KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156

156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka

156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa an yiwa Imam Hassan bai’a a matsayin Khalifan musulmi a kufa, sannan ya kira taron mashawartansa suka zauna suka kuma fidda wassu al-amura guda biyu don fuskantar Imam Al-Hassan(a). Kuma sune, aika jasusu mai aiko masu labarai sirri daga kasar Iraki, musamman a biranen Kufa da Basra wadanda suka kasance manya-manyan garuruwan a lokacin a kasar Iraki.

Sannan na biyu kuma suna son sayan wasu manya-manyan shugabannin Iraki wadanda suke taimakawa Imam Alhassan (a) don su barshi shikadai, hakan zai tilasta masa ya mika kai ga mu’awiya dan Abusufyan.

Sannan ba tare da bata lokaci ba suka aika mutanen biyu zuwa kasar Iraki, daya a Basra da kuma a Kufa babban birnin daular musulunci karkashin Imam Hassan (a).

A lokacin da wadan nan ma’aikata biyu suka je inda aka turasu suka fara ayyukansu na leken asiri, sai asirinsu ya tonu, Imam Hassan (a) ya tura shurdatul Khamis suka bazu a cikin kufa har sai da suka zakulo jasusun Ma’awiya a cikin birnin suka kawoshi a gaban Imam Alhassan (a) wanda ya bada Umurni a kashe sai aka kashe shi.

Haka ya faru a Basra ma, inda Abdullahi dan Abbas ®   ya sa aka nemo shi aka kuma kama shi aka kawo shi a gabansa ya bada umurni aka kasheshi.

Daga sai Imam Hasan (a) ya rubutawa Mu’awiya wasika, inda a ciki ya aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin kufa da Basar, sannan yayi masa  barazana da yaki. Sannan ya fada masa cewa ya ji labarin ya nuna jin dadi da shahadar mahaifinsa Imam Ali (a).

Mu’awiya ya tsorata ya kuma mayar masa da amsa kan cewa bai ji dadin kasan mahaifinsa ba, amma yaki ya yi magana kan dan leken asirin da ya aika. Haka ma Ibnu Abbas ya rubutawa Mu’awiya wasika yana aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin mutanen Basra. Shi ma mu’awiya ya mayar masa da amsa inda ya  bayyana masa cewa Imam Alhassan (a) ya rubuta masa wasika irin tasa, yana aibata shi. Amma bai bayyanawa Ibn Abba kan cewa Imam Al-Hassan (a) yayi masa barazana da yaki.

Bayan haka sai Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan wasika inda a cikin yake bashi shawara yake kuma kodaitar da shi kan yakar Mu’awiya da kuma wasu dabarbaru da ya bashi. Ga nassin wasikar kamar yadda take.

:Bayan haka, Lalle musulmi sun mayar maka shugabancinsu bayan Aliyu (a), to zage dantse don yaki, ka yi jihadi da makiyinka, ka kusanto da mutanenka, wadanda suke da raunin Imani ka sayi addininsu don kare kanka daga cutar da kai. Ka kuma dora mutane daga manya-manyan gidaje da daukaka don sai danginsu su bika sannan kan jama’a ta hadu, …..

Ka yi koyi da abinda abinda ya zo daga wajen shuwagabanni adilai, suna cewa karya bata halatta sai a yaki… kuma ka san cewa abinda ya sa mutane suka kauracewa mahaifinka suka koma wajen Mu’awiya shi ne shi mai son daidaita rabo a tsakanin, sai wannan yayi masu nauyi.

Kuma ka san cewa kana yakar wanda ya yaki All..da manzonsa(a) a farkonmusulunci ne, har sai da al-amarin All..ya bayyana ya kuma sami rinjaye. A lokacinda aka kadaita Allah aka shafe shirka addini ya daukaka, sai suka bayyana cewa su masu Imani ne a gaban mutane, suka karanta Alkur’ani suna masu istahza’I da ayoyinsa, suka tsaida sallah suna cikin kasala, suna aikata sauran farillu ba da sonsu ba.

A lokacinda suka gani ba wanda zai sami daukaka a adini sai masu tsoron Allah sai suka sifantu da sifofin salihan bayi don musulmi su yi masu zaton alkhairi. Basu gushe a cikin wannan halin bas ai da musulmi suka yi tarayya da su a cikin amanoninsu. Suka ce Allah ne za iyi masu hisabi, idan sun kasance masu gaskiya, to yan’uwammu ne a addini, idan kuma sun kasance makaryata, su ne mafi asara a cikin abunda suka aikata.

Hakika na yi fatan wadan nan da yayansu da wadanda suke kama da su, su kyautata imaninsu, amma wallahi tsawon rai baya kara masu kome sai bata. Kuma bai kara masu, ga ma’abuta addini ba sai kiyayya. Wato sai kara kin abuta addini suke yi.

Ka yakesu kada ka yarda da kaskanci kada ka yada da mika kai garesu. Mahaifinka Aliyu (a) bai karbi shugabanci ba sai ya sami galaba a cikin al-amarinsa, sai ya karba. Sun san cewa shi ya fi cancanta da shugabanci, ko da sun yi hukunci da adalci, amma a lokacinda suka yi hukunci da son zuciya ya koma kan inda yake, har ajalinsa ya zo masa.

Kada ka fice daga gaskiya wanda kai kafi cancanta, kai kafi dacewa da shi har zuwa lokacinda mutuwa zata shiga tsakaninka da ita.

Wassalam.

Wasikar dan Abbas ta kunshi wadannan abubuwa kamar haka.

01-Iban Abbas yana bawa Imam Al-Hassan (a) shawara kan ya sanya manya-manyan mutane, kuma wadanda maganarsu take tasiri a cikin mutane a matsayin ma’aikatar gwamnatinsa don sayan wadanda suke da Rauni a imaninsu, wanda kuma zai kawo hadin kan al-umma, mutane su zama jama’a guda. Da haka kuma zai sami ikon yakar mu’awiya.

A nan malamai suna cewa Ibn Abbas ya gafala daga siyasar gaskiya tsantsanta wacce limamai Ahlul baiti (a) suke tafiya a kai. Sabanin duk hanyoyin da suka yi hannun riga da asasin addinin musulunci. Ko da kuwa hanyoyin suna aya kaiwa ga nasara a nan duniya.

02-Ya gabatar da abubuwanda a ganinsa suka sanya mutane suka akauracewa Imam Ali(a), wanda ya sa bai sami nasarorin da yakamata ya samu ba, da kuma yadda mu’awiya ya kai ga nasarorin da ya samu.

 Imam Ali (a) ya kama hanyar adalci da kuma daidaita tsakanin ummar musulmi a cikin rabon duniya. Baya Fifita wani a kan wani don matsayinsa ko danginsa a cikin al-ummar.  Kuma yayi haka ne don shi ne addinin musulunci ya zo da shi. Kuma shi ne yake cikin nassin ayoyin alkur’ani suka tabbatar, na rashin bambanta tsakanin baki da fari, sannan ya rusa katangar da ke tsakanin mawadaci da talaka, ya sanya (mutane dai dai suke kamar hakoran mastefi, dukkaninsu daga Adama, kuma Adama daga turbaya ne.) babu bambanci tsakanin wani da wani sai da tsoron Allah, babu fifiko tsakanin wani da wani, sai a aiki da kuma cancanta.

Imam Ali (a) ya tafi a wannan hanyar har sai da ya zama abin buga misali a tsawon tarihi na dai-daita tsakanin mutane, da kuma adalci a tsakaninsu. Yana daga cikin rabon adalci da kuma dai daita tsakanin mutane wanda Imam Ali (a) ya gina shugabancinsa a kai wani lokaci ya dai-daita tsakanin wata bakuraishiya da kuyanganta a rabo, sai ta zo masa a fusace tana cewa: shin kana dai daita tsakanina da wannan kuyanga ta a rabo?

Sai Imam (a) ya kalleta da gefen idanunsa, sai sanya hanunsa a kasa, ya debo turbaya yana jujjuyata a cikin hannunsa,  yana cewa: Wannan turbayan bangarensa bai fi wani bangare ba.

Wannan adalcin, wannan daidaito tsakanin mutane, yayi nauyi ga mafi yawansu saboda da dama daga cikinsu, suna son maslahar kansu ne kawai. Don haka suka kauracewa gwamnatin adalci, suka je suka mika kansu ga hukumar Mu’awiya wacce bata da wata manufa ta Alkhairi da adalci, sai biyan bukatu, da sha’awar shuwagabanninta da kuma cimma manufofinta ta ko wace hanya.

03-Ya kawo yadda Banu umayya suka kasance suna yakar Allah da manzonsa, (s) har saida Allah ya daukaka addininsa, gaskiya ta sami nasara. Suka mika wuya ga musulunci ba don sun yi Imani da shi ba, sai dai don tsoron takobi. Suna karatun ayoyin Alkur’ani tare da isgili da ayoyinsu, suna tsaida sallah a cikin kasala, suna aikata addinin bisa dole ba don suna so ba.

Sannan a lokacinda suka ga cewa ba mai samun daukaka a cikin addinin, kamar yadda Allah yake cewa {mafi girma a wajen Allah a tsakaninku shi ne wanda ya fiku tsoron Allah}

Daga nan sai suka fara sifantuwa da halayen salihan bayi, har sai da suka sami karbuwa a wajen musulmi. Wasu musulmu sunkarbesu amma suna shakkan imaninsu.. 04-Ibn Abbas ya kodaitar da Imam kan yakar wadan nan kafirai-a cikin zuciyarsu amma wadanda suka bayyana Imani da kuma ayyukan salihai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments