Kungiyar Hamas Ba Zata Wargaje Ba Saboda Da Hare-Haren Zaluncin Gwamnatin Mamaya

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Ba za a yin nasara a kan kungiyar ba duk da gagarumin barna da aka yi wa yankin Gaza Jaridar

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Ba za a yin nasara a kan kungiyar ba duk da gagarumin barna da aka yi wa yankin Gaza

Jaridar Ma’ariv ta Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ambato Manjo Janar Yitzhak Brik yana cewa: “An yi musu alƙawarin ‘samun cikakken nasara’, amma gaskiyar magana ita ce manufar kawar da Hamas tana nesa da su kamar yadda gabas take nesa da yamma.”

Jaridar ta ƙara da cewa: “Yahudawan sahayoniyya ba su taɓa ganin irin wannan wulaƙanci da Rashin dabarun yaƙi ba. Duk da mallakar mafi kyawun rundunar sojojin sama a duniya da kuma motocin yaƙi masu sulke a ƙasa, gwamnatin mamayar Isra’ila ta gaza kayar da wata ƙungiyar gwagwarmaya tsawon shekaru biyu. Wannan gazawar ta shafi aiki ne da kuma na shugabanci.”

Bayanin Manjo Janar Brik, kamar yadda jaridar yahudawa ta ruwaito, bai ba wa mai karatu mamaki ba. Mai bincike na Burtaniya Dr. Azeem Ibrahim, ya riga ya bayyana dalilan da ya sa wannan haramtacciyar gwamnati ta gaza murkushe kungiyar Hamas.

Dr. Ibrahim ya bayyana cewa: Duk da ƙudurin gwamnatin mamayar Isra’ila na bin sahun “nasara” ko da bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta ne ta hanyar kai hare-hare kan Gaza da kuma lalata yankin, gaskiyar da ke ƙasa tana ba da labari daban-daban. Daga cikin tarkacen Gaza, kimanin mayaka 15,000 ne da suka fito daga ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas suka bayyana kuma yawancinsu suna da cikakken makamai, waɗanda ke “aiki don sake kwace iko da yankin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted