KungiyarAnsarullah Ta Yemen Ta Ce: Alkawarin Allah Ne Zai Tarwatsa Zaluncin Azzalumai

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Rushewar zaluncin ‘yan Sahayoniyya alkawari ne da ba makawa Shugaban ƙungiyar Ansarullah, Sayyid Abdul-Malik Badr al-Din

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Rushewar zaluncin ‘yan Sahayoniyya alkawari ne da ba makawa

Shugaban ƙungiyar Ansarullah, Sayyid Abdul-Malik Badr al-Din al-Houthi, ya tabbatar da cewa: Alƙawarin Allah na rugujewar zaluncin ‘yan Sahayoniyya ba makawa, yana mai jaddada cewa: “Babu abin da zai ƙarfafa daidaito da maƙiyi wanda ya kai mafi munin matsayi na alaƙa da Shaiɗan, mugunta, da keta.”

A cikin hudubar da yake gabatarwa a cikin watan Ramadana, Sayyid al-Houthi ya jaddada cewa: Alkawuran Allah na rugujewar zaluncin Yahudawan Sahayoniyya a bayyane suke, kuma tabbas, saboda alaƙarsu kai tsaye da adalci da hikimar Allah.

Ya nuna cewa mummunan halin da al’ummomi suka fada ciki a yau sakamakon sakaci da kuma mummunan ƙarancin kula da wajibai na addini. Ya lura cewa gwamnatoci suna ci gaba da ɗaukar manufofin “kulla alaka da Isra’ila”, waɗanda ke nufin “amincewa da Yahudawan Sahayoniyya da kuma miƙa wuya ga ikonsu da umarninsu,” duk da munanan laifuka da zaluncinsu.

Sayyid al-Houthi ya ƙara da cewa: “Babu wani abu da zai ƙarfafa alaka da maƙiya ‘yan Sahayoniyya wanda ya kai mafi munin matsayi na kulla alaƙa da Shaidan, ” wanda akidarsa ta dogara ne akan kawar da al’ummomi da kuma ɗaukar wasu a matsayin “dabbobi. ” Wannan yana cikin “maganganun jami’ansu, al’adunsu, da makarantunsu, waɗanda suka amince da zubar da jinin mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted