Mutanen birnin Najaf da wasu birane a kasar Iraki suna shirin gudanar da gagarumar zanga zangar rashin amincewa da sanya tashoshin jiragen Iraki cikin haramcin da Amurka ta yi wa saukar jiragen fasinjuar JMI a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran mutanen kasar Iraki musamman mutanen birnin Najaf suna zargin gwamnatin Ali zaidan ta biyewa kasar Amurka wacce ta haramta saukar jiragen fasinjar JMI a kasar.
Labarin ya kara da cewa an shirya gudanar da zanga zangar ne a dandanin juyin juya halin 20 da ke birnin Bagdza, haka ma a birnin Basra.
Masana a kasar Iraki sun bayyana cewa wannan haramcin zai shafi tattalin arzikin kasar Iraki, sannan zai shafi wasu al-amura da dama a rayuwar mutanen kasar Iraki. Musamman idan JMI ta maida martani. Sun ce fiye da daliban makarantar Jami’o’ii 50,000 suke karatu a kasar Iran. Ana shigo da iskar gas daga kasar Iran don amfanin mutanen Iraki da wasu al-amura da dama wadanda suka hada da jinya da al-amuran al-adu. Musamman ziyarar haramomin limamai masu tsarki.
Masu zanga zangar suna kira zuwa ga Ali Zidan firay ministan kasar da ya bude akalla tashoshin jiragen sama na Bagdaza da Najaf.