Lebanon: Mutane 15 Ne Su Ka Yi Shahada Tun Daga Tsagaita Wutar Yaki

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, mutane 15 ne su ka yi shahada tun daga lokacin da aka sanar da tsagaita

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, mutane 15 ne su ka yi shahada tun daga lokacin da aka sanar da tsagaita wuta a tsakanin kasar da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa, a ranar juma’ar nan da ta wuce, hare-haren ‘yan sahayoniya sun kashe mutane 6 a kudancin kasar, yayin da wasu mutane 2 su ka jikkata.

An tsagaita wutar yaki ne a tsakanin Lebanon da Haramtacciyar Kasar Isra’ila, a matakin farko bayan da Iran ta sanar da cewa shi ne sharadin zuwanta Islambad domin ttataunawa.

A gefe daya kungiyar gwgawarmaya ta Hizbullah tana cigaba da mayar da martani akan hare-haren ‘yan sahayoniyar, tana mai jaddada cewa matukar suna kai hari, to su ma za mu mayar da martani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted