Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 195

195-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadah Muttahari, ko cikin littafin mathnawi na maulana jalalluddeen rumi […]

Araqchi Ya Ce: Iran Ta Dogara Ne Da Al’ummarta Don Haka Zata Kare Musu Hakkokinsu

Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Sun dogara da al’ummarsu kuma ba za su yi watsi da hakkokinsu ba Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Haƙƙoƙin Iran da mutuncin al’ummar kasar ba za a iya yin sulhu a kansu ba, yana mai jaddada jajircewar Jamhuriyar Musulunci ga ikonta da kuma dogaro […]

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Musanta Karyayyakin Da Ake Yadawa Kan Iran

Ministan Harkokin Wajen Iran ya musanta ikirarin kafofin watsa labaran ‘yan sahayoniyya, yana cewa: Ba a aiwatar da hukuncin kisa kan wani ba Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani ga karya da rahotannin kafafen yada labarai na ‘yan sahayoniyya suka yada kan Iran, yana mai ikirarin cewa labaran da ake yadawa […]

Dr Larijani Ya Tattauna Da Shugabannin Kungiyar Hamas A Birnin Doha Na Qatar

Tattaunawa tsakanin Dr Larijani da shugabannin Kungiyar Hamas a birnin Doha kan ci gaban yankin Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya gana da wasu shugabannin Hamas a birnin Doha na Qatar, domin tattauna sabbin ci gaban siyasa da na fili a yankin, musamman hare-haren da ake ci gaba da kai wa yankin […]

Shugaban Kungiyar Hamas Ya Karyata Cimma Matsaya Kan Karbe Makaman Kungiyarsa

Shugaban kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Babu wata shawara da aka yanke na karbe makaman ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa Shugaban Kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana shigar Fira Ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda Kotun Laifuka ta Duniya ke nema ruwa ajallo, a cikin abin da ake kira “Majalisar Zaman Lafiya” a matsayin “wasan kwaikwayo […]

Iran : Shirin makami masu linzami ba zai taba kasancewa a teburin tattaunawa ba

Sakataren Majalisar Tsaron Iran, wani reshe na Majalisar Tsaron Kasar ya ce karfin makamai masu linzami na Iran “layi ja” ne da ba za a taba sanya shi a teburin tattaunawa ba. Rear Admiral Ali Shamkhani, ya bayyana hakan ne a gefen taron tunawa da zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci da aka gudanar jiya […]

Duniya na taya Iran murnar cika shekaru 47 na nasarar juyin juya hali

Shugabannin kasashen duniya da manyan jami’ai na ci gaba da aikawa da sakonnin fatan alheri ga Iran a game da bikin cika shekaru 47 da samun nasarar Juyin juya halin Musulinci. Shugaban Nicaragua Daniel Ortega ya fitar da wata sanarwa yana taya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, Shugaba Masoud Pezeshkian, da […]

Congo ta musanta mika dimbin albarkatun ma’adinanta ga Amurka

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC) ta musanta cewa ta mika dimbin albarkatun ma’adinai ga Amurka, bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta bai wa Washington damar samun albarkatu irinsu jan karfe, cobalt, coltan, da lithium. ‘Ba abunda muka sayar,” in ji Ministan Ma’adinai na kasar Louis Watum a taron Ma’adinai na Afirka da aka yi […]

An bude taron majalisar zartaswa ta AU

An bude zaman taro na 48 na majalisar zartaswa ta kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Taron na kwanaki biyu da aka fara jiya Laraba, wanda yake samun halartar ministocin harkokin waje daga kasashe mambobin kungiyar AU a karkashin tsarin taron kolin kungiyar karo na 39, […]