Kungiyar Taliban Ta Bayyana Cewa Karkashin Shariar Musulunci Makomar Mutanen Kasar Zata Yi    Kyau

Ministan wucin gadi a ma’aikatar cikin gida na kasar Afganistan ya bayyana cewa mutanen kasar Afganistan suna da kekyawar makoma a karakshin ikon shari’ar musulunci

Ministan wucin gadi a ma’aikatar cikin gida na kasar Afganistan ya bayyana cewa mutanen kasar Afganistan suna da kekyawar makoma a karakshin ikon shari’ar musulunci a kasar.

Tashar radiyo ta harshen dari mai watsa shirye  shiryensa da harshen dare daga nan Tehran ya nakalto Sirajuddeen Hakkani ministan riko a ma’aikatar cikin gida na gwamnatin Taliban yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da wikilin kasashen Turai a birnin Kabul Rafael Udiche a birnin Kabul.

A nashi   bangaren wikilin kasashen Turai na birnin Na Kabul ya ce yana fatan al-amuran tsaro zasu kara kyautatuwa a kasar ta Afganistan ta yadda mutanen kasar zasu koma rayuwar da suka saba ba tare da matsalolin tsaro irin na baya ba.

Tun ranar 15 ga wtaan Augustan shekara ta 2021 ne mayakan Taliban suka sake dawo da ikonsu kan kasar afganistan bayan da Amurka tare da taimakon wasu kasashen yamma suka kwace kasar daga hannun Taliban na tsawon shekaru kimani 20.

Sai duk tare da dawowa kan iko a kasar Afganistan da ta yi, kungiyar Taliban ta kasa samun kasa guda a duniya wacce ta amince da halaccin ikonta a kan mutanen Afganistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments