178-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddin Romi. Ko kuma dai cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatima (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku hadisan karya wadanda aka jinginawa manzon Allah (s) a zamanin Mu’awiya dan Abusufyan. Mun ji yadda Imam Muhammad Bakir (a) limami na 5 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon Allah(s) ya karyata irin wadan nan hadisan da dama, ya kuma kawo hadisan karya da suka kirkiro har kimani 200, wanda misali ne kawai ba su Kenan ba.
Malaman hadisi sun bayyana cewa mafi yawan hadisan karya wadanda aka kirkiroso dangane da falalar Khalifa Abubakar da kuma Umar an kirkirosu ne a zamanin Mu’awiya dan Abusufyan don samun kusanci a gare shi sannan shi kuma yana ganin wadanda hadisan suna iya cutar da iyalan gidan manzon Allah (s) su kuma rage matsayinsu a cikin musulmi.
Kamar yadda muka fada a cikin shirimmu da ya gabata, banda kirkiro jadisai na falalar sahabban manzon Allah (s) musamman khalifofi na biyu na farko. Mu’awiya bai takaita da haka ba, ya sa aka kirkiro hadisai wadanda suka aibata iyalan gidan manzon Allah (s) su rage matsayinsu a wajen mutane su kuma batar da dukkan falalolinsu wanda manzon Allah (s). Kuma ya kashe kudade masu yawa saboda haka.
Daga ciki ya bawa dogarinsa, Samratah dan Jundubi dinari dubu 400 kan ya hau kan mimbari yayi Khuduba ya ce wannan ayar inda Allah Ta’ala yake cewa.
{Daga cikin mutane akwai wanda zancensa a rayuwar duniya tana kayatar da kai, alhali yana nunawa Allah abinda ke cikin zuciyarsa, kan cewa shi mai tsananin husuma ne. Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da ‘ya’yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna.}. Bakara Ya. 204. Kan cewa ayoyin sun sauka kan Aliyu dan Abitalib (a). Sai Samrata ya ruwaito hadisi ya jingina shi da manzon Allah(s) ya tabbatar da cewa ayar ta sauka a kan Aliyu dan Abitalib (a).
Sai Mu’awiya ya debi kudade daga baitul Mali yabashi. Wannan kamar yadda ya zo cikin littafin Nasa’ihul Kafiya SH 253.
Allah ya yi izini a yi amfani da kudaden musulmi wajen taimakawa musulmi raunana, mabukata, amma dan Hindu yana bada su don dushe hasken Allah (a), Yana yakar addinin musulunci da kudaden, da kuma waliyan Allah Ta’ala.
Don haka, masu kodayi duniya daga cikin sahabban manzon Allah (s) sun kirkiro hadisai wadanda suka jinginasu ga manzon Allah (s) don kaskanta iyalan gidan manzon Allah (s) a cikin musulmi.
A wani kirkirerren hadisi wanda Amru dan Asi ya ruwaito, ya fadawa mutanen sham kan cewa manzon Allah (s) ya fada dangane da dangin amminsa Abutalib (a) {Lalle dangin Abutalin ba sune masu jibantan al-amari na ba, Lalle masu jibantan al-amarina sune, Allah da salihan muminai). Kamar yadda ya zo cikin sharhin Nahjul Balgaha na Ibnu Abil Hadid JZ 11 SH na 42.
Da haka kwamitin kirkiro hadisai na Mu’awiya suka yi ta kirkirosu suna aibata zurriyyar manzon Allah (s), suna kokarin dushe hasken Allah, suna nisantar da shuwagabannin musulmi wadanda Allah ya tsarkakasu, ya kuma sanyasu shuwagabannin su har duniya ta nade.
Ibn Abil Hadid wanda ya rubuta sharhin Nahjul Balagha mai mujalladi 10, yana cewa malaminsa Abu Jaafaru Al-Iskafi yana cewa Mu’awiya dan Abusufyan ya samu wasu daga cikin sahabban manzon Allah (s) da kuma wasu tabi’ai suka kirkiro hadisan suka jinginawa manzon Allah (s) don munana Aliyu dan Abitalib (a) da kuma tauya matsayinsa, da kuma aibata shi, don sa mutane su barranta daga gareshi. Ya kuma sanya masu kudade da dukiyoyi wanda zasu yi kodayin mallakarsu, sai suka yi ta kirkiru hadisai irin wadanda yake so. Daga cikinsu akwai Abuhurairah da Amru dan Asi, da Mughira dan Shu’abah, daga cikin Tabi’ai kuma akwai Arwatu dan Zubair. Kamar yadda ya zo cikin sharhin Nahjul Balagha na ibnu Abulhadid JZ 4 SH na 63.
Wadan nan matakan da Mu’awiya ya dauka dai sun sabbaba rabuwan kai a tsakanin musulmi, kuma da haka ya bude kofar kariyawa wa Allah da manzon Sa (s). Kuma zababbun malamai daga cikin sahabban manzon Allah (s), sun kauracewa wadannan hadisan.
Bashir Al-Adwi daya daga cikin malaman hadisi a Basra, ya zo wajen Ibn Abbas yana ruwaito masa hadisan manzon Allah (s) sai Ibn Abbas ya yi banza da shi ya kuma wulakanta shi. Sai Bashir yayi Fushi. Sai Ibnu Abbas ya ce masa: Mun kasance a da can, idan ana ruwaito mana hadisan manzon Allah (s) mukan bude idanumma mu kuma kasa kunnuwammu da wanda yake ruwaito hadisai, amma bayanda suka fara karya wa manzon Allah (s) bama karban hadisi daga wajen kowa sai wadanda dama mun san su. Kamar yadda ya zo cikin ‘Figrul Islam SH 258.
Sai dai abin bakin ciki da kirkiran hadisan da Mu’awiya yayi, shi ne da dama daga cikin hadisan sun isa wajen malaman hadisi sun rubuta su a cikin littafansu, sun kuma karantar da su dalibansu. Kuma babu shakka da sun san cewa wadan nan hadisan karya ne ba manzon Allah (s) ne ya fadesu ba da basu rubutasu ba, basu kuma bada wani muhimmanci garesu ba.
Har’ila yau a wata zancen Ibnu Abil Hadidi dangane da hadisan karya da aka junginawa manzon Allah (s) .
(Kirkirarrun hadisai da dama sun bayyana, sannan malamai da alkalai da kuma shuwagabanni sun dade suna amfani da wadan nan hadisan. Kuma wadanda suka zama bala’ii babba ga musulmi sune malaman da suke bayyana tsoron Allah ga mutane, amma kuma suna kirkiro hadisan karya, suna yadasu, don samun abinda duniya, na kudade da gidaje da kyaututtuka daga hannun sarakuna. Amma daga baya sai wadan nan hadisan suka shiga hannun ma’abuta addini, wadanda su basa karya, kuma ba zasu taba amincewa da hadisan karya da sun sani ba, suka karbi wadan nan hadisan suka ruwaitosu, suka rubutasu a cikin littafansu, suna tsammanin cewa hadisan gaskiya ne, da sun sani ba su yi amfani da su ba , kuma ba zasu ruwaitosu ba) Sharhin Nahjul Balagha, ibnu Abil Hadis JZ na 11 SH-45.
Haka ma littafan nasu suna dauke da hakayoyi na Banu Isra’ila wadanda wasu sahabban manzon Allah (s) kamar Abu Hurairah ya ruwaitosu daga yahudawan da suka musulunta suka kuma shiga cikin musulmi suka yada hakayoyi na banu Isra’ila wadanda addinin musulunci bai amince da su ba.
Mai littafin Tazkiratul Huffaz, ya bayyana cewa da khalifofi na farko sun tara hadisan manzon Allah (s) tun bayan wafatinsa da hakan bai faru ba. Da al-ummansa (s) bata rarraba ba. Amma basu aikata haka ba. Saboda khalifa Abubakar ya tattara hadisan manzon Allah (s) ya kona su. Sannan Umar ya zo bayansa ya nemi shawarar shabban manzon Allah (s) dangane da tara hadisansa (s) har suka basu hadisan da suka rubuta sai bayan wani lokaci ya ce ya fasa. Sai yace masu (Lalle ni na ambata maku dangane da rubuta sunna, amma na tuna cewa wasu mutane daga cikin Ahlul Kitabi a gabaninsu sun rubuta littafai, tare da littafin Allah sai suka koma kansu suka manta da littafin Allah, don haka ni wallah b azan hada littafin Allah da wani abu ba). Sai ya kona hatta hadisan da sahabbai suka bashi aro don ya tattara sunnar manzon Allah(s). Taqyidul Ilmi. 49. Da kuma Hami’il bayanul Ilmi wa Fadlihi. JZ 01 SH 77.
Wannan dalilin da ya bayar da rashin haduwar hadisai da littafin Allah, ba abinda hankali zai karba ba. Don hakan zai faru ne da ace hadisan sun sabawa littafin Allah. Amma hadisan manzon Allah (s) suna fassara littafin Allah ne, don haka ba zasu saba masa ba. Suna fassara ayoyin al-kur’ani ne ta yaya zasu karkatar da mutane daga littafin Allah?.
Babban abinda malamai suke zato ya hanasu tattara hadisan manzon Allah (s) dai shi ne, bangare mai yawa daga cikin hadisan suna dauke da umurnin manzon Allah (s) na bin iyalan gidansa, da kuma komawa a garesu saboda sune jagorori bayansa. Sabanin abinda su suka yi. Sannan ba zasu iya ware wasu hadisan su kadai su rubutasu su ki rubutun hadisan da suka shafi iyalan gidan manzon Allah (s) ba.
Don haka tara hadisan manzon Allah (s) zai fallasasu da sauri. Tunda sun rika sun bayyana cewa, ba zasu taba abincewa annabci da kuma khalifanci su hadu a gida guda ba. Kuma shi yasa, a lokacinda ya kusan wafati, ya bukaci su bashi abin rubutu ya rabuta masu abunda ba zasu taba bata ba har abada sai suna hana shi, suka ce littafin Allah ya ishesu. Saboda ya sha fada masu su rike littafin Allah da kuma iyalan gidansa idan basa son bata.
Don haka basa son ganin wadan nan hadisan wadanda suke tabbatar da hakkin shugabancin iyalan gidan manzon Allah (s) a bayansa.
Don haka kirkiran hadisan karya wadanda Mu’awiya yayi a cikin shekaru kimani 20 da yayi yana shugabancin Al-ummar Musulmi ya rarrabasu a cikin dukkan al-amura. Sun yi sabani mai tsanani a tsakaninsu, kuma suna kan hakan har yanzun. Wannan yana daga cikin bala’inda da ya sami al-ummar Musulmi bayan wafatin manzon Allah (s) wanda Mu’awiya ya haddasa.