Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Yi Gargadi Kan Yiwuwar Bullar Masifar Yunwa A Kasar Sudan

Kungiyoyin kasa da kasa goma sha tara sun yi gargadin yiwuwar bullar masifar yunwa nan kusa kadan a Sudan Kungiyoyin ba da agaji na kasa

Kungiyoyin kasa da kasa goma sha tara sun yi gargadin yiwuwar bullar masifar yunwa nan kusa kadan a Sudan

Kungiyoyin ba da agaji na kasa da kasa guda goma sha tara sun yi gargadin yiwuwar bullar masifar yunwa nan kusa kadan a kasar Sudan, idan bangarorin da ke rikici da juna suka ci gaba da hana kungiyoyin jin kai ba da agaji ga masu bukata.

Wannan gargadi ya zo ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin kungiyoyin agaji na kasa da kasa 19 suka sanya wa hannu, kuma 12 daga cikinsu na Majalisar Dinkin Duniya ne, kamar yadda shafin yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

A cikin sanarwar, kungiyoyin kasa da kasan sun yi gargadin cewa: Kara kawo cikas ga samar da agaji cikin gaggawa, hakan yana nufin karin yawan mutanen da za su mutu. Sannan kungiyoyin jin kai sun yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna a Sudan su dauki matakan kare fararen hula da saukaka ayyukan jin kai da kuma daukar matakin tsagaita bude wuta a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments