Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 189

189-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

189-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin siarar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da magana kan siyasar Iyalan gidan manzon Allah (s) a gaban irin ta’asan da Mu’awiya  dan Abusufyan ya aikata, da shi da ma’aikatansa bayan ya sami iko da daular musulunci. Inda muka bayyana cewa Iyalan gidan manzon Allah (s) su wakilan Allah ne a bayan kasa, don haka basa kuskure a cikin siyasarsu a gaban wadan nan mujrimai wadanda suka kwace iko daga hannunsu bayan wafatin manzon Allah (s).

Don haka siyasarsu ita ce siyasar addinin musulunci na gaskiya, Tunda basa sabawa littafin Allah sannan ba sa sabawa sunnar manzon Allah (s). Mun yi Magana dangane da matsayin su dangane da khalifancin kanta, muka tabbatar da cewa, itace siyasar  Alkur’ani mai girma, itace siyasar manzon Allah (s). Mun yi maganar adalci inda muka tabbatar da cewa shi ne ginshikin shugabanci a wajensu, mun yi maganar dai daito a rabon dukiyar Al-umma, sai muka tabbatar da cewa siyasarsu a wannan bangaren ne ya sanya mafi yawan larabawa suka tsani Amirul muminina (s) har suka kai ga yakarsa a Jamal da Siffin.

Munyi maganar makirci, wanda mu’awiya da ma’aikatansa suka yi ta yi kan iyalan gidan manzon Allah Musamman Imam Ali (a) da dansa Imam Hassan (a) mun tabbatar da cewa, makirci da kha’inci da yaudara duk basa cikin hanyoyin da suke bi wajen shugabantar al-ummar Musulmi. Sannan a dayan bangare gaskiya da fadinta da aikatata sune a gabansu. Don basa son duka abinda zai kasu sabawa Allah T. saboda fadin gaskiya da kuma aiwatar da ita a kasa Imam Ali (a) ya rasa damar zama khalifa na ukku. Da sauransu.

A yauma zamu dora daga inda muka tsaya, inda zamu fara da inda Imam Ali(a) yake cewa

{In ba don makirci da kuma yaudara zai kai ga wuta ba, da na kasance wanda ya fi kowa iya makirci a cikin mutane}.

Sau da dama labarai sukan zo masa dangane da makircin da ake masa yana Kufa, sai yayi nishin ajiyar zuciya sain yace {Kaito na ! Suna mani makirci sun kuma tabbatar da cewa na san da hakan, kuma na fi su sanin hanyoyin makirci, sai dai ni na san cewa makirci da yaudari hanyar wuta ce, sai in yi hakuri a kan makircinsu kuma b azan aikata abinda suka aikata ba}.

A wani hadisin yana cewa {Duk mai yaudara zai zo ranar kiyama dauke da tuta, wacce za’a gane shi da ita}.

Ita yaudara tana bayyana ne a cikin zuciya wacce bata yi Imani da mutuncin dan adam ba, bata yi Imani da ginshikan addini ba, Imam Ali (a) yana sifanta mai yaudara a matsayin wanda aka shafin imani a cikin zuciyarsa. Yana cewa

{Lalle cika alkawali dayan tagwayen gaskiya ne, ban taba sanin garkuwa wanda ya fi shi kariya daga bata ba, Kuma wanda ya san yadda makoma (lahira take} ba zai  yaudari wani  ba. Amma hakika muna cikin wani zamani wanda mafi yawann mutane suke daukar yaudara wayo ne, sannan jahilai sun danganta hakan da kekyawar dabara.

Me ya samesu! Allah ya la’anesu, hakiki, masu wannan aiki suna gabatar da dalilai na yin hakan, don sabawa umurnin Allah da haninsa, bayan sun ganshi a gabansu. Amma kuma sai su ga dama ce ta nema mata mafati da sunan addini}.

Wasu daga cikin wadanda suke bin son zuciyarsu, ko suke neman matsayi a fadojin wadannan wadannan sarakuna, kan cewa Imam Ali(a) bai san siyasa ba, bai iya jagoranci ba, kuma Mu’awiya ya kware a cikinta. Kuma shi ya fi cancanta da shugabancin.

A wani wuri Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) yana cewa {Wallahi 1 ! Mu’awiya bai fi ni way oba, said ai yana yaudara yana sabo, kuma ba don kin yaudara ba da na fi kowa wayo, said ai duk wani mai yaudara mai sabo ne, kuma duk mai sabo kafiri ne}.

Don haka dukkan siyasar Amirul Muminina (s) da kuma sauran limamaim masu tsari daga yayansa (a) shi ne siyasar musulunci tsantsa, wacce ba ta amince da yaudara, ko makirci, ko kodaitarwa zuwa abinda ba gaskiya ba. Siyasarsu bata yi Imani da dukkan hanyoyi na munafurci ba a cikin al-umma ba. Ko da kuwa wadan nan hanyoyi suna iya basu nasara a kan makiyansu na wani lokaci kuwa.

Saboda shi khalifanci a addinin musulunci yana da matukar muhimmanci a yada gaskiya da halaye masu kyau wansa Allah ya sauko da shi. Dole ne ya zamanto wadanda suke iya rike khalifanci su zama da farko masana cikekken addinin, sannan suna da imina mai zurfi tabbatacce, da shi.

Imam Al-Hassan dan Ali (a) bayan shahadar mahaifinsa ya tafi a kan tafarkinsa, da siyasarsa, don haka bai yi amfani da duk wata hanya wacce addinin musulunci bai amince da shi ba, a gwagwarmayar da Mu’awiya dan Abu sufyan ba.

Ya nisanci dukkan hanyoyi wadanda basa kaiwa ga hakika da kuma gaskiya ba. Kuma da ya bi ko da daya daga cikin hanyoyin da mu’awiya ya bi, da bai sami nasara a kansa ba.

Wannan matsayin na Imam Al-Hassan (s) ya rikita hatta wadanda suka fi kusa da shi, wadanda kuma suka kasance Mabiya iyalan gidan manzon Allah (s) a lokacin, kamar Sulaiman dan Sard. Wanda ya zo ya nuna damuwarsa da matakan da Imam (a) ya dauka ha rya kaiga sulhuntawa da Mu’awiya da kuma mika masa ragamar shugabancin musulmi ba tare da yaki ba.

Amma sai Imam Al-Hassan (a) ya fada masa cewa

{Da na kasance ina aiki don neman duniya, ko kuma ina neman sarauta, (ka san cewa) Mu’awiya bai fi ni jarunta ba, bai fi iya dauriya, da kuma riko da manufa ba, said ai ni ina ganin abinda bakwa gani, bana nufi da abinda na aikata in banda hana zubar da jini ba}.

Wannan hadisin ya nuna mana cewa, da Imam Hassan (a) yana neman duniya ne, (Allah ya kiyaye shi) ko matsayi a cikinta da babu shakka da ya ami galaba a kan Mu’awiya san Abu sufyan. Saboda hanyoyin zuwa ga samun shugabanci da jawo hankalin mutane su bi shi ba hanyoyi ne wadanda musulunci ya amince da su ba.

Shi kuma a matsayin sa limamai mai tsari baya halatta a gareshi, kuma bai kamata ba, ya bi hanya ko hanyoyi ta kaiwa ga shugabanci wadanda addinin musulunci basu amince da su ba.

Banda haka ya fi ko wani musulmi a doron kasa a lokacin kodayin kare addinin musulunci daga gurbata da kuma sanin abinda ya kasance masalaha ga al-ummar musulmi.

Sai kuma ma’aikatansu, wati wani irin mutane ne Ahlul Baiti suke dauka a matsayin masu taimaka masu wajen gudanar da harkokin shugabanci a garuruwa da wurare da suke nesa da su? Ko kuma a matsayin kwamandojin sojojinsu? Ko dai don taimaka masa a cikin a harkokin gudanarwa?.

Saboda yana daga cikin al-amura masu hatsari a cikin shugabanci, shugaba ya hana mutane hakkinsu, sai sun bi ta hanyoyin da basu dace ba, kamar cin hanci da rashawa don samun hakkinsu.

Ko way a san cin hanci da rashawa suna jawo rashin aminci a cikin al-umma ga shuwagabanni. Sukan lalata al-umma ha rya zama talaka zai debe kauna daga adalcin shuwagabanni, sannan talauci da rashi su kaisu ga aikata laifuffuka, wadanda suka hada da sata da kuma kissan kai, da bayyanar fasadi daban-daban a cikin al-umma. Da rashin adalci da kuma yaduwar zalunci.

Dangane da wannan Imam Ali (A) ya rubutawa daya daga cikin ma’aikatansa wasika yana fada masa, salon shugabanci yana cewa

{Bayan haka ! Lalle wadanda suka zo gabaninsu sun halaka ne, a lokacinda suka hana mutanen hakkokinsu, Sai ya zama masu dole su sayi hakkokinsu daga shuwagabanninsu, sai shuwagabannin suka kaisu hanyar bata sai su kuma suka bisu, (aka taru aka lalace}.

Su iyalan gidan manzon Allah (s) suna hangen fiye da wannan, saboda sun tilastawa ma’aikatansu nisantar karban kyauta ko gudanar da harkar kasuwanci da mutane, ko da kuwa su na kusa da su ne a dangi, saboda kada su yi tasiri wajen adalcin da yakamata su gudanar a cikin al-umma.

Don haka ne Amirul muminina (a) a lokacinda labari ya zo masa kan cewa Sahal Dan Hunaif, ma’akacinsa a Basra ya halarci wani biki wanda wani mai kudi a Basra ya gayyace shi, sai ya rubata basa wasika yana aibata shi yana cewa:

{Bayan haka! Ya kai dan Hunaif! Labari ya zo mani kan cewa wani mutum daga cikin matasa masu kudi a Basar ya gayyana ce ka zuwa biki, sai ka gaggauta karban gayyatar, inda aka gabatar maka nau’oin abinci, aka kawo maka manya-manyan kwanukan abinci, ban tsamman, yanda nake zatonka, zaka amsa wannan gayyatar wadan nan mutane ba, wadanda suke nisantar da talakawa, su kuma kira mawadatansu ba. Amma ka duba a cikin abinda aka gabatar maka na abinci, wanda kake shakkan cewa an same shi ta hanyar da bata dace ba, kada ka ci, sannan wanda ka tabbatar da halaccinsa ka ci}.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments