Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 197

197-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

197-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadah Muttahari, ko cikin littafin mathnawi na maulana jalalluddeen rumi ko cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.

////… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun fara Magana dangane da abinda wasu malaman tarihi suka kawo na sabani tsakanin Imam Al-Hassan da kuma kaninsa Imam Al-hussain(a). Mun kawo dalilai da dama wadanda suke tabbatar da cewa, wadan nan jagorori ba zasu taba samun sabani a tsakaninsu, saboda na farko tsarkinsu, wanda ayoyin alkur’ani da hadisan manzon Allah (s) suka tabbatar da hakan.

Mun kawo aya ta 33 daga cikin suratul AlAhzaba wacce ta tabbatar da hakan. Munce malaman sun yi masa tawile-tawile amma babu wanda ya kai abinda hadisan manzon Allah (s) ingantattu suka tabbatar da cewa wannan ayar ta sauka ne a kan Aliyu da Fatimah matarsa da yayansu Al-Hassan da Al-Hussain(a).

Mun kawo hadisan manzon Allah (s) ingantattu wadanda suka yi magana a kan cewa ya barmana littafin Allah da kuma iyalan gidansa Ahlubaitinsa. A wani hadisin yace ba zasu rabu ba sai sun riske ni a tabkin Alkhauthara, a wani hadisin ya idan kun rike su ba zaku bata ba har abada.

Banda haka mun karanta a tarihin musulunci ko na sunna kan cewa, wadanda suke suke girmamasu hatta a cikin malaman sunnan basu tsira daga sharrin malamai da kuma sarakunan da suke kiyayya da su ba, al-hali Allah ta’ala ya sanya ladar manzancin sa a cikin sonsu, son danginsa. Kuma idan an sosu afaninsa zai koma ne garemu.

Amma a yau zamu fara magana dangane da haduwar Mu’awiya dan Abu Sufyan da Imam Al-Hassan(a) a karon farko, tun bayan sulhun, wasu malaman tarihi sun bayyana cewa sun hadu a Annakhalah da ke wajen birnin Kufa, wasu kuma sun bayyana cewa haduwarsu a cikin birnin Kufa ne.

Wannan haduwar tana da zafi kwarai a cikin zuciyar Imam Al-Hassan (a) wanda a fili ya ga yadda bata ta sami nasara a kan gaskiya, sannan gaskiya ta fadi saboda kha’incin da wasu daga cikin al-ummar kakansa manzon Allah (s) suka yi masa. Ya ji zafi don ganin yadda mu’awiya dan Abusufyan daya daga cikin tulakaa , yentaccen bawan kakansa manzon Allah (s) ya sami nasara a kan sa tare da makirce-makircen da ya kullawa mahaifinsa amirul muminina(a) da farko sannan shi daga baya.

A wannan haduwar ne wannan mu’awiyar ya bayyana irin sharrin da ya boyewa musulmu a cikin zuciyarsa wanda bai bayyana shi sai a lokacinda ya sami rinjaye a kansu, a dai dai lokacinda ba zasu iya komawa baya ba. Har’ila yau a wannan haduwar ce Mu’awiya ya bayyana sirrin da ke cikin yakar Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) da yayi, da kuma dansa Imam Al-Hassan(a) a cikin shekaru kumani 5 da suka gabata.

A cikin jawabinsa Mu’awiya yace: Ya ku mutane! Babu wata al-umma da zata sami  sabani bayan annabinta ba, face daga karshe bangaren da yake kan bata ya sami nasara a kan mai gaskiya.) a lokacinda ya fahinci cewa ya bayyana kansa, ya kuma fadi gaskiyar abinda yake kasa, wato ya tabbatar da cewa, shi ne yake kan bata, duk da cewa shi ne ya sami nasara, sai yayi sauri ya gyara, sai yace (sai wannan al-umma).

Daga nan sai ya gabatar da magana mai daci ga mutanen kasar Iraki, ya kuma bayyana masu hakikanin abinda ya sa yake su, kuma shi ne mulki ba neman jinin khalifa Uthman ba, inda yake cewa:

Na rantse da Allah, ni ban yakeku don ku yi sallah ba, ko don ku yi azumi ba, ko don ku je hajji ba, ko don ku bada zakka ba, lalle kuna aikata dukkan wadan nan, amma gaskiyar itace na yakeku ne don in sami iko a kanku, kuma Allah ya bani abinda nakesu ko da kuwa bakwaso. .

Sannan ya kara da cewa: Ku saurara! Lalle dukkan al-kawulan da na amincewa Al-Hassan (a) suna karkashin kafata, b azan cika ko daya daga cikinsu ba.

Daga nan sai ya ci gaba da zagin Imam Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) da kuma dansa Imam Al-Hassan (a) wanda ke gabasa, ya kuma take al-akuwulan da ya dauka masa a kan hakan.

Bayan ya kammala wannan khudubar tasa, wace take daga cikin khudubobi mafi muni a tarihin addinin musulunci, sai ya bukaci Imam Al-Hassan (a) ya hau kan mimbari ya fadawa mutane a kan cewa ya bar masa shugabanci, wasu malaman sun bayyana cewa, Amru dan Asi ne ya ce masa, ya bar Imam Al-Hassan (a) yah au kan mimbari don mutane su fahinci cewa bai iya magana ba, amma sun kuskure.

Saboda Imam Al-Hassan (a) yayi khudubobi sau da dama a rayuwar mahaifinsa Amirul muminina (a), sannan yayi khudubobi bayan shahadar mahaifinsa kuma bayan ya karbi rgamar shugabanci, a cikinsu ya bayyana cewa shi jikan shugaban masu balagha ne kuma dan Aliyu dan Abitalib (a) ne.

Imam Al-Hassan (a) ya haw kan mimbari, mutane sun yi shiru suna son su ji me zai fada, wasu basa son ya yi magana, wasu kuma sona son su ji daga gareshi, musamman bayan mummunar khudunar da Mu’awiya yayi.

Imam Al-Hassan (a) yayi khuduba cika da balagha ta kakansa manzon Allah (s) da mahaifinsa Amirul mumini, ya amnaci abinda ya faru da iyalan gidan manzon Allah (s) bayan wafatinsa, na kwace khalifanci daga hannunsu, da kuma abubuwan da suka biyo bayan, na jarrabawa ga iyalan gidan manzon Allah (s) har zuwa kan Mu’awiya.

Ga Khudaubar kamar yadda ya fadeta. Da farko ga abinda ya fada a gabatarwan Khudubar.

{Godiya ta tabbata ga Allah a duk lokacinda mai godiya ya gode masa, kuma na shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah, a duk lokacinda mai shaida ya shaida masa da hakan, kuma na shaida kan cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, ya aikeshi da shiriya, ya kuma amince da shi a kan wahayinsa, amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma iyalan gidansa.

Amma bayan haka: Wallah na so a ce na wayi gari – da godiyar Allah da ni’amarsa- nani mafi nasihar mutane ga halittun  Allah, ban kasance mai kula wani sharri ga wani musulmi ba, ko kuma ina kulla masa wani sharri ba ko kuma yaudara.

Ku saurara lalle abinda kuke ki na hadin kai yafi alkhairi gareku kan rarrabuwar kai, kuma ku saurar ! Lalle ni ana hanga masu mafi al-khairi a gareku daga abin ku kuke hanga ga kawukanku, kuma kada ku sabawa umurni na, kada ku sabawa ra’ayi na, Allah ya gafarta mani da ku gaba daya, ya kuma shiryatar da ku zuwa ga abinda yake abin so da yarda.

Sannan ya juya zuwa ga mutane yana cewa

Yaku mutane, ku san cewa, tsoron Allah shi ne, abinda mafi wayon masu wayo suke suke so, kuma sabon Allah shi ne abin so mafi wawtan wawaye}.

{Kuma na rantse da Allah da kun nema tsakanin Jaluq (yamma ) zuwa Jaabars (gabas) da ba zaku sami wani wanda jikansa manzon Allah  amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan gidansa ba, ba zaku samu ba sai ni da dan’uwa na Al-Hussain. Hakika kun san cewa Allah ya shiryar da ku ne da kakana muhammadu (s) Allah ya tsamar daku daga bata tare da shi, ya kuma daukakaku da shi daga jahilci, ya daukakaku da bayan kaskanci ya kuma yawaitaku bayan karancinku.

Kuma Lalle Mu’awiya ya yi jayayya da ni a cikin hakki na, nawane ba nashi ba, amma sai na yi dubi a cikin maslahar Al-umma, da kuma kawo karshen fitina, kuma kun kasance kun yi mani bai’a a kan cewa zaku zauna lafiya da wanda na zauna lafiya da shi, kuma zaku yaki wanda na yaka, sai nag a cewa zan zauna lafiya da mu’awiya, kuma an kawo karshen yaki tsakanina dashi, hakika na yi masa Mubaya’a, al-hali ina ganin hana zubar da jinni yafi zubar da shi, ban yi haka ba sai don masalaharku, da kuma wanzuwarku. {Kuma ban sani ba Mai yuwa fitina ce a gareku da kuma jin dadi zuwa wani lokacin}

Kuma Mu’awiya ya riya cewa wai ina ganinsa ya fi ni cancanta da khalifanci, kuma bana ganin kaina na cancanceta ba, yayi karya, mu muka fi cancanta da jagorancin mutane a cikin littafin Allah mai girma da daukaka, kuma daga bakin annabinsa (s) , sai dai, bamu gushe ba, ana zaluntarmu tun lokacinda Allah ya dauki ran annabinsa, kuma Allah ne zai shiga tsakanimmu da wanda ya zalunce mu, ya kuma hau kan wuyoyimmu, ya kuma dora mutane a kammu, ya hanamu rabommu na dukiya, ya hana mahaifiyarmu abinda manzon Allah ya bata, kuma na rantse da Allah ! da mutane sun yiwa mahaifina bai’a a lokacinda manzon Allah (s) ya rabu da su da sama ta basu dinginta (ruwan sama) sannan kasa ta bada albarkanta, kuma da baka isa ka yi kodayinta ba ya kai Mu’awiya.

Amma a lokacinda ta fito daga asalinta, sai kuraishawa suka yi ta jayayya a kanta. Masu kodayinta cikin yentattun bayi da yayan yentattun baya suka yi kodayin samunta, kai da mutanenka, manzon Allah (s) yace: Al-umma ba zata dora wani mutum shugabancinta ba, a lokacinda akwai wanda ya fishi ilmi ba, face al-amarinsu yana komawa baya har sai sun koma daga inda suka baro}.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted