Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 177

177- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi

177- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur'ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddin Romi. Ko kuma dai cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatima (s) diyar

manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata munci gaba da kawo maku abubuwan da Mu'awiya dan Abusufyan ya aikata a lokacinda al-amuran shugabanci suka koma hannunsa.

Daga ciki mun ambaci yadda ya jagoranci kirkiro hadisan karya, wadanda suka jinginasu ga manzon Allah (s), don daukaka ma'awiya wanda gidansu banu Umayya basu da wata falaha a farkon musulunci sai dai su suka tsaya a gaban manzon hana (s) na tsawon shekaru kimani 21 suna yakarsa suna hana yaduwar addinin musulunci. Su suka yaki manzon Allah (s) a yaki na farko a musulunci wato yakin Badar, inda aka halaka shuwagabanninsu, wadanda suka hada da Utba da shaiba da walid dan Ubta mahaifi ammi da kuma dan,uwan Hindu matar Abusufyan kuma mahaifiyar Mu'awiya.

Su suka jagorancin yakin Uhudu inda hindu ta sa aka kashe Hamza ammin manzon Allah (S) sannan ta sa aka yi masa muthala kuma ta ci hantarsa. Abusufyan ne ya jagoranci yakin Ahzab yaki mafi girma wanda Kurasihawa suka dorawa musulmi. Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda manzon Allah (s) ya kwace birnin Makka a hannunsu, suka musulunta a dole, ko kuma a katse  wuyarsu saboda laifukan da suka aikata.

Don haka bayan fatahin makka sun mika wuya ne basu musulunta ba, shi ya sa manzon Allah (s) ya sanyasu cikin mu'allafatu kulubuhim. Amma bayan shekaru kimani 40 da hijira, mu'awiya wanda ya sha kiyayyar manzon Allah (s) da iyalan gidansa daga iyayensa, ya so ya samarwa danginsa Banu Umayya daukaka da matsayi a addinin musulunci wanda babu su. Don haka sai ya fake da kirkiran hadisan karya wadanda suka jinginawa manzon Allah (a). da kuma wasu hadisan wadanda suke kaskanta  manzon Allah (s) da kuma danginsa masu tsarki, wanda Aliyu dan Abitalib (a) shi ne shugabansu.

A cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar daya daga cikin hadisan da suka kirkiro na kaskanta iyalan gidan manzon Allah (s), wanda kuma shi ne hadisin Abdullahi dan Umar wanda yake magana kan cewa, wai a zamanin manzon Allah (s) basa daukar wani da daraja fiye da Abubakar da Umar da Uthman.

Wanda kuma daga wannan hadisin ne suka fidda akidar khalifofi rashiduna  3 ne, Abubakar da Umar da kuma Uthmanu, inda suka fidda Aliyu (a) daga zama na 4, suke son kuma maye gurbinsa da Mu'awiya dan Abusufyan.

Amma wannan akidar ta kawo rarraba a cikin musulmi har zuwa zamanin sarki Haruna Rashid daya daga cikin sarakunan Abbasiya, wanda bayan ya fahinci makircin da ke cikin wannan akidar, tare da taimakon malaman Ahmad bin Hambal ya amince da sanya Aliyu (a) a matsayin Khalifa na 4.

Mun kuma bayyana cewa da hake ne ahlussunna waljama'a suka amince da sanya Aliyu dan Abutalib a matsayin khalifa na 4 daga cikin khalifofi Rashidun. Mun bayyana cewa a cikin ahlussunna akwai wadanda basu yarda da khalifancin Imam Ali(a) ba har yanzun, kuma su ne wahhabiyawa, amma mafi yawan su sun sanya shi a matsayin khalifa na 4. Kuma suna girmama iyalan gidan manzon Allah (s).

Amma malaman shi'a mun bayyana cewa suna ganin Imam Ali (a) a matsayin Khalifan manzon Allah (s) wasiyyinsa da kuma magajin ilminsa, kofar ilminsa, sonsa Imani kinsa munafurci, yakarsa yakar manzon Allah (s) ne. Wadan nan duk tare da kafa hujjoji daga cikin ayoyin alkur'ani da

daruruwan kuma ingantattun hadisan manzon Allah (s). Daga cikinsu mun kawo maku hadisin Khuzaifa dan Yaman daya daga cikin manya-manyan sahabban manzon Allah (s) wanda kuma aka sanshi da cewa shi maabucin sirrin manzon Allah (s), ne na sunayen wadanda suka yi kokarin kashe shi a akabar-Tabuka. Yana fada dangane da Imam Ali (a) kan cewa : Aikinsa a yakin Khandak na kashe Amru dan Abdu wad, ya fi ayyukan al-ummarsa daga lokacin har zuwa ranar kiyama. Abu Hatam Ahmad dan Ahamdan Razi dangane da Shi'anci, yana cewa: Sunar mazhaba ta farko a musulunci wacce ta bayyana a lokacin rayuwar manzon Allah (s) itace mazhabar shi’a. kuma a lokacinda ana kiran mutane hudu daga cikin sahabban manzon Allah (s) da wannan sunan. Kuma suna Miqdad dan Aswada, Salman Alfarisi, Ammar dan yasir da kuma Abu zar Alghifari. Kamar yadda ya kawo shi a cikin littafinsa  (الزینة فی الکلمات الإسلامیة العربیة:ج3، ص259).

Banda wannan akwai manya-manyan sahabban manzon Allah (s) wadanda suka hada da Salman Alfarisi, Abuzaril Ghiffari, Mikdad dan Aswad, Khabbat dan Arat, Jabir dan Abdullahil Ansari, Abusa'idnil Khuduri, Zaid dan Arkam, duk sun yi Imani da cewa Ali (a) shi ne musulmi na farko, kuma ba wani daga cikin sahabban manzon Allah (s) wanda ya kai shi daraja ko ya kai matsayinsa.

Aban dan Taglab ( R ) ya ce shi'anci ya yadu a cikin sahabban manzon Allah (s) da tabi'ina da kuma wadanda suka bisu, kuma suka rawaito hadisan manzon Allah (s) da dama dangane da hakan. Idan mun yi watsi da hadisan da suka ruwaito zamu rasa hadisan manzon Allah (s) da dama. Wannan kamar yadda ya zo cikin Usdul Gabah fi Ma'arifatus Sahaba JZ 4 SH 18. Da wasu littafai da dama.

Ibn Khaldun Al-Maliki ya rubuta a cikin wani littafinsa, yana cewa: wasu daga cikin sahabban manzon Allah (s) wadanda suka hada da Zubair dan Awwam, Ammar dan Yasir, Mikdad dan Aswad suna daga cikin shi’ar Imam  Ali, kuma suna ganin ya fi cancanta da shugabanci fiye da kowa a cikin sahabban manzon Allah (s).

A wani rubutun yana cewa a cikin sahabban manzon Allah (s), Khazifa dan Yaman, Zubair dan Awwam, huzaimatu dan Thabit wanda aka fi saninsa da Zushahadataini, Abul-Haitham Malik dan Tayyahan Hashimu dan Utbah wanda aka fi saninsa da Mirqal, Abu ayyubal Ansari, Ammar dan Yasir, Abu sa'idinil Khuduri, Abu Rafiu, Adiy dan htam Atta'ii, Amru dan Hamq Alkhaza'ii, Hijir dan Adiy Al-kindi, Sa'id dan Jubair, Uthman dan Hunaif Al- ansari, Sahal dan Hunaif, Ubay dan Kaabu, Bara'atu dan Azib, Ahnaf dan Kais, Thabit ibn Kais ibnu Khatam, Sa'adu dan Ubada.

Kais dan Sa'adu dan Ubada, Habbab dan Arat, Bilal ladanin manzon Allah (s), Abdullahi dan Budail, Muhammad Budail, Karzatah dan Kaabu Al-Khuza'I, Sulaiman dan Surad al-khuzaee, Anas dan Haritha, Abukatada Al-Ansari, Abudujana Al-Ansari, Sa'ad bin Mas'ud Athaqafi ammin Mukhtar athaqafi. Yazid dan Nuwairah, Nafi'u dan Utbah, Salman Alfarisi, Abu-laila Al-ansari, Abu Tufail Amir dan Wathilah, Abdullahi dan Abbas da sauransu.. duk suna cikin sahabban manzon Allah wadanda suke tare da Aliyu dan Abitalib, suna daga cikin mataimakansa kuma shi'arsa(s).

Sannan a cikin tabi'ai akwai, malaman hadisi da malaman fikihu, kamar Sulaiman dan Mehron Aamash, Nu’uman dan Thabit,

Shaabatu dan Hajjaj Abdurrazak san’ani, Ubaidullahi dan Musa, Abdurrahman dan Abi Hatam, Sufyan Al-Thauri, duk suma cikin masoyam Imam Ali(a). Kuma suna ganin yafi Uthman daraja. Tare da wannan dimbin sahabban manzon Allah (s) da malamai daga cikin tabi'ina, da suke tare da shi. Zamu kara da cewa manzon Allah (s) yana cewa{Ya Aliyu! Baka ji inda Allah mai girma da daukaka yake cewa {Lalle wadanda suka yi Imani kuma suka aikata ayyuka na gari, wadannan su ne mafi nagartan halittu.. } sai yace:

Sune kai da shi'arka, haduwata da ku tabkin Al-kauthara, idan al-ummu sun taru don hisabi, za'a kira ku, Gurran Muhajjalina.} a wani hadisin ya ce: Su ne kai da shi'arka, zaka zo kai da shi'arka ranar qiyama, kuna masu yarda sannan yardaddu, kuma makiyinka zai zo suna cikin fushi … har zuwa inda Aliyu (a) yace: Su waye makiya na ya manzon Allah!? Sai yace: wanda ya barranta kansa daga gareka ya kuma la'aneka, sai manzon Allah (s) yace: Wanda yace Allah ya jikan Aliyu, Allah ya jikansa. .. da wasu hadisai da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted