kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi tofin Allah tsine game da kisan kare dangi mafi muni da HKI ke yi kan mata da yare kanana da basu da kariya a yankin Gaza , inda isra’ila take ci gaba da yin lugudan wuta ta sama da kasa a yankin duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka kulla tsakani.
majiyar lafiya ta yankin falasdinu ta bayyana cewa akalla mutane 15 ne da suka kada da mata da yara kanana suka jikkata a wani hari da sojojin isra’aila suka kai a sansanoni falasdinawa dake gaza.
haka zalika wasu falasdinawa guda 7 sun mutu ciki har da mata guda 2 a yankin Gaza, kuma wannan yana zuwa ne bayan da masu shiga tsakanin suka fara tattaunawa a birnin alkahira na kasar Masar da kungiyar Hamas da sauran bangarorin dake da ruwa da tsaki wajen yarejejniyar dakatar da bude wuta da aka cimma.
kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassam yace gwamnatin sahayuniya tana daukar mataken rusa yarjejeninar da aka cimma da irin hare haren da take kaiwa, wanda hatta ma yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya kulla ba tayi tasiri ba ko kadan wajen dakatar da isra’ila kai hari kan kasar labanon da ci gaba da mamaye yankunanta.