta, wadanda suke kare mashigar Hurmuz, ba su isa  tsallake tekun larabawa ba. Idan kuwa har su ka yi hakan, to za su cutar da kawukansu, kuma nan ba da jimawa ba, hatta tekun larabawan zai wofinta daga gare su.

Wani sashe na bayanin jagoran juyin musulunci ya tabo tarukan da ake yi a cikin Iran a kowace rana ta Allah tun daga fara yaki, da kuma babban gangamin da aka yi da mutanen Iran su ka nuna zamansu cikin Shirin ko-ta-kwana domin sadaukar da kawukansu.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce, a baya idan ana maganar jarunta a Iran ana danganta ta ne da maza,amma a wannan lokacin mata ne suke rigegeniya da maza da shiga gabansu wajen nuna jarunta

Da  yake Magana akan cikar Sayyid Hassan Nasrallah ya cika shekaru biyu da da shahada, jagoran juyin musulunci na Iran bayyana shi da alami na gwagwarmaya mai girma.” Haka nan kuma ya yi jinjina akan jajurcewa da tsayin dakar babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah na yanzu Sheikh Na’im Kassim da mayakan Hizbullah da suke samun ilhami daga yunkurin Ashura.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted