Araqchi: Iran A Shirye Take Ta Bude Mashigar Ruwan Hormuz

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: A shirye suke su bude mashigar Hormuz idan Amurka ta amince zata dauki wasu matakai da aka gindaya

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: A shirye suke su bude mashigar Hormuz idan Amurka ta amince zata dauki wasu matakai da aka gindaya mata

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Shawarar Iran ta kwanaki bakwai a bayyane take, yana mai cewa: “Sun shirya bude mashigar Hormuz, muddin Amurka ta dauki wasu matakai. Waɗannan buƙatun ba sababbi ba ne, kuma ba su fito daga sararin samaniya ba; su ne haƙƙoƙin Iran da take son a girmama su.”

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana a wata hira da shirin “Haɗuwa da ‘Yan Jarida”: “Shirin na kwanaki bakwai yana da ikon dawo da yanayin da ke faruwa a Tekun Farisa da Mashigar Hormuz zuwa al’ada. Don haka, muhimmiyar tambaya ita ce: Me yasa suke ƙin wannan shirin? Wannan tambaya ce da dole ne su amsa.”

Araqchi ya jaddada cewa, da farko dai, “Suna son kawo karshen wannan yakin, wannan yaki na zalunci. Sun fara wannan yakin watanni takwas da suka gabata suna fatan cimma nasara cikin kwana biyu ko uku. Watanni takwas sun shude, kuma ba su cimma burinsu ba.”

Ya ci gaba da cewa: “Fata a fannin diflomasiyya ya ci gaba, amma a gaskiya, idan aka yi la’akari da halayensu a cikin shekaru biyu da suka gabata, babu wata hujja ta komawa ga diflomasiyya da kuma yin mu’amala da wannan gwamnati ta Trupm.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted