Search
Close this search box.

Lebanon: Kungiyar Hizbullah Ta Kai Farmaki Kan Sansanin Sojojin HKI A Arewacin Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai farmaki kan cibiyar sansanin sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran

Kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai farmaki kan cibiyar sansanin sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto bayanin kungiyar a safiyar yau Lahadi na cewa, dakarun kungiyar sun yi amfani da makaman ‘Drones’ na kunan bakin wake a hare haren da suka kaiwa sansanin sojojin HKI mai suna Bait Halal a safiyar yau lahadi.

Bayanin da kungiyar ta fitar bayan hare haren sun bayyana cewa sun kai hare haren ne don tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin HKI take wa kissan kiyashi a gaza da kuma saboda hare haren da sojojin yahudawan suka kai kan wasu yankunan a kudancin kasar ta Lebanon.

Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan da dama suka halaka wasu kuma sun ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments