Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 200

200-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

200-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah(s) da muke kawo maku, mun tsaya inda sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abusufyan, ya yiwa wasu daga cikin Mabiya iyalan gidan manzon Allah (s) zafi, har sai da ya kai suka fita cikin hayyacinsu. Wasunsu suka kai ga matsayin sun farta wasu mummunan kalmomin wadanda basu dace a fadawa Imam Al-Hassan (a).

Mun bayyana cewa daya daga cikin wadanda sulhun ya rikita ya kuma yi masu zafi akwai babban kwamandan sojojin Imam Al-Hassan (a) wanda ake kira Kais dan Sa’adu dan Ubada Alansari, wanda a lokacinda labari ya riskeci kan cewa Imam Al-Hassan (a) ya sulhunta da Mu’awiya kuma ya mika masa shugabancin Al-Ummar musulmi, sai ya face da kuka. Yayi kuka mai yawa, yana cewa, ta yaya shugaban adalci za iyi sulhu da shugaban zalunci Mu’awiya dan Abusufya.\

Kais ya san cewa Mu’awiya dan Abusufyan bai ma musulunta ba, da shi da babansa sun dai mika wuya, amma Imani bai shiga zuciyarsu ba. Saboda haka ne, manzon Allah (S) ya sanya babban Mu’awiya cikin mu’allafatu kulubuhum wadanda ake basu bangare na zakka don kodaitar da su su zama muminai.

A fatahin Makka, an kama babban mu’awiya dan Abusufyan, aka kawoshi gaban manzon Allah(s) sai yace masa , lokaci bai yi ba ya Abusufyan ka Sahida babu abin bauta da gaskiya sai Allah, sai yace shi bai yarda da ba, sai aka ce masa idan baka yarda ba za’a kaste wuyarka, sai yace to ya yarda tunda ka sami iko a kammu. Kaga wannan ya nuna cewa, bai yi iamani ba sai da yaga cewa za’a kashe shi, sai manzon Allah(s) ya sake ce masa, lokaci bai yi ba ya abusfyan ka shaida ni manzon Allah ne, ? sai yace wannan kam akwai wanai abu a cikin zuciya ta, sai aka ce masa idan baka shaida shi manzon Allah ne ba sai an katse wuyarka. Sai yace na yarda.

A yakin Bandar an kashe mahaifin Hindu matar Abusufyan, Ubtaba, da amminta Shaiba, dan uwanta walid.

Don haka wannan ya sanya suna kiyayya da manzon Allah (s) har abada da. Ko da suka musulunta. Don haka a cikin shekaru biyu da suka yi tare da manzon Allah (s) a makka basu sauya ba, kuma manzon Allah (s) ya san cewa suna neman wata dama ta wargaza addinin musulunci ne.

A baya mun kawo jawabin Mu’awiya na farko a masallacin kufa, inda ya fadawa mutanen Kufa kan cewa bai yakesu ba, don su yi sallah, ko azumi, ko zakka ko hajji, ya yakesu ne don ya sami iko a kansu kuma Allah ya bashi ko da bakaso.

Sannan wannan ya tona asirinsa kan dalilan da yayi ta yayatawa kan cewa Aliyu(a) ya kashe Khalifa na 3 ko kuma ya kare wadanda suka kashe shi. Ba gaskiya bane, yayi amfani da kissan Khalifa na uku don ya sami goyon bayan jahilai daga cikin musulmi, musamman mutanen sham don ya yaki gaskiya. Ya yaki Aliyu dan Abitalib (a). da kuma dansa bayan shahadarsa. Amma a lokacinda ya sami nasara a kansu sai ya bayyanawa mutanen kufa gaskiyan abinda yasa ya yake su tunda sune suka taimakawa Aliyu da kuma Imam Al-Hassan (a) don yakarsa. Kan cewa yayakesu ne don ya sami shugabanci a kansu kuma ya samu ko da basa so.

Don haka daga cikin yan shia masu goyon bayan Imam Al-hassan (a) akwai Kais dan Sa’adu dan Ubada. Wanda kuma muka ce bai ji dadin sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abusufyan. Don hala a lokacinda labari ya zo masa kan cewa Imam Alhassan (a) yayi sulhu da Mu’awiya ya face da kuka yana cewa ta yaya limamin gaskiya zai bi limamin karya…

Sai juya wajen sojojin da suke karkashinsa yana fada masu cewa: Kuna da zabi biyu ko ku yi yaki ba tare da limami ba, ko kuma ku yi bai’a ta bata. Sai suka ce masa said ai mu yi yaki babu limami amma ba zamu yiwa batacce bai’a ba.

Daga nan sai ya jagorancesu suka farwa sojoji sham, wato sojojin mu’awiya da suke kusa da su, har saida suka koresu daga inda suke. Amma wannan ya tada hankalin Mu’awiya dan Abubu sufyan, wanda ya rubutawa Kais dan Sa’ad ya gargadinsa kan cewa idan bai bari ba zai kasheshi.

Amma Kais ya mayar masa wasika inda yake ce masa shi gunki ne dan gunki, da wasu magangannu na zagin Mu’awiya. Sai Mu’awiya yayi fushi yana sun ya mayar msa da martani a rubuce, sai Amru dan Asi ya hana shi, ya ce masa, idan ka mayar masa zai sake fadan wanda ya fi wannan wasikar Muni. Sai Mu’awiya ya amince, amma ya sake aika masa wata wasika yana ce masa: kai don wa kake yaki, wanda kake yaki don shi (wato Imam Al-Hassan (a)) yayi mani bai’a , ta yaya zaka halaka kanka a kan abinda ba naka ba?).

Kuma gaskiya ne Mu’awiya ya fada masa, don idan da ace Kais ya sami nasar kan Mu’awiya ba zai iya zama shugaba ba, tunda sun saba a lokacin shuwagabanni ko khalifofi gaba daya kuraishawa ne, shi kuma kais ba-ansare ne.

Daga sai kai ya yi shiru y afara tunani, don, na farko ya san cewa da shi da sojojinsa gaba daya basu isa su sami nasara a kan sojojin sham gaba daya ba. Daga karshe yana cikin wannan halin sai an kawo masa wani sako daga wajen Mu’awiya.

Wata farar takarda ce, wacce Mu’awiya ya aika masa kan cewa ya rubuta duk abinda yake so zai bashi. Kais ya san cewa idan ya je gaban Mu’awiya a lokacin ba tare da ya sami tabbacin amincinsa ba, mu’awiya yana iya cewa a kashe shi. Don haka sai ya karbi takardar ya kuma rubuta bukatu biyu, sune amincin kansa da na sojojin Imam Al-Hassan da suke karkashinsa. Sai ya sa aka mayarwa Mu’awiya takardan.

A sannan sai ya kama hanya, zuwa cikin masallacin kufa inda ake taro tsakanin Imam Al-Hassan (a) da kuma mu’awiya dan Abisufyan, yana tafiya kansa a sunkuye saboda kaskanci da kuma bakinciki da yake cika. A lokacinda ya shiga wajen Mu’awiya, ya ga mutane suna kewaye da shi. Sai ya daga kansa, yana masu Magana, a cikin maganarsa, yana cewa ya ku mutane, kun zabi kafirci a kan Imani, kun zauna karkashin shugabancin Amirul muminina Aliyu dan Abitalib(a) shugaban musulmi dan ammin manzon Allah (s), amma ku dawo ku zabi bata a kan gaikiya , ko dai Allah ya dode zukatanku ne, ko kuma baku hankali. Sai ya juya yad ubi Imam Al-Hassan (a) yace masa. Ka halatta mani bai’arka ? (ya dan manzon Allah (s)) sai yace masa Ee.

Sai ya zauna, sai mu’awiya yace masa zaka yi bai’a ne ya kais sai yace masa ee. Sai kais yad aga hannayensa ya azasu a kan cinyoyinsa. Sai Mu’awiya ya tashi da kansa ya zo ya aza hannunsa a kan hannu kai yayi masa bai’a. Da haka aka rufe wannan Magana ta Kais dan sa’adu dan Ubada.

Amma Imam Al-Hassan (a) ya cutu da wasu daga cikin shiarsa wadanda suka kasa fahintar dalilan da yake basu na sulhuntawa da Mu’awiya dan Abusufyan.

Daga cikinsu mun fara kawo maku Hijru dan Adiy wanda ya je madina wani Imam Al-Hassan (a) bayan ya mikawa mu\awiya shugancin al-ummar musulmi. Ya shiga wajensa yana fada masa, a cikin bakin ciki da kuma karayar zuciya: Yana cewa, wallahi na so ace ka mutu kuma muma mun mutu tare da kai kafin mu ga wannan ranar (wato ranar da yayi sulhu da Mu’awiya). ..har zuwa karshen maganarsa.

Sai Imam Alhassan (a) ya kama hannunsa, ya je da shi wata zawiya ko luggu a cikin gidan yana fada masa dalilan da suka say a sulhunta da Mu’awiya.

Kafin mu ci gaba, kun san cewa wadan nan kalaman Hijr dan Adiy, wa Imam Al-Hassan (a) a matsayinsa na Ma’sumi, har kuma yana masa fatan mutuwa, bai dace ba. Amma Imam Al-Hassan (a) ya san irin yadda matakin da ya dauka ya yi mummunan tasiri a kan mabiyansa, don haka yayi ta hakuri da su. Sannan ya yi kokarin fahintar da su ta hanyoyi daban-daban kamar yadda zamu gani.

Don haka Imam Al-Hassan (a) yak ama hannun Hijr dan Adiy ya ja shi gefe yana masa bayani dangane da abinda ya say a sulhunta da Mu’awiya dan Abusufyan. Yace masa

{Ya Adiy! Lalle ni naga karkatan mafi yawan mutane zuwa ga sulhu basa son yaki, ni kuma bana son in dora masu abinda basa so, don haka na sulhunta don ina son kada a kashe shiarmu, kuma ina son jinkirta wannan yakin zuwa wani lokaci, lalle shi Allah yana cikin sha’aninsa a ko wace rana }

Don haka Imam ya fada masa yadda sojojinsa suka kosa da yaki, da kuma yadda suke son zaman lafiya, kuma yana son ya sake tada wani yaki a dai dai lokacinda ya san zai sami nasara a kan mu’awiya nan gaba, idan yaga hakan ya dace.

Kuma wanda yake tare da mu ya san haka, saboda khudubokin da shi Imam (a) ya yi a mada’in inda ya fada masu, cewa {Mu’awiya ya aiko mani da wata bukata wacce babu daukaka a cikinsa -idan zaku tuna-idan shirya mutuwa mu kai karansa ga Allah, idan kuma baku shirya mutuwa ba, in amince,} sai suka ce aminci aminci. Wanda ya nuna cewa basa son yaki.

Amma bayan wannan bayanin da Imam(a) yayiwa Adiy bai gamsu ba. Don haka sai ya wuce zuwa kanin Imam Al-Hassan (a) wato Imam Al-Hussain(a), zuciyarsa tana zafi da kuma hamasar a koma yaki da Mu’awiya ko da kuwa zai mutu ne.

Ya shiga wajen Imam Al-Hussain (a) yace masa {Ya baban Abdullah! Kun sayi kaskanci da daukaka, kun karbi kadan kun kuma bar da yawa, mun yi biyayya a yau, amma mun yi sabo na tsawon zamani, ka bar Hassan da ra’ayinsa na sulhuntawa, ka tara shi’arka daga cikin mutanen kufa, da wasu wurare, ka kuma shugabantar da ni da aboki na, runduna ta farko, dan hindu (Mu’awiya) ba zai sani ba, sai kawai ya gammu da takubba muna yakarsa}

Sai Imam Al-Hussain (a) yace masa {Hakka mun rika mun yi bai’a, mun kuma yi alkawari, kuma babu wata hanya ta kwance bai’ar da muka yi} . da wannan maganar Adiy ya san cewa babu kuma wata hanya ta komawa yaki. Sannan idan kun lura da kalaman Imam Hussain (a) baya daukar sulhun da Imam Al-Hassan (a) ya yi, ra’ayinsa ne shi kadai ba, said ai dukkan iyalan gidan manzon Allah (s) suna kansa. Yana cewa ;mun yi bai’a’ babu hanyar kwance bai’ar mu”. Duk abinda Imam Al-Hassan (a) yayi a madadinsu ne, basa saba masa. Wannan Hijir dan Adiy kenan.

2-Al-Musayyid dan Najbah, wanda ya kasance fitacce daga cikin muminai Mabiya iyalan gidan manzon Allah (s), wanda kuma ya san hakkinsu, mutumin Kufa, Ya ruwaito hadisai daga Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) hakama ya ruwaito hadisai daga Khuzaifa dan yaman( r). Ya je yakin Kadisiyya a zamanin Khalifa na biyu,  Musayyib ya shaidi dukkan yake-yaken Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) a Jamal da Siffin da kuma nahrawan. Daga karshe ya fita tare da Sulaiman dan Sarda a shekara ta 65 suna masu neman fansar jinin Imam Hussain (a) ya kuma yi shahada a yakin Ainul warda a kasar Sham.

Musayyid ya tasirantu da sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abu sufyan, ya zo gaban Imam Al-Hassan (a) yana cewa masa.

{mamakina da kai baya karewa! Ka yiwa Mu’awiya bai’a kana da mayaka dubu 40,000 ? kuma baka samawwa kan aminci da alkawali a bayyane ba? Ya baka wani al-amari tsakaninsa da shi kadai. Sannan yace: Wallah ban taba ganin wanda ya amince da irin wannan ba sai kai} sai Imam Al-Hassan (a) yace masa menen ra’ayinka? Sai yace: Ra’ayi na shi ne, ka warware abinda yake tsakaninka da shi, don shi ma ya rika ya sabawa al-kawalin da yayi maka.

Sai Imam Al-Hassan (a) ya tashi ya zauna don ya bayyana masa manufar sulhuntawa da mu’wiya, yace

{Ya Musayyib! Da ina bukatar duniya da abinda na aikata, mu,awiya bai fini hakuri da kuma juriya a yaki ba, sai dai ni ina bukatar masalaharku ne, da hana yaki a tsakaninku, }.

A nan Imam (a) ya nuna masa cewa idan da duniya yake so to fa mu’awiya bai fi shi hakuri da dauriya a yaki ba, amma shi ba zai yi abinda mu’awiya yake yin a yaudara, da kha’inci da kuma wasu hanyoyin da musulunci bai amince da sub a dan kaiwa ga shugabanci da sarauta ba. Don haka yana kan hanyar mahaifinsa na bin gaskiya da adalci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted