Hamas : Duk wani mataki game da Gaza dole ne ya dakatar da hare-haren Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce duk wani mataki da za’a dauka game da Gaza dole ya dakatar da hare-haren Isra’ila. Hamas ta kuma yi Allah wadai da kiran “Majalisar Zaman Lafiya” kan Gaza na Amurka. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta tabbatar da cewa duk wata shawara ko yarjejeniya ta […]

Araghchi Ya Nanata Tsarin Tattaunawa Tsakanin Iran da Amurka

Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada kokarin shirya daftarin yarjejeniyar tattaunawa da Amurka, bisa girmama juna, yayin da tattaunawa kan shirin nukiliya na Iran ke shiga wani mataki mai zurfi. Abbas Araghchi ya yi wadannan kalaman ne a lokacin wata tattaunawa ta wayar tarho yau Juma’a, tare da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty, inda […]

Amurka: Kotun Koli ta ce harajin da Trump ya sanya a 2025 basa bisa ka’ida

Kotun koli a Amurka ta yanke hukuncin cewa shugaban Amurka ya wuce ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi ta hanyar sanya haraji kan kusan dukkan kayayyakin da ke shigowa kasar. Mafi rinjayen alkalai shida ne suka yanke hukuncin. Ya shafi harajin da Donald Trump ya gabatar, amma ba wadanda aka yi amfani da […]

Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Mai Tsanani Idan Aka Kai Mata Hari

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce: Duk wani hari kan kasarsa zai sanya sansanonin makiya su fuskanci hare-haren daukan fansa Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya bayyana cewa: Kasarsa ba za ta fara wani yaki ba, amma za ta mayar da martani mai zafi kuma kwatankwacin […]

MDD Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka

Majalisar Dinkin Duniya ta jadadda cewa: Ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ya zama dole domin kauce wa rashin zaman lafiya Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya sanar da cewa: Kungiyoyin kasa da kasa sun tabbatar da goyon bayansu  ga ci gaba da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Da yake magana da […]

Grossi: Akwai Bukatar Cimma Yarjejeniya Mai Cikakken Tsari Tare Da Iran

Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya ya ce: Ana ci gaba da tuntubar juna game da Iran, kuma cimma yarjejeniya na buƙatar cikakken tsari Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da cewa: Ana ci gaba da tuntubar juna da tattaunawa game da Shirin makamashin nukiliyar Iran. […]

Kungiyar Hamas Ba Zata Wargaje Ba Saboda Da Hare-Haren Zaluncin Gwamnatin Mamaya

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Ba za a yin nasara a kan kungiyar ba duk da gagarumin barna da aka yi wa yankin Gaza Jaridar Ma’ariv ta Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ambato Manjo Janar Yitzhak Brik yana cewa: “An yi musu alƙawarin ‘samun cikakken nasara’, amma gaskiyar magana ita ce manufar kawar da Hamas tana […]

Matakan Ci Gaba Da Take Hakkin Bil’Adama Suna Ci Gaba A Kasar Sudan

Shaidu masu ban tsoro na kisan kai, fyaɗe da kakaba yunwa da ake aiwatarwa kan ƙabilu a yakin kasar Sudan! An rubuta laifukan yaƙi, laifukan cin zarafin bil’adama, da kuma wani kamfen da ke nuna kisan kare dangi a cikin wani rahoto da Ofishin Bincike na Duniya mai zaman kansa a Sudan ya fitar, wanda […]

An zabi Kasar Iran A Matsayin Mataimakiyar Shugabar Kwamitin Musamman Na M D D

rahotanni sun bayyana cewa an zabi iran a matsayin mataimakiyar shugabar kwamitin musamman na majalisar dinkin duniya kan yarjejeniya, kuma mamba ce a ofishin kwamitin. wannan matakin yazo ne a lokacin taron da aka gudanar a hedkwatar majalisar dake birnin newyork, don haka kasar iran za ta  yi aiki a matsayin mataimakiya ga shugabar musamman […]

Jagora Ya Halarci Wajen Taron Karatun Alur’ani Da Aka yi A Ranar Farko Na Watan Ramadan

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamana’I ya halarci taron karatun Alkur’ani mai tsarki  da aka fara a ranar farko ta Azumin watan ramadana mai alfarma, tare da manyan mukarraban gwamnati da fitattun makaranta Alkur’ani mai girma da kuma sauran masana ilimin Alkur’ani mai girma. taron na karatun Alkur’ani mai girma da ake […]