Babban lauya mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Karim Khan, ya bayyana cewa: Cin zarafi da laifuka kan yara da fararen hula sun kara tsananta a Sudan, musamman a yankin Darfur, yana mai jaddada cewa wadanda suka ba da umarnin aikata wadannan laifuffuka da kuma wadanda ke ba da kudi don kara ruruta wutar rikicin kasar za su fuskanci tuhuma da bincike.
A jawabin da ya gabatar a gaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya Khan ya jaddada cewa: Halin da ake ciki a Sudan na kara tabarbarewa, bisa la’akari da rahotannin yin fyade ga mata da cin zarafin yara musamman a yankin Darfur.
Babban lauyan akotun ta ICC ya kara da cewa: Mayakan da ke El Geneina da El Fasher da kuma dukkan kasar Sudan sun yi imanin cewa za su kubuta daga hukunta su, yana mai cewa, tabbas za su fuskanci tuhuma da gudanar da bincike kansu musamman wadanda ke ba da umarni ga sojojin Sudan da kungiyar Dakarun kaidaukingaggawa da kuma wadanda ke taimaka musu da kuma ba su kudade.