Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 198

198-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

198-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko cikin wasu laittafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddeen Rumi, ko kuma cikin wasu laittafan. Da fatanmasu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.

///… Madallah, idan masu sauraro suna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, yi maganar haduwar Imam Al-Hassan a karon farko a wani wuri da ake kira Nakhala a wajen birnin Kufa. Wasu kuma suka ce a cikin masallacin birnin Kufa. Magana mafi inganci ita ce sun hadune a masallacin Kufa. Inda a cikinsa ne Imam Al-Hassan ya mika masa shugabancin al-ummar Musulmi.

Da farko mun bayyana cewa, mu’awiya dan Abusufyan ne ya fara hawa mimbari ya kuma gabatar da khuduba, wanda muka kira mafi munin khuduba a tarihin addinin musulunci wanda wani shugaba a taba gabatarwa.

A cikin khudubarsa ta farko Mu’awiya bayyana bayyanawa mutane kan cewa dukkan alkawulan da ya cimma da Imam Al-Hassan (a) ba zai cika ko da daya daga cikinsu ba. Ya kuma juya wajen mutanen kufa yana fada masu cewa, ya yakesu ne ba don su yi sallah, ko suyi azimi ko su yi zakka ko su yi hajji ba, duk suna yi, amma babbar abinda yasa ya yakesu shi ne samun iko a kansu kuma Allah ya bashi hakan ko da kuwa basa so.

Da wannan Mu’awiya ya nuna cewa babu ruwansa da addinin musulunci, kuma neman jinin Khalifa Uthman ba shi yasa ya yaki Imam Ali(a) da kuma Imam Al-Hassan daga bayansa ba. Yana neman iko ya kuma samu, ko da mutanen kufa wadanda suka goyi bayan Imam Ali (a) da kuma Imam Al-Hassan daga bayansa basa so.

Wannan kuma ya tabbatar mana abinda Mu’awiya ya aikata a lokacin shugabancinsa. Inda ya bakanta tarihin addinin musulunci, ya kuma aikata laifuka wadanda Allah zai kama shi da su.

Bayan haka Imam Al-Hassan ya haw kan mimbarin mahaifinsa a Kufa, tare da Bukatar Mu’awiya don ya bayyanawa mutane kan cewa ya mika masa shugabancin al-ummar Musulmi. A lokacinda Imam Al-Hassan (a) ya haw kan mimbari ya yi khudu mai kyau, ya kuma fara da godiyar Allah da kuma salati ga manzon Allah (s) da kuma iyalan gidansa.

Sannan yayi magana ga mutanen kufa yana fada masu kan cewa, tun farko da suka yi masa bai’a bayan shahadar mahaifinsa, sun yi masa ne, bisa kan cewa zasu zauna lafiya da wanda ya zauna lafiya da shi kuma zasu yaki wanda ya yaki. Ya tunatar masu da wannan sannan ya fadawa masu cewa, shi yana da masaniya kan abinda basu sani ba, don haka kada su saba masa kan abinda ya umurcesu, don ya san abinda basu sani ba, ya fi su sabin abinda ya kasance masalaha garesu fiye da kawukansu.

Ya ce: Mu’awiya yayi jayayya da shi kan Khalifanci, ya bayyana bayyanawa mutane shi yafi cancanta da shugabanci a kan sa, amma yayi karya, saboda su iyalan gidan manzon Allah a littafin Allah ne Allah ya tabbatar da shugabancinsu. Sannan manzon Allah a aikace ya  bayyana wannan matsayin na su.

Imam y ace, bai dauki wannan matakin ba, sai da ya ga cewa shi ne maslaha ga ga al-ummar musulmi. Sannan yace na zabi sulhuntawa da zaman lafiya da Mu’awiya.

Sannan ya fara magana kan cewa iyalan gidan manzon Allah basu gushe ba suna a matsayin wadanda aka zalunta tun bayan wafatin kakansu manzon Allah(s). Ya ce bayan an kwace hakkinsu na kwalifanci a bayansa, sannan ya tsaya inda yake fada kan cewa da musulmi sun yiwa mahaifinsa bai’a bayan wafatin manzon Allah (a) da sun ci daga sama kasa, da sama ta bada digonta kasa kuma ta fito da al-barkatunta.

Da kuma kuraishawa basu ji jayayya a kanta ba, da kuma tulakaa da yayan tulakaa basu yi kudayinta ba.

Mun tsaya inda ya kawo hadisin manzon Allah (s) wanda yake cewa: Ba wata al-umma wacce zata shugabantar da wani mutum a cikinta, sannan akwai wanda ya fi shi ilmi face al-amarinsu yayi ta komawa baya, har sai sun dawo kan inda suka fara.

Ya ci  gaba da cewa: {Hakika banu Isra’ila sun bar annabi Haruna (suka bi samiri) al-hali sun san cewa shi ne khalifan annabi Musa, a cikinsu, suka bi samiri, al-ummar nan ta bar mahaifina suka bada bai’a ga waninsa, al-hali sun ji manzon Allah (s) yana cewa : Matsayinka da ni kamar matsayin Haruna da Musa, sai annabci. Hakika sun ga manzon Allah (s) ya nada mahaifi na a ranar Ghadir, ya kuma umurcesu da wanda ya halarci taron nadin ya isarwa wanda baya nan.

Yace manzon Allah (s) ya gudu daga mutanensa a lokacinda yake kiransu zuwa ga Allah, ya shiga kogo, da ya sami mataimaka da bai gudu ba. Haka ma mahaifi na ya kame hannunsa daga barin yakar wadanda suka kwace hakkinsa, a lokacinda yake hadasu da Allah su mayar masa hakkinsa. Kuma ya nemi taimako ba wanda ya taimaka masa,

Allah ya bawa Haruna yalwa a lokacinda suka kaskantata sun kuma su kashe shi, Allah ya sanya annabi (s) a cikin yalwa a lokacinda ya shiga kogo, bai samu mataiamaka ba, haka al-amarin yake ga mahaifina, da kuma ni, Allah ya yelwatamana, a lokacinda wannan al-ummar ta kyale mu, abin sani wannan sunnace da kuma misalai wadanda sashensu na bin sase, }.

 A wani wurin yana cewa {To na rantse da wanda ya aiko Mohammadu (s) da gaskiya, ba wanda zai tauye hakkimmu Ahlul bait, sai Allah ya rage masa a cikin ayyukansa, ba wata daula wacce zata cutar da mu face an sanya mana daula ta karshe. (Lalle zaku san labarinsa ko da bayan wani lokaci ne} S 88.

Sannan a wani wurin yana cewa {Ya kai mai ambaton Aliyu (a) nine Hassan kuma mahaifi na Ali(a), kuma kai ne Mu’awiya mahaifinka Sakhar, mahaifiyata Fatima mahaifiyarka Hindu, kakana manzon Allah (s) kakanka Harb, kakata Khadija kakarka Katilatu, Allah ya la’anci wanda ke da boyayyen Ambato, da mafi sharrin nasaba, da mafi dadewa a kafirci da munafurci}. Daga nan sai aka ji sautin mutane na ta tashi suna cewa Ameen, ameen, ameen. Kuma duk wanda ya ji wannan khudubar yace Ameen, muma mun ce Ameen, Ameen.

Wannan khudubar tana daga cikin khudubobi mafi cika da Balagha, kuma Imam Al-Hassan(a), ya kawo al-amura wadanda suka kai inda ake, wadanda suka shafeshi suka kuma shafi mahaifinsa. Idan ba don wanda ko wadanda suka sanya rigar khalifanci, bayan wafatin manzon Allah (s) suka kwacewa mahaifinsa hakkinsa ba, da mutane iran su Mu’awiya basu yi kwadayin samunta ba.

Bayan wannan khudubar ya sauka daga mimbari, ya koma ya zauna. Amma wasu daga cikin mabiyansa (a) basu ji dadi ba, daga cikinsu akwai Kaisa dan Sa’ad dan Ubada daya daga cikin kwamandojin rundunarsa.

A lokacinda kais ya kammala jin wannan khudubar, ya ji sakonni masu sanya zuciya ta yi zafi. Ya ji zafi sosai, to amma yaya zai yi. Shugaba ne wanda ba’a saba masa ne ya fadesu.

Amma duk da haka jikinsa yayi sanyi, sannan ya shiga tunana yana cewa ta yaya shugaban shiriya zai sulhunta da shugaban bata. Yana son ya daga kafarsa amma ya kasa, saboda wannan khudubar bai kashe jiki. Daga nan sai ya fashe da kuka yana rera wasu kasidu yana cewa:

Labarin ya zo mani Ina kan kasa mai tudu-Kan Cewa Limamin gaskiya ya kasance  mai Sulhuntawa.  

Da ga nan sai Kais ya juya wajen sojojinsa ya ce masu. Ku zabi dayan biyu, ko yaki ba tare da limami ba, ko kuma yin bai’a  batacciya. Sai suka amsa masa da cewa, mun zabi yaki ba tare da shugaba ba.

Daga nan sai suka tunkari wasu daga cikin sojojin sham suka fara dukansu da takobi, har saida suka kawar da su daga sahunsu. A lokacinda Mu’awiya ya ga haka sai hankalinsa ya tashi, ya kuma aikawa Kais dan Sa’adu dan Ubada yana gargadinsa yana kuma barazana a gareshi. Sai Kais ya ce, wallahi ba zamu hadu ba sai tare da takobi da mashi a tsakanimmu.

A lokacinda Mu’awiya ya debe kauna daga shawo kansa, sai ya sake aika masa sako yana gargadinsa kamar yadda ya zo a cikin wannan wasikar.

(Bayan haka, kai bayahude ne, zaka halaka kanka, ka kasheta kan abinda ban aka ba. Idan daya daga cikin bangarori ya sami nasara, zasu yi watsi da kai, idan kuma mafi ki a gareka ne ya sami nasara zai yaudareka, ya kuma kashe ka, hakika mahaifinka, ya fidda bakansa ya kuma yi harbi ba tare da samun bararasa ba, yayi kuskure sannan mutanensa suka yi watsi da shi, sannan mutawa ta riskeshi yana kaskantacce kuma a bakwanta. Wassalam).

A lokacinda kais ya karanta wasikar sai ya amsa masa da cewa: (Kai gunki ne dan gunki, ka shiga musulunci ba da sonka ba, sannan ka jawo rarraba a cikinsa, kuma ka fita daga cikinsa da sonka, Saboda Allah bai sanya maka rabo a cikinsa ba, musuluntarka daga baya baya ne, kuma munafurcinka bai tsinana kome ba, baka gushe ba kana mai yakir Allah da manzonsa, kuma kai kungiyace daga kungiyoyin mushrikai, kana kana mai adawa ga Allah da manzonsa, da kuma bayinsa muminai.

Kuma ka ambaci mahaifi na, … hakika ka sani kuma mutane sun sani kan cewa ni da babana bama son addinin da ka fito,   kuma masu taimakawa addinin da ka shiga cikinsa (ba da sonka ba ). Wassalam).

Wannan asikar ta bayyana hakikanin Mu’awiya, a lokacinda ya karantata, sai yi fushi yana son maida martani, sai dilan larabawa kuma wazirinsa Amru dan Asi ya hana shi. Yana fada masa cewa: idan ka maida masa martani zai rubuta maka wanda ya fishi tsanani. Amma in ka barshi daga karshe sai ya shiga inda mutane suka shiga. Daga nan sai ya amince da ra’ayin dan Asi, sai ya dakatar da mayarwa Kais wasika.

Amma ya rubuta masa wasika, yana (Bisa shugabancin wa kake yaki? Hakika wanda kake biyayya gareshi ya yi mani bai’a.).

Kais ya ki amsa masa, daga karshe sai ya aika masa takarda, tare da bukatar ya rubuta duk abinda ya ga dama za’a bashi. A nan ne sai kai ya rubuta cewa yana son aminci da kuma amincin mabiyansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted