Kotun kolin kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa a jiya Alhamis kan wani tsohon jami’in gwamnatin kasar kan laifin aikata kisan gilla da kishe-kashe kan ‘yan kasar da kuma boye gawarwakinsu a manyan kaburbura.
A cikin wata sanarwa da majalisar koli ta shari’ar kasar Iraki ta fitar ta bayyana cewa: Kotun kolin manyan laifuka ta kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan daya daga cikin jiga-jigan tsohuwar gwamnatin kasar Khairallah Hammadi Abd Jaru bisa laifin aikata kisan gillar da aka yi wa mutane 198 daga yankin Balad a shekara ta 1981, da kuma hannu a cikin aiwatar da hukuncin kisa kan ‘yan kasar da kuma boye gawarwakinsu a cikin manyan kaburbura.
Sanarwar kotun kolin ta kara da cewa: Mai laifin ya taba rike mukamin daraktan tsaron kasar kuma ya rike mukamai da dama a wasu lardunan kasar kafin shekarar 2003.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa: Wanda ake tuhumar ya shiga cikin kama jama’a da aiwatar da kashe-kashe kansu a gundumar Balad bisa zarginsu da kasancewa ‘yan jam’iyyar Da’awa mai alaka da addinin Musulunci, baya ga gano manyan kaburbura, da aka kashe jama’a a lokacin shugabancinsa a larduna.