Kokarin Mayar Da Duniya Karkashin Kama-Karyar Amurka Da “Isra’ila”

 Duk wani mai hankali a wannan zamanin, ba ya bukatar sai an yi masa dogon bayani da sharhi domin ya fahimci hakikanin abinda yake faruwa.

 Duk wani mai hankali a wannan zamanin, ba ya bukatar sai an yi masa dogon bayani da sharhi domin ya fahimci hakikanin abinda yake faruwa. An shiga wani lokaci da “Masu tabin hankali” suke Mulki. Wadanda abu daa su ka yi Imani da shi, wanda shi ne dole ne kowa da kowa ya mika musu wuya, ya yi musu jujjada. Abin nufi da kowa da koma, ya hada da ‘yan kasarsu, da kuma sauran al’ummun duniya baki daya.

Abinda Trump yake yi wa Iran na yaki da barna da rusau, shi ne yake yi wa abokan Amurka turawa, illa iyaka salo ne ya banbanta. Akansu bai kai ga fara jefa bama-bamai ba, amma yana yi musu ta’addanci na zance.Haka nan kuma abinda yake yi kenan a kudancin Amurka, ya killace ta, ta fuskar tallalin arziki da kudade. Haka nan kuma wasu yankuna da dama a doron kasa.

Salon yadda hulda da mu’amala da abokansa fararen fata na turai, yana cike da dagawa da jiji da kai.  Yana son ya mamaye yankin Greenland,cikin sulhu ko da karfin soja.Bai bar kasar Canada mai makwabtaka da su ba, ita ma yana son ya mamaye ta.

A can Afirka ma wacce dama y arena ta, bai bar mutanenta sun ji da matsalolin da suke damunsu ba. Ya zargi Afirka ta Kudu da cewa, tana yi wa fararen fata kisan kiyashi. Ya kafa mata kahon tsana da takurawa.

Nigeria kuwa ya cewa ya yi wai ana yi wa kiristoci kisan kiyashi.! Da yake ya Renata, sai ya kai mata hari a jajibirin Kirsimet.

 Mutum ne wanda baya jure ace masa “A’a.” So yake kowa ya rusuna a gabansa,a yi masa biyayya kamar yadda ake yi wa sarakunan zamanin jahiliyya.

 Shi kanshi Netanyahu, bai gaza Donald Trump a hauka da tabin kwakwalwa ba. Ya gasmar da kansa cewa shi zababbe ne daga Allah,kuma yana son a sashi a cikin sahun Annabawan Banu-Isra’ila. Zubar da jini a wurinsa da aikata duk wani bakin laifin da a tsawon tarhin bil’adam samun kwatankwacinsa yake da wuya, babu wanda bai aikata ba.

A hakikanin gaskiya, Netanyahu yana a matsayin hoton sahayoniya ne na hakika.

 Wadannan tababbun mutanen biyu sun kulla kawance na aikata laifuka akan bil’adama baki daya da kiyayya da shi. Sun kuwa yi aniyar ci gaba da abinda aka ga sun yi a Gaza, da kuma a Lebanon, sannan a Iran akan duniya baki daya.

Babu abinda zai taka musu birki idan ba abinda Iran take yi ba, na kwanwasar kawukansu, domin su dawo cikin hayyacinsu, su fahimci cewa; Kura ta san gidan mai babbar sanda.

 Abin tambaya ana shi ne a wane sahu mutum zai tsaya, ?

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted