Search
Close this search box.

Lapid : Netanyahu Da Mukarabansa Sun Rasa Makama

Madugun ‘Yan adawa a Isra’ila, ya ce firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da mukarabansa mutane ne kawai wadanda suka maida hankali kan makomarsu ta siyasa. Yair

Madugun ‘Yan adawa a Isra’ila, ya ce firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da mukarabansa mutane ne kawai wadanda suka maida hankali kan makomarsu ta siyasa.

Yair Lapid, ya caccaki gwamnatin ta Netanyahu dake cikin tsaka mai wuya, inda ya bayyana hakan ne a shafinsa na ”X”, inda ya kara da cewa Netanyahu da wadanda ke kewaye da shi na son kai wargaza Isra’ila ne.

Ko a farkon wannan wata, ya bayyana cewa gwamnatin Netanyahun, ta ”rasa makama”.

Ya bayyana cewa dangantaka tsakanin Isra’ila da Amurka ta ruguje, kuma masu karamin hali na dandana kudarsu a kasar.

”Ana kashe sojoji ko wace rana a Gaza, sannan suna fada a tsakaninsu a talabijin, sannan ministoci suna kalubalantar junansu a yayin taruka.

Gwamnnatin Netanyahu dai na fuskantar matsin lamba na cikin gida da ketare, saboda yakin da ta ke a Gaza.

Ko a baya baya nan Rahotannin sun ce an yi zanga zanga a Tel Aviv, inda akayi artabu tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zangar a cikin daren jiya.

Masu zanga zanga na kalubalantar yadda gwamnatin kasar ke tafitar da yakin Gaza, inda suke bukatar gwamnatin ta matsa kaimi waken ganin an sako mutanen da ake garkuwa dasu a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments