Dakarun Izzuddeen Al-Qassam Sun Halaka Sojojin Yahudawan Sahayoniyya Masu Yawa

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun nuna yadda suka halaka sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da raunata wasu tare da kama wasu a matsayin fursunonin yaki Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa: Dakarunsu sun yi nasarar ritsawa da sojojin yahudawan sahayoniya a daya daga cikin ramukan karkashin kasa da […]

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Ci Gaba Tafka Laifuka Yaki Kan Falasdinawa A Zirin Gaza

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aikata munanan laifuka a kan fursunonin Falasdinawa da take tsare da su Ma’aikatar kula da fursunonin Falasdinu ta yi Allah wadai da munanan laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a gidajen yarin da suke tsare da Falasdinawa, tana mai kira ga kasashen duniya da su bude babban bincike kan laifukan […]

Burkina Faso : An Kara Wa Sojojin Dake Mulki Wa’adin Shekaru Biyar

Gwamnatin mulkin soji ta Burkina Faso za ta ci gaba da mulki har nan da shekaru biyar masu zuwa bayan mahalarta taro kan makomar kasar sun bayar da shawarar komawa kan mulkin dimokuradiyya zuwa watanni 60 daga watan Yuli mai kamawa. Sabon tsarin, wanda shugaban mulkin sojin Burkina Faso Ibrahim Traore ya sanya wa hannu, […]

Denmark, Ta Bukaci Isra’ila Ta Kawo Karshen Aikin Soji A Rafah

Ministan harkokin wajen kasar Denmark, ya bukaci Isra’ila data kawo karshen aikin soji a binrin Rafah. Furucin Lars Loke Rasmussen, na zuwa ne bayan da  kotun kasa da kasa ta ICJ, ta bukaci Isra’ila data dakatar da ayyukan soji a birnin Rafah da kuma bude mashigar Rafah dake kudancin zirin Gaza. Ministan harkokin wajen Denmark […]

Hamas Ta Ce Ta Hallaka Sojojin Isra’ila da Dama

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta sanar da kashewa, da raunatawa, da kuma kame wasu sojojin Isra’ila, ta hanyar kai musu hari a arewacin zirin Gaza. Abu Obeida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, reshen soji na Hamas ne ya bayar da wannan bayanin a wani faifan faifan bidiyo yau Lahadi. Lamarin ya faru ne a yayin […]

Lapid : Netanyahu Da Mukarabansa Sun Rasa Makama

Madugun ‘Yan adawa a Isra’ila, ya ce firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da mukarabansa mutane ne kawai wadanda suka maida hankali kan makomarsu ta siyasa. Yair Lapid, ya caccaki gwamnatin ta Netanyahu dake cikin tsaka mai wuya, inda ya bayyana hakan ne a shafinsa na ”X”, inda ya kara da cewa Netanyahu da wadanda ke kewaye […]

Ana Sa Ran Kimanin Motocin Agaji 200 Su Shiga Gaza Daga Masar

Rahotani daga Gaza na cewa ana sa ran kimanin motocin Agaji 200 su shiga yankin daga kasar Masar a yau Lahadi. Khaled Zayed, shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent ta Masar a arewacin Sinai, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, a yau ne ake sa ran manyan motocin agaji 200 za su […]

Kungiyar Hamas Ta Bada Sanarwan Halaka Sojojin HKI, Da Kama Wasu

Kungiyar Hamas a zirin Gaza ta bada sanarwan halaka da kuma jikatar sojojin yahudawan HKI a wata fafatawa da suka yi  a yankuna daban daban na zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abu ubaida kakkan reshen soje na kungiya Hamasa  ya na fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara […]

Majalisar Dokokin Kasashen Larabawa Ta Bukaci A Dakatar Da Yaki A Gaza

Shugaban majalisar dokokin kungiyar kasashen Larabawa ya bukaci a tsagaita budewa juna wuta  a gaza da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Adil Al-asumi shugaban majalisar dokokin kungiyar kasashen larabawa yana fadar haka a taron majalisar dokokin kasashen larabawan da aka gudanar a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. […]