Kungiyar Hizbullah Ta Nuna Sabbin Hotunan Leken Asiri Na Sansanin Sojan HKI Mafi Muhimmanci Akan Iyaka

Faifan Bidiyon din wanda aka bai wa sunan; “Sakon Da Tsuntsun Huda-huda Ya Dawo Da Shi, yana kunshe da cikakkun hotuna da bayanai akan yadda

Faifan Bidiyon din wanda aka bai wa sunan; “Sakon Da Tsuntsun Huda-huda Ya Dawo Da Shi, yana kunshe da cikakkun hotuna da bayanai akan yadda tsarin ginin wannan cibiyar  da “Ramata David” yake da dukkanin bangarorin da ta kunsa.

Wannan ita ce cibiyar sansanin soja daya tito da HKI take da ita a yankin Arewacin  Falasdinu da take a karkashin mamaya.

A cikinta da akwai jiragen yaki da masu saukar angulu da kuma na leken asiri.

Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai kungiyar ta Hizbullah ta nuna wani faifan bidiyo din wanda aka dauki cibiyoyin tattalin arziki, soja da sansanonin ‘yan share wuri zauna a birnin Haifa.

Ita dai kungiyar ta Hizbullah tana fitar da wadannan hotunan nan ne domin gargadin HKI cewa, matukar ta fadada yankunan da take kai wa hari a cikin Lebanon, to yankunan da suke a karkashin mamayarta ma za su fuskanci kai hare-hare.

A jiya ne dai kafafen watsa labarun  HKI su ka bayyyana cewa; Sayyid Nasrallah ya cika alkawalin da ya yi na cewa, kungiyarsa za ta fadada wuraren da take kai wa hare-hare.

Da safiyar yau Alhamis ma dai kafafen watsa labarun na HKI sun cea an ji jiniyar gargadi tana kadawa a “Rayhana”,”Karam Bin Zamra”, dake yankin Jalil.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments