Kungiyar Hizbullah Ta Mallakin Sabbin Makamai Da Manyan Kasashen Yankin Ba Su Da Su

Kungiyar Hizbullahi ta mallaki wasu sabbin makamai wadanda manyan kasashen yankin ba su mallaka ba! Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta buga labarin da

Kungiyar Hizbullahi ta mallaki wasu sabbin makamai wadanda manyan kasashen yankin ba su mallaka ba!

Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta buga labarin da ta yi karin haske kan abin da jaridar “Al-Jarida” ta kasar Kuwaiti ta buga a ‘yan kwanakin nan, inda ta bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta mallaki makamai masu linzami da suke amfani da karfin wutar lantarki ta “electromagnetic”.

Dangane da gagarumar ci gaban da kungiyar ta Hizbullah ta samu,  jaridar ta Ma’ariv ta yi hira da Rotem Mei Tal, Shugaban Kamfanin Asgard Systems, wanda ke da alaka da bunkasa fasahar soji don masana’antun tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila, inda jami’in ya ce, “Bayyana makamai a matsayin tsarin electromagnetic yana nufin yin magana game da wani abu da babu wanda ya taba gani, amma kowa ya fahimta lallai akwai yiwuwar kera shi, kuma a gare su wani sabon tsari ne na karfin siyasa da na soji a yankin Gabas ta Tsakiya.

A bayaninsa na bayanin makamin lantarki, Rotem Mei Tal ya kara da cewa: Mutum zai yi tunanin cewa walƙiya ta afkawa ginin da ke zaune a cikinsa, sai tsarin ruwa da wutar lantarki da na’urorin gida misalin talabijin da na’urorin kiwon lafiya su daina aiki, kamar yadda yake faruwa a lokacin da wutar lantarki ta katse. Wannan tsarin a cikin wannan yanayin na iya ƙonewa daga ciki. Kamar gajeriyar lantarki.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments