Kungiyar Hamas da wasu gunguin kungiyoyin gwagwarmaya a yankin sun matukar kalubalantar hare haren baya bayan nan na Isra’ila a zirin Gaza.
Kungiyoyin sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa lamarin tamkar aikata laifukan yaki ne da kuma takala.
Sanarwar ta ranar Asabar ta ce hare haren da suka hada da wadanda aka kai kan wani gidan iyali a arewacin Gaza da kuma wata motar ‘yan a Khan Younès wandanda sukayi sanadin mutuwar mutum sama da goma tsokana ce karara a game da rikicin da gwamnatin sahayoniya ke ci gaba da aikatawa a fadin duniya ba tare da la’akari da al’amuran jin kai ba.
Ci gaba da hare haren Isra’ila a fadin zirin Gaza, gazawa ce ta masu shiga tsakani da kasashen duniya domin kawo karshen laifukan Isra’ila.
Hamas ta bukaci kasashen duniya da kuma dukkan bangarorin dasu dauki matakin da ta dace domin kare falasdinawa da kuma matsawa Isra’ila lamba domin ta mutunta alkawarin da ta dauka a yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kuma dokokin kasa da kasa.