Lebanon:  Mutane Biyu Sun Yi Shahada A Wani Harin Wuce Gona Da Iri Na “Isra’ila”A Birnin Beirut

Tashar talabijin din “Almayadin” mai watsa shirinta daga Lebanon ta watsa labarin dake cewa; Harin da ‘yan sahayoniya su ka kai wa unguwar Dhahiya a

Tashar talabijin din “Almayadin” mai watsa shirinta daga Lebanon ta watsa labarin dake cewa; Harin da ‘yan sahayoniya su ka kai wa unguwar Dhahiya a yau Lahadi da marece ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu da kuma jikkata wasu da dama.

Wannan harin dai yana zuwa ne a matsayin ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi, wanda ya zuwa yanzu ya ci dubban rayukan mutanen kasa,musamman a kudancin kasar.

A gefe daya, kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah tana ci gaba da mayar da martani akan sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila da suke mamaye da kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted