Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 199

199-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

199-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barakammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah(s) da muke kawo maku, mun isa inda Imam Alhassan (a) ya hadu da Mu’awiya dan Abusufyan, a masallacin kufa a karon farko inda a nan ne Imam Al-Hassan (a) ya mika masa shugabancin al-ummar musulmi a hukumance.

Da farko mun bayyana cewa Mu’awiya dan Abusufyan ne y afara hawa mimbari ya yi mummunan khuduba wacce ba’a taba khuduba mafi muni a tarihin addinin musulunci irinta ba.

Inda a cikinta Mu’awiya dan Abusufyan ya bayyana cewa, dukkan al-kawulan da yayiwa Imam Al-Hassan (a) saboda sunhuntawa da shi suna karkashin kafansa kuma ba zai cika ko da daya daga cikinsu ba. Ya kuma fadawa mutanen kufa kan cewa bai yakesu ba, saboda su yi sallah, ko su yi azumu ko su fidda zakka ko su je aikin hajji ba, suna hakan, amma babban dalilin da ya say a yakesu ne shi don ya sami iko a kansu kuma Allah ya bashi ko da kuma mutanen kufa basa sa.

A nan mu’awiya ya nuna cewa babu ruwansa da addinin musulunci kwata-kwata, kuma yakar Imam Ali (a) da yayi da kuma Imam Al-hassan dansa daga, baya ba saboda kissan Khalifa Uthman bane, sai dai yayi amfani da kissan Khalifa Uthman ne don ya yaudari musulmi su goya masa baya, ya yaki gaskiya, ya yaki shuwagabannin shiriya daga cikin iyalan gidan manzon Allah (s).

Sannan bayan haka Mu;awiya ya kira Imam Al-Hassan(a) ya haw kan mimbari ya kuma bayyana cewa ya mayar masa da iko ko kuma shugabancin al-ummar musulmi.

Imam Al-hassan (a) ya hau kan mimbari ya kuma yi khuduba mai kyau, inda a cikinta y afara da yabon Allah da gode masa, da kuma salati ga kakansa manzon Allah (s) da kuma iyalan gidansa. Sannan tabo muhimman al-amura wadanda suka hada da khalifancin manzon Allah, (s). inda ya ce, Mu’awiya ya yada cewa shi yafi cancanta da Khalifanci, don shi bai iya shugabanci ba, sai yace yayi karya, saboda su iyalan gidan manzon Allah (s) shugabancinsu ya zo a cikin al-kur’ani mai girma, sannan manzon Allah (s) ya bayyana hakan, a ranar Ghadir, ya kuma umurcim wanda ya halarci Ghadir ya isarwa wadanda basu ji ba. Yace amma al-ummar musulmi sun kaurace masu, yace da ta yiwa babansa Aliyu dan Abitalib (a) bai’a a ranar wafatin manzon Allah (s) da sunci ta sama da kasa, da sama ta bada digonta, sannan kasa kuma ta fidda al-barkatunta.

Yace da al-ummar musulmi sun yiwa mahaifinsa bai bayan wafatin manzon Allah(s) da kuraishawa, da kuma tulakaa da Yayan tulakaa basu yi kodayin samun khalifanci ba. Ya jiya wajen mu’awiya dan Abusufyan yana cewa: Ya kai wanda yake ambaton Ali (s) nani Alhassan dan Ali (a) kakana manzon Allah (s) mahaifiya ta Fatimah, kakata Khadija.  Kai kuma babanka Sahar, mahaifiyarka hindu, kakanka harb , da katilah Allah ya la’anci mafi boyuwar Ambato daga cimmu mu, sai mutane suka ce Amin, mu ma mun ce Ameen.

A nan ne muka bayyana cewa a lokacinda ya tabbatar da cewa ya mikawa mu’awiya shugabancin al-ummar musulmi, ya kuma yi kira ga mabinysa musamman mutanen kufa su yi masa biyayya su zauna lafiya da wanda ya zauna lafiya, su kuma yarda da mu’awiya. Don shi ne masalaha ga al-ummar musulmi duniya da lahira. Amma Kais dan Sa’ad dan Ubada, Al-ansari , kuma shugaban rundunar Imam Al-Hassan wannan al-amarin yayi masa nauyiz, sai ya fashe da kuka yana cewa ta yaya limamin adalci zai mika kai yayi bai’a wa limamin bata.

Kais ya jiya ga sojojinsa yana fada masu cewa, kuna da zabi biyu, ko ku yi yaki ba tare da shugaba ba, ko kuma kuyi bai’ar bata. Sai suka zabi yaki ba tare da shugaba ba, a nan sai suka farwa sojojin sham da yaki har sai da suka kauda su daga inda suke.

Hankalin mu’awiya ya tashi, ya Aikawa Kais wasika ta farko yana gargadi da barazana ga kaisa, amma kai ya mayar masa da da wata wasika mai zafi, amma Amru dan Asi ya hana Mu’awiya sake maida masa amsa. Mu’awiya ya amince amma ya Aikawa kai kai cewa don wa yake yakin? Saboda wanda yake yaki don shi yayi masa bai’a me yasa zai kashe kansa kan abinda ba nashi ba, ….?. A nan ne sai Kais ya shi tunani kan abinda za iyi. Daga karshe dai Mu’awiya ya aika masa farar takarda ya rubuta abinda yaga dama zai bashi. Sai kai ya bukaci aminci da kuma amincin sojojinsa. Bai nemi wani abu bayan haka ba.

Amma kais dan Sa’adu baya son ya hadu da mu’awiya, saboda ya yi bakance ba zai hadu da shi ba sai in akwai mashi da takobi a tsakaninsu. A lokacinda labari ya kai wa mu’awiya sai ya bada umurni a kawo masa mashi da takobi don ya bawa Kais dama kada ya karya alkawalinsa ko bakancensa. Sai aka Aikawa kais dan sa’ad ya zo.

Kais yak ama hanya zuwa wajen taron Mu’awiya da Imam Al-Hassan, (a) yana mai sunkuyar da kansa, A kaskance, duk jikinsa yayi sanyi. Ba ya Kallon mutane, har yazo ya shiga cikin mutane, har ya zo gaban Mu’awiya, sannan yad aga kansa ya dubi mutane yana cewa

(Ya ko mutane! Hakika kun zami sharri a kan Alkhairi, kun sauya maye gurbin daukaka da kaskanci, da kuma kafirci da Imani, sai gashi kun dawo, bayan shugabancin Amirul muminina kuma shugaban musulmi , kuma dan ammin manzon Allah ubangijin talikai kun dawo kuna bin yentaccen bawan manzon Allah (s) dan yantaccen bawansa. Wanda zai dandana maku zalunci, zai shugabanceku da takobi, ta yaya kuka jahilci wannan?  Ko dai Allah ya toshe zukatanku ne, kun zama wadanda basa hankalat? ).

Daga nan sai Kais ya juya zuwa ga Imam Alhassan (a) yana cewa: yana cewa: Ka dauke mani bai’arka (ya dan manzon Allah(s)) sai Imam ya amsa masa, ee na halatta maka bai’a ta.

Sai Mu’awiya ya juya wajen kais y ace masa zaka yi bai’a ne yak ais sai ya amsa : ee. Sai ya sunkuyar da kansa saboda jin kaskanci, yad aga hannayensa ya sanyasu a kan cinyoyinsa, sai mu’awiya ya tashi da kansa yaje ya sanya hannunsa a kan hannun Kais don amsa bai’arsa. Wannan taron yayi zafi sosai ga Imam Al-Hassan (a) haka ma ga manya-manyan mabiyansa kamar shi kais dan Sa’adu dan Ubada.

Daga nan Imam ya fita daga masallaci ya koma gidansa ya kuma fara shirye-shiryen komawa Madina.

Da haka kuma Imam Al-Hassan ya bar kasar Iraqi, ya bar birnin Kufa wanda mutanensa, basu cika al-kawalin da suka yi masa da shi da mahaifinsa(a) ba. Sun bar kufa da kuma kasar Iraqi ga Mu’awiya dan Abu sufyan su yi abinda suka ga dama a cikinsa.

Sannan su kuma mutanen kasar Iraki ba zasu taba manda da yadda Imam Ali (a) ya zo ya gyara garinsu ya samar da aminci da wadata a cikinsa ba. Ya maida garinsu cibiyar Khalifancin Al-ummar Musulmi. Sai ga shi a yau garin da kuma kasar Iraqi ta koma hannu mafi munin shuwagabanni a cikin al-ummar musulmi, wanda ya kauda dukkan amincwin da kasar ta samu a baya. Ya maida kasar Iraki musamman biranen Kufa da basra a matsayin wurare mafi muni ga musulmi Mabiya Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) da yayansa. Sannan suna nadama, mafin tsananin nadama kan rashin amsa kiran Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) na su fito su yaki Mu’awiya dan Abusufyan kafin lokaci ya kure masu. Amma nadamar ta zo a lokacin da ba zata yi amfani ba.

Sai dai musiba da kuma bala’I mafi girma su ne wadanda Imam Al-Hassan (a) da kansa ya fuskanta daga kuma shi’arsa masoyansa wadanda suka kasa fahintar irin hikimar da ke cikin sulhun da yayi da Mu’awiya dan Abu sufyan. Hakama wasu makiyansa sun zo suna masa isgila a kan sulhun da yayi da Mu’awiya dan Abusufyan suna ganin ya yaudare shi.

Don haka a cikin wannan halin Imam (a) ya koma madina sannan yana karban daya bayan daya daga cikin wadan nan mabiyansa wadanda suka rikici a cikin matakin da ya dauka.

Wasu daga cikin wadan nan masoya da kuma makiya sun yi amfani da kalmomi masu tsanani a kan Imam (A) wanda bai kamata ga masoyi ya fadeshi ga limaminsa ma’asumi ba. Kalma mafi muni wanda yasunsu suka yi amfani a kan Imam Al-Hassan(a) wanda kuma suka cutar da shi da it ace “Ya kai mai kaskantar da muminai! Kamar yadda zamu gani a kalaman wasu daga cikinsu.

Wadan nan kalmomi sun cutar da Imam Al-Hassan (a) fiye da sulhun da ya yi da Mu’awiyan kanta, saboda sun fito ne daga masoyansa, wadanda suke riya cewa sun san matsayinsa sun kuma yarda da shugabancinsa.

Daya daga cikinsu shi ne Hijr dan Adiy, wanda ya iso gaban Imam Al-Hassan (a) cikin bakin ciki, kuma jikinsa a mace, wanda kuma labarin sulhun ya bugi zuciyarsa matukar doka, sai ya yi sallama ya zauna sai ya fara magana ga Imam (a) yana cewa: (Wallahi da na so ace ka mutu mun kuma mutu tare da kai bamu ga wannan ranar ba, ga shi mun dawo ba tare da abinda muke so ba, sannan sun koma suna masu farin ciki da abinda suke so).

Bamu san yadda Hijru dan Adiy ya iya furta wannan Kalmar ta fatan mutuwar Imam (a) da kuma kansa ba, duk da cewa ya san matsayin Imam Alhassan (a) na cewa baya aikata abinda Allah baya so. Kuma Allah yana tare da shi a cikin duk al-amuran da yake yi. A cikin shirimmu nag aba zamu ga jawabin Imam (a) a gare shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted