Search
Close this search box.

Lavrov Ya Fara Ziyara A Wasu Kasashen Afrika

Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov, ya fara wata ziyara a wasu kasashen Afrika da suka hada da Guinea Conakry, Congo Brazaville da kuma

Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov, ya fara wata ziyara a wasu kasashen Afrika da suka hada da Guinea Conakry, Congo Brazaville da kuma Chadi.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Sergey Lavrov ya isa a birnin Conakry na kasar Guinea, inda ya gana da shugabannin kasar.

Marabin Lavrov, ya ziyarci Guinea Conakry tun shekarar 2013.

Makasudin ziyarar a wannan karo ita ce karfafa huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Da yammacin yau ne kuma ministan harkokin wajen Rashar, zai isa kasar Congo Brazaville, inda cen din kuma zai tattauanwa da shugaba Denis Sassou-Nguesso, game da rikicin cikin gida na kasar Libiya.

A matsayinsa na shugaban kwamitin koli na kungiyar Tarayyar Afirka kan rikicin kasar Libiya, shugaban kasar Congo Denis Sassou-Nguesso, zai yi kokarin cimma yarjejeniya da Rasha domin ci gaba da shiga tsakani kan rikicin Libiyar mai sarkakiya.

Bayan Congo, ana sa ran Serguei Lavrov zai iasa a birnin Ndjamena na kasar Chadi, inda zai gana da shugaban kasar Mahamat Idriss Deby, wanda aka zaba ya kuma kama aiki kwanan nan.

Wannan ita ce ziyararsa ta shida a nahiyar Afirka cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ministan ya ziyarci Sudan, Mali, Mauritania, da Afirka ta Kudu a watan Fabrairun 2023, bayan ya ziyarci Afirka ta Kudu, lokacin da ya halarci taron BRICS, sai kuma kasashen Eswatini, Angola, da Eritrea a watan Janairu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments