Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155

155-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka

155-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa an yiwa Imam Hassan bai’a a matsayin Khalifan musulmi a kufa, sannan ya kira taron mashawartansa suka zauna suka kuma fidda wassu al-amura guda biyu don fuskantar Imam Al-Hassan(a). Kuma sune, aika jasusu mai aiko masu labarai sirri daga kasar Iraki, musamman a biranen Kufa da Basra wadanda suka kasance manya-manyan garuruwan a lokacin a kasar Iraki.

Sannan na biyu kuma suna son sayan wasu manya-manyan shugabannin Iraki wadanda suke taimakawa Imam Alhassan (a) don su barshi shikadai, hakan zai tilasta masa ya mika kai ga mu’awiya dan Abusufyan.

Sannan ba tare da bata lokaci ba suka aika mutanen biyu zuwa kasar Iraki, daya a Basra da kuma a Kufa babban birnin daular musulunci karkashin Imam Hassan (a).

A lokacin da wadan nan ma’aikata biyu suka je inda aka turasu suka fara ayyukansu na leken asiri, sai asirinsu ya tonu, Imam Hassan (a) ya tura shurdatul Khamis suka bazu a cikin kufa har sai da suka zakulo jasusun Ma’awiya a cikin birnin suka kawoshi a gaban Imam Alhassan (a) wanda ya bada Umurni a kashe sai aka kashe shi.

Haka ya faru a Basra ma, inda Abdullahi dan Abbas ®   ya sa aka nemo shi aka kuma kama shi aka kawo shi a gabansa ya bada umurni aka kasheshi.

Daga sai Imam Hasan (a) ya rubutawa Mu’awiya wasika, inda a ciki ya aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin kufa da Basar, sannan yayi masa  barazana da yaki. Sannan ya fada masa cewa ya ji labarin ya nuna jin dadi da shahadar mahaifinsa Imam Ali (a).

Mu’awiya ya tsorata ya kuma mayar masa da amsa kan cewa bai ji dadin kasan mahaifinsa ba, amma yaki ya yi magana kan dan leken asirin da ya aika. Haka ma Ibnu Abbas ya rubutawa Mu’awiya wasika yana aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin mutanen Basra. Shi ma mu’awiya ya mayar masa da amsa inda ya  bayyana masa cewa Imam Alhassan (a) ya rubuta masa wasika irin tasa, yana aibata shi. Amma bai bayyanawa Ibn Abba kan cewa Imam Al-Hassan (a) yayi masa barazana da yaki.

Bayan haka sai Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan wasika inda a cikin yake bashi shawara yake kuma kodaitar da shi kan yakar Mu’awiya da kuma wasu dabarbaru da ya bashi. Ga nassin wasikar kamar yadda take.

:Bayan haka, Lalle musulmi sun mayar maka shugabancinsu bayan Aliyu (a), to zage dantse don yaki, ka yi jihadi da makiyinka, ka kusanto da mutanenka, wadanda suke da raunin Imani ka sayi addininsu don kare kanka daga cutar da kai. Ka kuma dora mutane daga manya-manyan gidaje da daukaka don sai danginsu su bika sannan kan jama’a ta hadu, …..

Ka yi koyi da abinda abinda ya zo daga wajen shuwagabanni adilai, suna cewa karya bata halatta sai a yaki… kuma ka san cewa abinda ya sa mutane suka kauracewa mahaifinka suka koma wajen Mu’awiya shi ne shi mai son daidaita rabo a tsakanin, sai wannan yayi masu nauyi.

Kuma ka san cewa kana yakar wanda ya yaki All..da manzonsa(a) a farkonmusulunci ne, har sai da al-amarin All..ya bayyana ya kuma sami rinjaye. A lokacinda aka kadaita Allah aka shafe shirka addini ya daukaka, sai suka bayyana cewa su masu Imani ne a gaban mutane, suka karanta Alkur’ani suna masu istahza’I da ayoyinsa, suka tsaida sallah suna cikin kasala, suna aikata sauran farilli ala tilas.    

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments