Kungiyar Hamas a zirin Gaza ta bada sanarwan halaka da kuma jikatar sojojin yahudawan HKI a wata fafatawa da suka yi a yankuna daban daban na zirin gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abu ubaida kakkan reshen soje na kungiya Hamasa ya na fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa sun rutsa da sojojin yahudawan ne a cikin wani rami na karkashin kasa a garin Jabaliya a tsakiyar zirin Gaza.
Labarin ya kara da cewa banda sojojin yahudawan wadanda dakarun izzuddeen kassam suka halaka, ko suka jikata, sun kama wasu da ransu.
Labarin ya kara da cewa, bayan an rutsa da sojojin yahudawan a cikin ramin da ke garin na Jabaliya, wasu sojojin sun yi kokarin kawo masu dauki, amma dakarun kassam sun tarwatsasu da nakiyoyi da suka bisne a kan hanyar shiga ramukan na karkashin kasa.