188-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin siarar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun fara Magana kan siyasar Iyalan gidan manzon Allah (s) a gaban irin ta’asan da Mu’awiya dan Abusufyan ya aikta da shi da ma’aikatansa.
Da farko mun bayyana matsayinsu dangane da khalifancin manzon Allah (s) a wajensu. Inda muka kawo maku jawaban imam Ali (a) da maganganunsa, wadanda suna nena cewa Khalifanci a wajensu ba ita ce manufa ba, kuma idan ba don tabbatar da adalci, da tsaida gaskiya da taimakawa raunana ba, basa bukatar Khalifanci. A duk lokacinda tabbatar da wadan nan al-amura ba za su sami ba, to khalifanci bai da wata kima a wajensu.
Mun bada misalai da dama, inda Amirul muminina (a) yake Magana a kan haka. Mun bayyana cewa da ya so da ya zama khalifa na ukku, amma sharuddan da shugaban kwamitin mutane 6 wanda khalif ana biyu ya dora a kansu wato Abdurrahman dan Auf, ya hanashi amsa masa. Don yace sai ya amincezai tafi a kan sirar shaikhaini, wato Abubakar da Umar.
A wani wani yana Magana kan cewa ya san makiyansa suka masa kaidi amma shi ba za iyi masu irin abinda suke masa ba, don ya san cewa kariya da kha’inci da yaudara duk suna kaiwa ga wuta, amma makiyansa kuma hanyar ce suka dauka don cutar da shi.
Mun bayyana cewa siyasar Ahlul Baiti (a) babu karya ko yaudara a cikinsa ta, kuma basa Kha’inci.
Imam Ali(a) ya ce: Kha’inci, yaudara karya duk suna kaiwa ga wuta, don haka su a matsayinsu na wakilan Allah a kan doron kasa ba zasu aikata haka ba. Don dukkaninsu hanyoyin wuta ne kuma ba zai kai wanda yake aikatasu zuwa ga yardar Allah ko kuma shiga Aljanna ba.
A wani wuri ya nuna cewa Mu’awiya bai fi shi wayo ba amma shi yana tsoron Allah ba zai aikata abinda Mu’awiya yake aikatawa don kokarin hawa kan kujerar shugabancin al-ummar Musulmi ba, don haka ya zabi su yi masa Kaida, duk da cewa sun san ya san suna masa kaidi, amma ba zai mayar masu da irin ayyukansu ba.
A wani wuri ya fadi cewa, ba don tsoron Allah ba da ya zama mafi iuya Kaida a cikin mutane. Yace mu’awiya bai fishi wayo ba, sai shi ba zai yaudari wani ba, ko yayi masa karya kuma kuma yayi kha’inci ba.
Haka ma dansa Imam Al-Hassan ya fadawa Abdullahi dan Sard daya daga cikin sahabban manzon Allah (s) wadanda ba sa son sulhun da Imam Hassan (a) yayi da Mu’awiya dan Abu sufyan ba, kan cewa ya yi haka ne don hana zubar da jinin musulmi, sannan ya ce masa ya san abinda basu sanin ba.
Dangane da Khalifanci yana cewa
{Ya Ubangiji ka san cewa, (Jayayyan da na yi Abubakar kan shugabanci) ba gasa nake da shi wajen neman shugabanci ba, ba kuma don neman wani abu na duniya ba, said ai don mu mayar da alamun addininka da bayyan gyara a bayan kasa, sannan wadanda aka zalunta daga cikin bayinka su Aminta, da kuma tsayarda abinda aka kawar da iyakokinka.}.
Don haka saboda wadannan abubuwan da ya ambata ne ya nuna fushinsa ga Abubakar ya kuma ki yi masa bai’a. Sannan ya yi ambaliyar hujjoji wadanda suke tabbatar da hakkinsa na Khalifancin al-ummar manzon Allah (s).
A wani hadisi da muka kawo a baya manzon Allah (s) yana fadawa Ali(a) kan cewa {Ya Ali! Kai kamar Ka’aba kake, za’a zo maka amma baka zuwa wajen wani, idan wadan na mutane suka zo suka mika maka ita (khalifancin ) ka karba idan basu zo ba kada ka je wajensu(kana neman shugabanci)}.
Don haka wajibi ne ga musulmi su bi iyalan gidan manzon Allah (a) su sallama masu shugabanci, don su yi hukunci da littafin Allah a cikinsu. Don su Ahlul Baiti su maidasu kan hanyar gaskiya. Sai dai mutane basu koma ga iyalan gidan manzon Allah (s) a bayans aba. Duniya ta rude su. Shugabancin duniya ya yi dadi a garesu. Sun bi son zuciyarsu sun kuma kwace al-amuran shugabanci daga ma’abutansa. Wato sun sanya shi a inda bai cancanta ba.
Wannan musibar daga baya ta game dukkan al-ummar Musulmi a zamanin har zuwa gada dayan tarihin addinin musulunci zuwa yanzu.
Sanna mun bayyana cewa manufofin iyalan gidan manzon Allah (s) a shugabanci su ne tabbatar da na farko Adalci a cikin al-ummar manzon Allah (s). Kamar yadda Allah ta’ala yake nufi, kamar inda yake cewa {Ya dawudu ! Lalle mun sanyaka khaifa a bayan kasa, don haka kayi hukunci tsakanin mutane da gaskiya, kada ka bi son zuciya, sai ya batar da kai daga tafarkin Allah}
A wata ayar yana cewa {Kuma idan zaku yi hukunci tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci}
Har’ila yau an kawowa Amirul muminina (a) karar daya daga cikin ma’aikatansa, wanda bai yi hukunci da adalci a cikin hukuncinsa ba, sai ya tube shi nan take ya kuma bayyana cewa {Ya Ubangiji kai ne mai shaida a kaina da kuma kansu, Lalle ni bai umurcesu su zalunci halittunka ba, ko barin hakkinka ba}.
A wani hadisin Imam Assadik (a) yana cewa {Ku ji tsoron Allah ku yi adalci, sannan kuna aibata mutanen da basu yi adalci ba}.
Lalle jin dadin ko wace al-umma yana tare da adalcin shuwagabanninta, idan sun yi adalci a cikin mutane, zasu sami yelwa da jin dadi, idan kuma zalunci da danniya sun yadu a cikinta, zata hadu da musibu daban daban, wadanda suka hada da rashin zaman lafiya da tashe-tashen hankula.
Saboda wannan dalilin ne addinin musulunci yake son shuwagabannin al-umma su kasance daga cikin salihan bayi masu tsoron Allah. Amintattu a kan kudaden jama’a da ke shiga hannunsu.
Don shugabanci yana da wuya, ga wadanda basu da tsarkin zuciya, kuma su kadan ne a cikin al-umma..
Yana daga cikin siyasar Ahlul baiti (a) daidato a cikin mutane wajen rabon kudade. Addinin musulunci ya kodaitar wajen rabon dukiyar Jama’a , dai dai tsakanin mutane, fiye dukkan addinin da suka gabata. Kuma kamar yadda muka fada a cikin shirimmu da ya gabata, Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) ya aiwatar da wannan a cikin al-umma a cikin shekaru kimani 5 da ya sami damar iko a ka al-ummar musulmi.
Sannan saboda wannan ne larabawa suka kyamaci gwamnatinsa. Harma wasu daga cikinsu suka kafa runduna suka yakeshi suka kuma halaka a hannunsa. Banda haka ya umurci ma’aikatansa su yi raba dai dai a cikin mutane, daga Baitul malin musulmi.
Kamar yadda ya zo a cikin wannan wasikar da ya Aikawa daya daga cikin ma’aikatansa.
{Ka tausawa mutanenka, ka sake fuskanka a gabansu, .. ..har zuwa ida yake cewa- ka dai dai a tsakaninsu hatta a kallonka a nunawa da kuma gaisuwa. Don kada manya-manyan mutane su yi kudayin cikin sa ka ka zalunci mutane. Sannan kada raunana kuma su debe kauna daga adalcinka,}.
Wannan siyasa ta daidaito tsakanin mutane da kuma adalci ne, ya ingiza wasu daga cikin sahabban manzon Allah(s) suka ki shi, suka kuma kulla masa sharri daban daban.
Idan baku manta ba, a lokacinda ya karbi khalifanci a madina ya shiga Baitul mali ya sami kudade, ya kuma rabawa mutane, daidai , ta yanda kowa ya sami dinara uku uku. Ya daidaita tsakanin bayi da iyayen gidajensu. Zubair Sahabin manzon Allah (s) kuma daga cikin wadanda suka yi hijira. Ya halarci yakin Badar da uhudu, kamar yadda ya bawa bawansa haka ya bashi.
Wannan yayiwa mutane nauyi a lokacin, musamman bayan an dauki shekaru masu yawa khalifofin da suka gabace shi suna rabon dukiya da wani tsari daban. Wannan kuma saboda basu fahinci manufar zuwan addinin musulunci da kuma abinda Allah yake nufi da adalci ba.
Imam Ali (a) baya Fifita balarebe kan wanda ba balarabe ba, hakama baya Fifita shuwagabannin kabilu kan yan kabilansa a rabo ba. Su shuwagabannin kabilu suna son ya zama rabon yan kabilarsu gaba daya a basu sannan ya bawa kansu abinda suka ga dama, sannan a cikin yan kabilarsu kuma su zabi wanda suke so su bashi wanda kuma basu so bas u hana shi. Ko kuma a rabon tun asali a warewa shuwagabannin kabilu rabo na musamman. Duk wannan ya sabawa rabon dukiyar jama’a a addinin muslunci bane.
Don tare da rabo cikin adalci ne kawai ake iya kawo karshen talauci a cikin mutane. Wanda Amirul muminina Aliyu dan abitalib (a) ya sami nasara yin haka a cikin lokacinda da ya rike khalifanci na shekaru 4 da watannin 9. Ya shafe talauci kwata kwata a cikin daular musulunci, sai wadanda bai san da samuwarsu ba bai san suna cikin talauci ba.