Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 195

195-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

195-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadah Muttahari, ko cikin littafin mathnawi na maulana jalalluddeen rumi ko cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.

////… madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun kammala Magana dangane sharuddan sulhun da Imam Al-Hassan (a) yayi da Mu’awiya.

Mun bayyana cewa  malaman tarihi sun kawo sharudda kimani 11 wadanda suka ce sune sharuddan sulhu tsakanin Imam Al-Hassan (a) da kuma Mu’awiya dan Abu sufyan, don mika masa ragamar shugabancin al-ummar musulmi, da kuma hana zubar da jinin musulmi a tsakaninsu.

Mun bayyaa cewa wasu malamai basu amince da wasu daga cikin sharuddan ba, saboda wasu dalilai. Kuma sharuddan sun hada da cewa, wai Imam Al-Hassan ya bukaci Mu’awiya ya bashi dukkan dukiyan da ke cikin Baitul malin Kufa. Sai kuma bukatar Imam Al-Hassan na Mu’awiya a rika bashi da shi da dan ‘uwansa Imam Al-Hussain (a) albashi na dirhami dubu dari a ko wace shekara.

Malamai sun bayyana cewa, babu bukatar Imam Al-Hassan ya bukaci Mu’awiya dan Abu sufyan ya bashi abinda yake hannunsa, don garin kufa da Baitul malinsa suna hannun Imam (a) don haka baya bukatar ya bukaci Mu’awiya ya bashi abinda ke karkashin ikonsa kafin sulhu.

Sannan, bukatar mu’awiya ya basu al-bashi a ko wace shekara, da shi da dan Uwansa Imam Al-Hussain (a) wani nau’ii ne na kaskasnci wanda bai dace da iyalan gidan manzon Allah (s) ba.

Sannan mun bayyana cewa an yi sulhun ne a garin Maskan da ke cikin kasar Iraki wanda ya sami halattar cincirindon sojoji daga bangarorin biyu. Haka ma mun yi maganar lokacinda aka yi sulhun, inda muka bayyana cewa mafi rinjayen zance ita ce, a cikin watan Jamada Thani na shekara ta 41 bayan hijira. Wanda kuma yake nuna cewa Imam Al-Hassan (a) ya rike khalifancin al-ummar musulmi har na tsawon watanni 6 da yan kwanaki.

 A yau zamu yi Magana kan cewa Imam Al-Hussain (a) kanin Imam Al-Hassan (a), yana tare da yayansa a dukkan matsayin da ya dauka bai kuma taba saba masa kan sulhun da yayi da Mu’awiya dan Abu sufyan ba, kamar yadda wasu malaman tarihi suke son nunawa.

Kuma mun ambaci abubuwan da suka faru, na kha’incin da wasu daga ciki  kwamandojin sojoji da kuma shuwagabannin kabilun larabawa suka yi, inda suka koma bangaren Mu’awiya dan Abusfyan, suka kha’inci Imam Al-Hassan (a), kuma daga cikinsu har da shugaban babban rundunarsa wacce take Maskan, kuma dan amminsa Ubaidullahi dan Abbas. Wanda ya yaudaru da alkawulan da Mu’awiya yayi masa, bayan da aika masa da dinari dubu 500 sannan yayi masa Al-kawalin cika masa idan ya shiga Kufa.

Sannan mun ji yadda wasu daga cikin shuwagabannin Kabilun labarawan Iraki cikin rundunar Imam Al-Hassan (a) suka rubutawa Imam Al-Hassan wasika a asirce, suka fada masa cewa, a shirye suke su kashe masa Imam Al-Hassan (a) ko kuma su kama shi da ransa su mika masa shi, idan ya ga dama. Sannan mu’awiya dan Abusfyan ya Aikawa Imam Al-Hassan wannan wasikar da suka rubuta, don ya tabbatar masa da cewa baya cikin amince hatta a cikin sojojinsa.

Wadan nan al-amura gaba daya, da wasunsu sun faru a gaban Imam Alhussain (a), don haka ya san halinda yayansa Imam Al-Hassan yake ciki. Don haka bai taba saba masa ba, banda haka yana goyon bayansa a dukkan matakan da ya dauka dangane da sulhu da Mu’awiya da sauransu.

Amma wasu malaman tarihin sun kawo wasu maganganu na karya wadanda suke nuna cewa, Imam Alhussain (a) yana da sabani da yayansa Al-Imam Al-Hassan dangane da matsayin da ya dauka kan sulhuntawa  da Mu’awiya dan Abusufyan.

Daga cikinsu akwai Ibn Athir a cikin littafinsa Usdul Ghaba, inda yake cewa: Imam Al-Hussain (a) baya son abinda dan uwansa Imam Alhassan (a) ya yin a sulhu, kuma sun nakaltoshi yana cewa : Ina hadaka da Allah kada ka gaskata mu’awiya ka kuma karyata babanka. Sai Imam Al-Hassan (a) ya amsa masa da cewa, ni na fika sanin wannan al-amarin. JZ 2 Sh 20.

Sun ruwaito cewac, Imam Alhassan(a) ya fadawa dan amminsa Abdullahi dan Jaafaru kan cewa: Lalle ina da wani ra’ayi ina son ka goya mani baya.

Sai Abdullahi yace: menene Ra’ayin? Sai Yace: Ina son komawa madina in zauna a can, in bar mu’awiya da wannan al-amarin, Fitina ta tsawaita kuma an zubar da jinane a cikinta, an kuma yayyake zukunci, an kuma dakatar da kula da mashigar dkafirai,

Sai dan Jaafaru ya goyi bayan ra’ayinsa, yana cewa: Allah ya saka maka da Alkhairik an al-ummar Mohammad (s) ina tare da kai.

Sannan ya aika zuwa Al-Hussain (a) , a lokacin da ya zo, sai yace masa, Lalle iana da wani ra’ayi, inda son goyon bayanka! Sai yace: Menene. Sai ya fada masa, sai Al-Hussain (a) ya tashi yana fushi, yana cewa: Ina neman tsari daga Allah kan kada ka karyata Aliyu (a), a kabarinsa ka gasgata Mu’awiya.

Wai sai Imam Al-Hassan (a) ya tasirantu da maganarsa, ya kuma bayyana cewa: ban   taba yin wani abu ba sai ka saba mani, da sauransu. Wallahi na so na jefaka a wani gida in tsare ka sai na aiwatar da al-amari na.

Sannan a lokacinda Al-Hussain (a) ya ga jajiecewar dan’wansa kan abinda ya tsaida zai aikata sai, Ya kuma dawo, ya yarda da ra’ayinsa yana cewa: Kai ne babba daga cikin Yayan Ali (a) kai ne khalif ana, kuma al-amarina shi ne bin al-amarinka, don haka kai aikata abinda ka ga dama) wannan kamar yadda ya zo cikin littafin Madeinatu Dameshq, JZ13 SH267.

Wadan nan duk karaya ce, babu kanshin gaskiya a cikinsa. Kuma Imam Al-Hussain (a) ya san duk abinda yake faruwa, kuma bai taba sabawa dan’uwansa Imam Al-Hassan(a) a kan wani abu daga cikin al-amuran da ya kuduri anniya zai aikata ba.

Ya kuma dukkan dalilai da suka sa dan’uwansa ga sulhu da Mu’awiya. Kuma yana goyon bayansa kan dukkan matakan da ya dauka. Da wannan dalilin ne, a lokacinda Imam Al-Hassan (a) ya kammala kulla sulhu da Mu\awiya wasu kabilun larabawa sun zo wajen Imam Al-Hussain (a) suna son ya kwace abinda dan’uwansa Imam Al-Hassan (a) ya kulla da Mu’awiya, amma yaki amincewa.

Da ra’ayinsa ya sabawa na dan’uwansa da ya amsa masu, kan bukatarsu. Banda haka bayan shahadar yayansa Imam Al-Hassan a shekara ta 50 bayan hijira, wasu Mabiya iyalan gidan manzon Allah (s) musamman daga kasar Iraki sun rubuta masa wasu kuma sun zo Madina suna kiransa bukatar ya jagorancesu wajen yakar Mu’awiya dan Abu sufyan.

Amma ya amsa masu da cewa: Matukar Mu’awiya yana da rai ba zai yi wani abu na kawo sauyi ba, sai yam utu zai ga abinda za iyi.} wannan kamar yadda ya zo cikin kibatabul Irshad JZ2 SH31. Na sheikh Al-Mufid.

Don haka rashin amincewarsa da yakar Mu’awiya dan Abusufyan, hatta bayan shahadar yayansa Imam Al-Hassan (a) ya nuna cewa, yana kan rayin sulhuntawa da shi, duk da cewa zuwa wani lokaci ne. .

Gaskiya ne sulhuntawa da Mu’awiya, musamman ma bayan ya ki aiwatar da ko daya daga cikin sharuddan da aka cimma da shi, ya kona zukatan Imam Al-Hassan da kuma dan Uwansa Imam Al-Hussain (a). amma me zasu iay yi, tunda yanayin da ake ciki bai basu damar sauya halin da ake ciki ba. Wannan duk ya karyata abubuwan da wadannan malaman tarihi suka kawo na sabani a tsakaninsu. Ko kuma inda suka ce, wai Imam Al-Hassan yace nasa: Ban taba son yin wani abu ba sai ka saba mani) wannan karyace a fili.

Wannan maganar ya tabbatar mana da cewa, wadan nan kissoshi duk karyace, saboda Imam Al-Hassan da Imam Al-Hussain (s) duk sun tashi ne karkashin tarbiyyar manzon Allah (s). Kuma ya bayyana cewa su limamaine a bayansa, ko sun yunkura sun yi fada ko sun zauna, don haka idan Imam Al-Hassan ya yi sulhu bai yi yayi ba, yayi dai dai tunda shi shugabane , sannan idan Imam Al-Hussain (a) ya yunkura yayi yaki da sojojin Yaziz yayi dai dai don manzon Allah (s) ya ce shi shugaba ne.

Don haka tarbiyyan da wadan nan limamai suka samu daga wajen kakansu manzon Allah (s) da kuma mahaifinsi Amirul muminina (a) da mahaifiyarsu Fatimah Azzahra (s) ya kai matsayinda ba zasu taba sabawa juna ba. Kamar yadda jikan Imam Al-Hussain (a) Imam Muhammad Bakir (a) yake bayyana irin yadda kakansa Imam AL-Hussain yake girmama Imam Al-Hassan(a) inda yake cewa:

{Al-Hussain (a) bai taba Magana a gaban yayansa Imam Al-Hassan (a) ba, saboda girmama shi} Kamar yadda ya zo a cikin manakib Ali Abitalib. Bayan wannan girmamawar shin zai yu Imam Al-Hassan (a) ya cewa Al-Hussain: Ban taba anniyar yin wani abuba sai ka saba mani ?.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted