Kungiyar gwagwarmaya ta Al-Nujaba’u ta yi alkawarin kai zafafan hare-haren daukan fansa kan muhimman wurare a haramtacciyar kasar Isra’ila
A martanin da kungiyar gwagwarmayar kasar Iraki ta Al-Nujaba’u ta fitar a jiya alhamis ta yi alkawarin mayar da martani mai tsanani da zai kasance na bazata tare da yin mummunan tasiri kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila. Tana mai jaddada cewa: Hare-haren da zata kai zasu kasance ne kan muhimman wurare a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila a matsayin daukan fansa kan harin wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai kan cibiyoyin kungiyar.
Kungiyar Al-Nujaba’u ta kasar Iraki ta yi wannan gargadi na mayar da martani kan gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya bayan harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan ginin cibiyar al’adu da yada labaranta da suke birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya.