Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 172

172-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda

172-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddin Romi. Ko kuma dai cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.

///…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatima (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata yi magana dangane da iyayen Mu’awiya dan Abusufyan, wato Abusufyan da Hindu. Inda muka bayyana cewa sun yaki manzon Allah (s) na tsawon kimani shekaru 21 a rayuwar sa na yada addinin Musulunci a Makka da Madina, har zuwa lokacinda ya fi karfinsu ya kwace birnin Makka a shekara ta 8 bayan hijira.

Basu musulunta ba saida suka ga cewa ba zasu tsira da ransu ba, an kama Abusufyan kafin manzon Allah (s) ya shiga Makka, an kawoshi gabansa, ya bukaci ya busulunta yaki, sai da ga cewa za’a kasheshi sai yace ya mika kai. Don haka ne ma ya sanya shi cikin wadanda ake kira ‘Mu’allafatu Kulubuhum’ wadanda ake jawo hankalinsu zuwa addinin musulunci.

Abu sufyan ya ci gaba da kasancewa haka har bayan shahadar manzon Allah(s), sannan ya lura cewa akyai sabani tsakanin musulmi kan wanda zai gaje shi. Sai ya zo Wajen Aliyu (a) yana kodaitar da shi ya dauki makami ya yaki Khalifa Abubakarm ya yi alkawalin zai taimaka masa da mayaka da dawaki. Imam Ali (a) yaki amincwa. Ya kuma zargeshi da sharri wa addinin musulunci. Sannan yayi watsi da maganarsa. Sannan ya rayu har zuwa zamanin Khalifa na Ukku Uthman bin Affan, wanda ya kasance cikin danginsa ne. sai ya fada masu cewa suyi ta jujjuya mulki a tsakaninsu kuma yana rantsewa da abunda Abusufyan yake rantsewa babu aljanna babsu wuta.

Hakama mahaifinyar Mu’awiya Hindu duyar Utbah, tana kiyayya ga manzon Allah(s) da kuma musulmi da musulunci tun kafin a kashe mahaifinta da amminta da kuma dan uwanta a yakin Badar, sai kiyayyar ta karu. A lokacinda manzon Allah (s) ya kwace Makka, ba bu abinda zasu iya yi sai suka mika kai, amma abubuwan da ke cikin zukatansu suna ciki.

Wadannan sune iyayen Mu’awiya dan Abusufyan kuma ya gaji kiyayyar addinin musulunci da manzon Allah (s) da kuma iyalan gidansa, banu hasham.

Mun kuma ka wo Hadisai wadanda suke tabbatar da cewa Mu’awiya zai sami iko a kan musulmi kuma zai yi sanadiyyar shahadar iyalan gidan manzon Allah (s) da dama.

Amma bayan wafatin manzon Allah (s), Khalifa na biyu ya kusanto da Mu’awiya dan Abusufyan, ya bashi gwamnan kasar Sham ya bashi izinin karban haraji da zakka da sanya shi limami mai sallah da mutane da dukka abubuwan da yake bukata na shugabanci.

Sannan al-adar Khalifa Umar ne yakan binciki dukkan ma’aikatansa gwamnoninsa da sauransu a karshen ko wace shekara. Amma baya binciken Mu’awiya dan Abusufyan walinsa a Sham. Wata rana an kawo masa labarin cewa Mu’awiya yana kashe dukiyoyin mutanen Sham yadda yaga dama baya a dalci, yana sanya rigunan Alhariri da dibaji, yana kasa yana kasa. Sai ya basu amsa da cewa ai shi ne Kisran Larabawa.

Sannan a lokacinda ya zo mutuwa ya kafa kwamitin mutanen shida don zaben daya daga cikinsu a matsayin Khalifa, duk da cewa ya san wanda zasu zaba, kuma yana son nisantar da iyalan gidan manzon Allah  daga  shugabanci, sai ya kirasu ya fada masu cewa, idan sun yi hasada a tsakaninsu, idan sun yi sabani a tsakaninsu suka kasa zaben daya daga cikinsu to mu’awiya walin sham yana a madakata, zai ya maganinsu.

Abin tambaya a nan idan da gaske manzon Allah (s) ya rasu yana mai amincewa da su, amma kuma yana jiye masu tsoron cewa Mu’awiya yana iya kwace Khalifanci daga garesu? To me yasa yana daukaka shi, ya barshi yana yin abinda yaga dama? yake kuma kwadaitar da shi khalifanci a kansu?. Da wasu tambayoyi da dama wadanda basu da amsa. 

Wanda ya nuna cewa, da wata manufa ya dora Mu’awiya a matsayin gwamnan sham, kuma daga ciki yana son ya kwace khalifanci musulmi wata rana.

Banda haka mun ga cewa, a lokacin Khalifa Uthman ya ci gaba da daukaka Mu’awiya da bashi karin karfi. Sannan bayanda musulmi suka kasheshi, sai Mu’awiya ya maida kissan Uthman a matsayin makami na yakar Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) wanda musulmi suka zaba bayan kashe Uthman.

Ya zarge shi da taimakawa wadanda suka kashe Khalifa Uthman, ya zargeshi da amintar da makasan Khalifa Uthman. Da haka kuma ya assasa fitina babba wacce ta raba kan al-ummar Musulmi, ya zama mutum na farko wanda ya nemi zama khalifa tare da zare takobi a cikin musulmi. Ya yaki Imam Ali (a) da dansa Imam Al-Hassan(a).

Sannan a lokacinda ya sami nasara a kansu, sai ya bayyana hakikanin abinda yake boye a cikin zuciyarsa, ya fara kokarin shafi addinin musulunci da kuma kashe musulmi masu Ikhlasi, yana kashe iyalan gidan manzon Allah (s) yana dawo da al-amuran Jahiliyya.

Da farko ya bayyana kiyayyarsa ga manzon Allah (s) a boye tare da wasu kebantattun mutanensa. Amma a fili bai isa ya bayyanawa mutane ba. Saboda zasu gane shi da sauri.

Sannan da baya mun bayyana cewa ya fadawa mutanen sham cewa su banu umayya su ne dangin man zon Allah (s), kuma magadansa. Basu gane ba sai bayan da aka kawo karshen daularsu bayan kimani shekaru 80 da wani abu.

Amma malaman tarihi sun bayyana cewa wata rana Mughira dan Shugaba da dansa Matraf sun je wajen Mu’awiya a Sham, don haka daga masaukinsu  yana zuwa wajen Mu’awiya su tattauna, ya dawo yana fadawa dansa Matraf yana kuma yabon Mu’awiya a hankalinsa da wayonsa da kuma tsarin tafiyar da shugabancinsa.

Amma sai wata rana ya dawo daga wajen Mu’awiya da sanyin jiki ya zauna baya magana ya kuma ki cin abinci, daga nan dansa Matraf ya san cewa wani abu ya faru ya kuma bata masa rai sosai.

Sai ya ce masa me yasa ina ganinka cikin bakin ciki da kuma a wannan daren?.

Sai yace: Ya da na ! Lalle na fito daga mafu munin mutane?

Sai yace: Me ya faru?

Ya kebe da Mu’awiya, sai na ce masa: Lalle ka kaiga burinka ya Amiral muminina, da ka dan kwatanta adalci, ka dan aikata alkhairi, ga shi tsofa, da ka dan dubi yadda zaka sada zumunci da yan’uwanda Banu Hashin, ka sada zumunci da su da yana da kyau. Kuma wallah a halin yanzu basu da wani abu da zaka ji tsoronsu da shi.

Sai ya ce mani: Faw faw, dangin taim wato (Abubakar) ya yi shugabanci, yayi adalci yayi abinda yayi, na rantse da Allah yana mutuwa aka manta da ambatonsa, sai dai a ce Abubakar, sannan dangin Adiy (wato Umar) ya yi shugabanci ya yi kokari, na shekaru goma, wallahi yana mutuwa aka daina ambatonsa sai dai wani ya ce Umar, sanna dan’uwammu Usman ya yi shugabanci, mutum wanda babu wanda yake da dangi Irinsa, yayi abinda zai yi, sai aka kashe shi, na rantse da Allah shi ma yana mutuwa aka daina ambatonsa, sai dai wani ce Uthman, amma ga dan Abu Kabshata nan (yana nufin manzon Allah(s) ana ta ihu da sunansa ko wace rana har sau biyar . Ana cewa Ashhadu anna muhammadn Rasulullah, wani aiki ne kuma ya rage, wani Ambato ne mai dawwama ya fi, bayan wanna? Kaiton ka, in banda turbudewa turbudewa?. Wanna kamar yadda ya zo a cikin sharhin Nahjul Balagha na Ibnu Abul Hadid kenen, JZ 5 Sh 130.

Wannan a fili yake nuna rashin amininsa da kuma kiyayyar da Mu’awiya yakewa manzonAllah (s). Baya son ya ji ana ambatun manzon Allah (s) sau 5 a ko wace rana a cikin kiran sallah. Da kuma yana iyawa da ya hana ambaton manzon Allah (s) a cikin kiran sallah, amma al-amarin ya fi karfinsa.

Kuma saboda kinshi, sai da wani lokaci ya dauki kwanaki 40 baya salati ga manzon Allah (s) da aka tambayeshi abinda yasa ya bar yin salati, sai yace : ba abinda ya hana ni sai don kada wasu mazaje su daga hancinsu don girman kai.  Wannan kamar yadda yazo cikin littafin . Nasa’ihul Kafiya SH 97.

Na biyu kuma Ma’awiya yana shafe haddi na addinin musuluni ya ki aiwatar da shi, ko su. Bai kuma himmatu da aiwatar da su ba. Kamar yadda wata rana aka kawo masa marayi ya yanke hannayensu, sannan wani daga cikinsu ba’a yanke masa hannunsa ba,

Kafin a yanke sai ya rera wata kasida yana cewa.

Dama ta, ina neman tsaronta da afwarka ya Amiral mumunina, don kada ta gamu da wurin da zai munanata.

Hannuna, tana da kyau da an suturceta, … har zuwa karshen baitocin. Sai wadan nan kalmomin suka shiga zuciyar Mu’awiya, sai yace to yaya zanyi da kai an kaste hannun yan uwanka barayi? Sai mahaifiyar Barawon tace: Ya amiral muminina ! ka sanya shi cikin zunubanka wadanda zaka tuba daga barinsu. Sai Mu’awiya ya ce masa ya tafi. Kuma ba shi ne hadda na farko wanda Mu’awiya ya yi watsi da shi ba.      

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted