Iran : Batun Falasdinu Shi Ne Na Farko Mafi Mahimmanci A Duniyar Musulmi_ Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce Falastinu ita ce batu na farko kuma mafi muhimmanci a duniyar musulmi. Jagoran ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar ga dimbin al’ummar kasar da suka taru a hubbaren marigayi Imam Khumaini da ke kudancin birnin Tehran yau Litinin a […]

Karshen Rejistar Takarar Zaben Shugaban Kasa A Iran

A Iran, yau Litinin ne ake kawo karshen rejistar takarar zaben shugaban kasar domin maye gurbin shugaban kasar mai rasuwa Ebrahim Raeisi. Gomman ‘yan takara ne da suka hada da fitattun ‘yan siyasa da sabbin fuskoki suka gabatar da sunayensu kafin karshen wa’adin rejistan yau Litini. A ranar 28 ga watan Yuni ne za a […]

IAEA, Ta Bukaci Ci Gaba Da Tattaunawa Da Iran A Matakin Koli

Shugaban Hukumar kula da Makamashin Nukiliya Ta Duniya, Rafael Grossi, ya bukaci ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Iran a matakin koli, game da batutuwan da ake takaddama akansu. Mista Grossi ya tabo batun ziyarar da ya kai birnin Tehran a baya-bayan nan da kuma yarjejeniyar da aka cimma da jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran […]

Lavrov Ya Fara Ziyara A Wasu Kasashen Afrika

Ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergey Lavrov, ya fara wata ziyara a wasu kasashen Afrika da suka hada da Guinea Conakry, Congo Brazaville da kuma Chadi. Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, Sergey Lavrov ya isa a birnin Conakry na kasar Guinea, inda ya gana da shugabannin kasar. Marabin Lavrov, ya ziyarci […]

Imam Khumaini {r.a} Shi Ne Tushen Nasarorin Da Gwagwarmaya Take Samu A Wannan Zamani

An bayyana marigayi Imam Khumaini (r.a) a matsayin tushen samar da nasarorin da gwagwarmaya take samu a wannan zamani Manazarta da masharhanta sun bayyana cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sun hana batun ambaton matsalolin al’ummar Falastinu, da hana batun tunasar da hakkokin Falasdinawa a tsakanin al’ummar Larabawa da Musulmi, amma zuwa Imam Khumaini {r.a} […]

Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Tarwatsa Yahudawan Sahayoniyya ‘Yan Kaka Gida 100,000

Gidan radiyon sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya watsa labarin cewa: Shiyar arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba da konewa sakamakon luguden wutar kungiyar Hizbullah ta Lebanon Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta tilastawa yahudawan ‘yan kaka gida kimanin 100,000 tserewa daga matsugunansu sakamakon luguden wuta […]