A yunkurin da ake na gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da mawuyacin halin da jama’a suke cikia Najeriya, wasu kungiyoyin kare dan adan sun gargadi gwamnati yin barazana ga masu shirin gudanar da zanga-zangar.
Kiran zanga-zangar da aka shirya gudanarwa daga daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa, ta samu karbuwa a shafukan sada zumunta da kuma wasu ‘yan kasar.
Hukumomin Najeriya sun yi gargaɗi kan gudanar da zanga-zangar da za ta jefa ƙasar cikin tashin hankali tare da yin kwatanci da halin da ƙasashe kamar Kenya da Sudan da Libya ke ciki sakamakon yin bore.
Sai dai duk da cewa gwamnatin Najeriya ta ce ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zanga ta lumana, amma shugaban kungiyar CISLAC kuma babban jami’i a kungiyar Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce “Dimukuradiyya ta ba ƴan ƙasa ƴancin fitowa su nuna damuwarsu.