Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 174

174-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda

174-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddin Romi. Ko kuma dai cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatima (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun fara magana kan al-amura wadanda Mu’awiya dan Abusufyan, yake sabawa manzon Allah (s) ko yake sabawa addinin musulunci tun lokacinda iko ya koma hannunsa.

Daga ciki, mun ambaci yadda yake bayyana kiyayya ga manzon Allah (s) amma a boye, mun ji yadda tattaunawar sa da Mughira dan Shuba ta kasance. Inda ya bayyana hakikanin abinda yake cikin ziciyarsa. Wanda kuma ya nuna cewa bai taba musulunta ba.

Mu’awiya yakan ci riba, ya sanya rigunan da aka saka daga alhariri da kuma dibaji, yana karban zakka a kan kyauta, ya kuma kwace dukiyar mutane, ya ki aiwatar da haddin musulunci. Sannan mafi muni daga cikinsu yana sanya sahabban manzon Allah (s) su kirkiro masa hadisai wadanda yake samarwa danginsa banu Umayya daukaka, su kuma kaskanta iyalan gidan manzon Allah (s) da su. su daukaka khalifofi uku da suka gabaci Amirulmuminina (a).

Ya bada umurnin a kirkiro hadisan manzon Allah (s) wadanda suke daukaka wasu sahabban manzon Allah (s) wadanda suke tare da shi. Umurni na farko wanda ya bayar dangane da wannan shi, wata takarda guda, da ya rubuta ga ma’aikatansa da gwamnoninsa inda yake cewa

(ku duba daga cikin masoyan Uthmanu wadanda suka ruwaito hadisan Falalarsa, suke kuma magana kan babban matsayinsa, ku kusanto da su ku daukaka su, ku rubuta mani hadisan da ko wanne daga cikinsu ya ruwaito dangane da shi, ku rubuta mani sunayensu da sunayen iyayensu da kuma abinda suka ruwaito.)

Daga nan sai ma’aikatansa suka zage dantse suka kusanto da wadannan masu kirkiro hadisai, suka rika basu kudade suna ta ruwaito hadisan karya suna jinginawa manzon Allah (s) dangane da falalar khalifa Uthman da Mu’awiya da kuma Banu Umayya.

Daga cikin falalolin Mu’awiya da suka kirkiro har da wannan hadisin, wanda suka ce manzon Allah (S) ya na fada dangane da shi (Ya Ubangiji ka sanar da shi littafi da lissafi, ka kiyaye shi daga azab, ka kuma sa shi a aljanna).

A wani hadisi kirkirerre, wanda tirmizi ya rauwaito yana cewa (Ya Ubanguji ka sa shi shiryeyye mai shiryatarwa).

Sannan a wani hadisi wanda Harith dan Abu Usama ya rawaito yana cewa, manzon Allah (s) yana cewa: Abubakar shi ne mafi tausayawa da kuma jin kai a cikin al-ummata.

A wani hadisin kuma suka ce yace (Mu’awiya dan Abusufyan shi ne mafi hakuri cikin al-ummata, kuma mafi yawan kyautarsu). A wani hadisin yana cewa (Ma’abucin sirrina, Mu’awiya dan Abusufyan.). Kamar yadda yazo cikin littafin Tathirul Jinan shafi na 26.

Ibnu Hajar Al-asqalan ya ruwaito wannan hadisin da aka kirkiro, sannan ya yi amfanida shi ya karyata dukkan abubuwan da ake zargin Mu’awaiya ya aikata, na na laifuffuka, ya kuma wanke shi daga aikata wani laifi. Ya sanya shi cikin nagartattun sahabban manzon Allah (s) wadanda suke tsentseni da addininsu.

Wadannan malaman tarihi sun fitini mutane da mu’awiya, saboda rashin tsentseninsu wajen tantace hadisan karya da na gaskiya. Suka dawo suna daukaka makiya Allah da manzonsa (a), a matsayin masoya, sannan a duk lokacinda suka zo, ko suka ga hadisan da suke bayyana falalar Aliyu dan Abitalib (a) sai su yi sauri su karyata su, ko kuma hadisan da suke bayyana falalar iyalan gidan manzon Allah (s) su karyatasu ko su boyesu.

Maqdisi ya bayyana cewa wata rana yana cikin babban masallaci na garin Wasid sai ya ga wani mutum ya tara mutanen yana fada masu wani hadisi, daga manzon Allah (s) yana cewa, Lalle Allah zai kusanto da Mu’awiya a ranar kiyama, sai ya ajiye shi a gefensa, sai ya rufe shi da hannayensa, ya kuma gabatar da shi ga mutane kamar ango, sai Maqdisi yace masa, saboda me zai yi haka?

Sai mai ruwaito hadisin yace, saboda yakar Aliyu dan Abitalib(a) da yayi. Sai Maqdisi ya  ce masa: Karya kake, ya kai batacce.

Sai mai ruwaito hadisin ya umurci mutanen da suke tare da shi, da cewa: Ku kama  wannan ‘rafidi’ ko dan shia. Sai mutane suka ca a kansa, sai da wani wanda ya sanshi ya kubutar da shi bayan ya sha duka.

Wannan kamar yadda ya zo cikin littafin Al-bad’u Wattarikh SH 127.  A wani labarin Muqaddisi ya ruwaito yana cewa an so a kashe shi a lokacinda ya karyata wani hadisi wanda yake cewa “Ma’awiya manzon Allah ne.

A wani hadisin sun bayyana cewa, wai wani mutum yayi barci sai ya ga manzon Allah (s) yana zaune tare da Abubakar da Umar da Uthman da Mu’awiya. Sai wani mutum yazo, sai Umar ya kai kararsa wajen manzon Allah (s) yace: Ya manzon Allah(s) ‘wannan yana kaskantamu, sai mutumin ya ce (ya manzon Allah(s), bana kasksantashi, sai dai wannan ne yake kasksanta su, sai ya nuna Mu’awiya. sai manzon Allah (s) yace: ba sahabine bane? Ba sahabi na bane, ? har sau uku. Sai manzon Allah (s) ya dauki bulala ya bawa mu’awiya, sannan ya ce masa ka dake shi. Sai Mu’awiya ya yi masa bulala.

Sai mai ruwaito hadisin yace, sai da gari ya waye na je gidan wannan mutumin sai na ga cewa ya mutu saboda bulalanda da mu’awiya yayi masa a mafarki, kuma mutumin shi ne Rashidul Kindi. Wannan kamar yadda ya zo a cikin littafin al-bidaya wannihana na Ibn Kathir JZ 8 shafi na 140.

Malaman tarihi sun bayyana cewa, mutanen da basa da ilmi, ko kuma jahilai, tare da wadannan hadisan suna daukar Mu’awiya a matsayin mutumin Allah, mai kuma tsoronsa, waliyin Allah wanda ya taba shi yana iya fadawa karkashin fushin Allah.

Har’ila yau malaman tarihin sun bayyana cewa, wata rana Abdurrahama Annasa’i, wanda ya rubuta ‘Sunan Annisa’ei,  ya shiga birnin Damascus, sai malamai suka tambayeshi kan cewa ba zai rubuta littafi kan falalar Mu’awiya dan Abusufyan ba, ga shi ya rubuta littafi mai suna ‘Khasa’su Amirul Muminina Ali (A) ? sai ya ce: shi bai san mu’awiya ya na da wata falala ba, in banda manzon Allah (s) yace, (kada Allah ya kosar da cikinsa). Sai suka tattaka shi har suka kasheshi.

Sai dai dukkan wadannan al-amura suna faruwa ne a kasar sham ne, amma sauran yankuna ko kasashen musulmi, hatta a lokacinda yake da iko a kansu, amma bai isa ya sami iko a kan kwakwalen sahabban manzon Allah (s) ko kuma wadanda suka san hakikanin munanin abubuwan da Mu’awiya ya aikata ko kuma yake aikatawa a Sham ba.

Bai san cewa musulmi suna sanya masa ido ba, kuma suna shakkara musuluntarsa ba, sun kuma san mummunan ayyukan da ya aikata ba, musamman na yakar wasiyin manzon Allah (s) Aliyu dan Abitalib da kuma jikansa Imam Al-Hassan Al-mujtaba(a). Da kuma da haddasa rarraba tsakanin  musulmi da yayi. Tare da kissan bayin Allah nagartattu daga cikin sahabban manzon Allah (s) da yayi, wadanda suka hada da Hijir da Adi daga kabilar Kinda da kuma abokansa 5. Wadanda ya bukaci su la’ani Aliyu dan Abutalib (a) suka ki, sannan Ibn Ziyad ma’aikacinsa a Kufa ya turashi Damashq wajen Mu’awiya, sai da suka zo da su bayan birnin Damashq, sai ya bada umurnin a kashesu a can, idan sun ki la’antar ‘Abu Turab’ wato Aliyu dan Abutalib (a).

Kamar yadda aka sani, Hijir dan Adi Al-Kindi dai ya yi shahada ne a hannun jami’an tsaron Mu’awiya dan Abusufyan, bayanda suka umurcesu da su la’ani Aliyu dan Abitalib (a) amma suka ki amincewa.

Sahabban manzon Allah (s) da dama sun nuna fushinsu da rashin amincewa da siyasar Mu’awiya na kashe shi’ar iyalan gidan manzon Allah (s). Wani abin lura a nan shi ne, a sheklara ta 2013 da ta gabata a kasar Siriya, kungiyoyin wahabbiyawa masu kafirta musulmi, sun mamaye yankin da kabarin Hijir yake, a wata unguwa da ake kira ‘Azraa’ kusa da birnin Damaskus, suka tona kabarin suka fito da gawarsa, wacce ta kasance kamar yau aka bisneta, suka tafi da ita zuwa wani wuri ba wanda ya sani, wai don kada yan shi’a da sauran musulmi su ci gaba da bauta masa.

Sannan bayan da kwamitin kirkiran hadisan karya na Mu’waiya suka cika duniyar Musulmi da hadisan falalar Mu’awiya da Uthman, sai Mu’awiya ya bada umurni su dakatar da su haka, kada ya kai matsayin da hatta jahilai zasu gane shi.

Daga nan sai ya bada umurni su kirkiro hadisai na falolin shaihunai biyu, wato Abubakar da Umar. Shi ma ya rubutawa ma’aikatansa dakarda guda, ya aika masu. Inda a cikinta ya ce masu su dakatar da hadisai kan Uthman, sannan su duba su gani cikin falaloli na Aliyu dan Abitalib (a), kada su rage ko guda  face sun kirkiro wani hadisi wanda zai sanya fafalar ga wani sahabi. Ga nassin wasikar da ya rubutawa ma’aikatan nasa kamar haka.

(Lalle hadisai sun yawaita kan Uthman, ya kuma yadu cikin dukkan birane, da kuma dukkan yankuna, idan wannan wasika ta isa gareku, to ku kirasu zuwa kirkiran hasisan falalar Abubakar da Umar, don lallai falalarsu da matsayinsu ya fi soyuwa a gareni, kuma na fi jin dadinsa. Kuma zasu zama hujja a kan ‘iyalan gidan manzon Allah (s), sai kuma ya fi tsanani a garesu kan falalolin Uthman da aka kirkiro…).

Wasikar ta isa hannu ma’aikatansa suka karanta ta a gaban jama’a, sai masu kirkiro hadisai suka fara rige-rige wajen kirkiro falalolin Abubakar da Umar. Sannan Mu’awiya ya bada umurni a yada hadisan, a karantasu a kan mimbarorin musulmi a bawa malamai masu karantar da yara su karantar da yara hadisan, Su kuma haddacesu.

Ma’aikata da hatta mata a cikin gidajensu su haddace wadan nan hadisan.

Imam Bakir (a) limami na 5 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s) ya bijiro wa sahabinsa Aban dan Taglab, wasu daga cikin kirkirarrun hadisan, inda ya kawo su kamar haka.

(Shugaban tsoffin yan Al-janna Abubakar da Umar. Mala’iku suna magana da Umar, Lalle mala’iku suna lakkanawa Umar magana, Lalle sakina tana magana ta kan harshen Umar, Lalle mala’iku suna kunyar Uthman da sauransu.

Hadisi na farko wanda Imam (a) ya kawo, sun kirkiroshi ne, don mukabala da sharerren hidisin da manzon Allah (s) yake fada dangane da Al-Hassan da Hussain (s), inda yake cewa {Al-Hassan da Al-Hussan shuwagabannin samarin al-jannane.}

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted