Kotun Koli Ta Nigeria Ta Bayar Da Belin Tsohon Ministan Shari’a Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci

Kotun koli dake birnin tarayya Abuja ta bayar da belin tsohon minstan shari’ar kasar, Abubakar Malami tare da dansa Abdulaziz, tare da daga ci gaba

Kotun koli dake birnin tarayya Abuja ta bayar da belin tsohon minstan shari’ar kasar, Abubakar Malami tare da dansa Abdulaziz, tare da daga ci gaba da yi musu shari’a zuwa ranar 4 ga watan Mayu.

Mutanen biyu dai za su sami sararawa ne daga tsare su da ake yi, bisa belin kudin da za sun kai kwatankwacin dalar Amurka 147,000 ga kowane daya daga cikinsu.

Ana tuhumar kowane daya daga cikinsu da laifukan ta’addanci, mallakar makamai ba tare da izini ba.

Lauyan da yake bai wa Malami kariya Adedayo Adedeji ya ce; Dangane da tuhuma ta biyu wacce hukumar jami’an tsaro ta sirri DSS ta shigar da kara, da kuma mu ka nemi a bayar da beli akanta,tuni dai mai kare kan nasa ya kore cewa ya aikata laifi.”

Haka nan kuma Malami, dansa da mai dakinsa, suna fuskantar wasu tuhume-tuhumen guda 16 da hukumar fada da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta tattara bayanai akansu. Daga ciki da kawai halarta kudaden haramun da mallakar kaddarori da sun kai dalar Amurka miliyan 6.

 Shi dai Malami ya zama ministan shari’a, kuma babban mai shigar da kara na tarayya daga  watan Nuwamba 2015 zuwa Mayu na  2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted