Search
Close this search box.

Kwamitin Tsaron MDD Ya Yi Shiru Na Minti Guda Domin Girmama Shugaba Ibrahim Raisi

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi shiru na minti daya domin girmamawa da kuma alhini na rasuwar  shugaban kasar Iran marigayi Ibrahim Raisi,

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi shiru na minti daya domin girmamawa da kuma alhini na rasuwar  shugaban kasar Iran marigayi Ibrahim Raisi, kamar yadda jakadan kasar Mozambique a MDD Pedro Comissario Afonso, wanda ke jagorantar majalisar a wannan watan ya bayyana.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun mike baki dayansu, sun tsit na minti daya.

A cikin wani sako, Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah Sayyed Ali Khamenei ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar Iran bisa rasuwar shugaban kasar Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da sauran abokan tafiyarsu da suka rasa rayukansu tare a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar Lahadin da ta gabata.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa al’ummar Iran sun yi rashi na bababn mutum mai gaskiya, mai kishin kasa da kuma kishin addininsa da al’ummarsa.

A halin yanzu haka dai ana shirin gudanar da janazar shugaba Ra’isi da sauran wadanda suka rasa rayukansu tare da shi a ranar gobe Laraba, inda raka jana’izar tasu a biranen Tabriz, Qom, Tehran da kuam Mashshad.

Ana sa miliyoyin mutane za su halarci rakiyar janazar a wadannan birane, inda kuma za a rufe gawar marigayi shugaba Ra’isi a mahaifarsa wato birnin Mashshad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments