Kwamandan Rundunar Sojin Iran Ya Sanar Da Dakatar Da Yakin Da Ya Sake Kunno Kai Tsakanin Iran Da Isra’ila  

Hedikwatar Rundunar Soji ta Tsakiya ta Khatam al-Anbiya ta sanar da dakatar da ayyukan soji kan sharudan doka Hedikwatar Rundunar Soji ta Tsakiya ta Khatam

Hedikwatar Rundunar Soji ta Tsakiya ta Khatam al-Anbiya ta sanar da dakatar da ayyukan soji kan sharudan doka

Hedikwatar Rundunar Soji ta Tsakiya ta Khatam al-Anbiya ta Kasar Iran ta sanar da dakatar da ayyukan soji a kan abokan gaba ‘yan Sahayoniyya, tana mai jaddada cewa: Idan hare-haren suka ci gaba, musamman a kudancin Lebanon, to lallai zata mayar da martani mai tsanani.

A cikin wata sanarwa da hedikwatar rundunar Soji ta Tsakiya ta Khatam al-Anbiya ta Iran ta fitar ta jaddada cewa: “Bayan hare-hare da ta’addancin da sojojin Yahudawan Sahayoniyya ja’irai suka kai a kudancin Lebanon da yankin Dahiyeh, tare da goyon bayan Amurka kanwa uwar gami, Sojojin Iran sun mayar da martani mai zafi kan wadannan tsagerun yahudawan sahayoniyya don tallafawa mutanen Lebanon da ake zalunta.”

Sanarwar ta kara da cewa: “Wannan martani ne da ‘yan Sahayoniyya da magoya bayansu ya kamata su koyi darasi a ciki.”

Ta yi karin haske: “Saboda haka, an ayyana dakatar da ayyukan soji; duk da haka, an jaddada cewa idan wadannan hare-hare da ta’addanci suka ci gaba, ciki har da kudancin Lebanon, za a dauki matakai masu tsauri da tsanani kan makiya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted