183-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahida Murtadha Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan mansu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma ciki sirar Imam Al-Hassan Almujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku. Mun bayyana yadda Manya-manyabn sahabban manzon Allah (s) da kuma sauran manyan mutane suka yi inkarin abinda Mu’awiya dan Abusufyan yayi na maida Ziyar dan Sumayya dan’uwanda.
Daga cikin mun ambaci Imam Al-Hassan da kaninsa Imam Al-Hussain (s). Sannan Abu Bakrata dan Uwan Shi Ziyad da, Abul Aryan wani mawaki sanenne a zamanin kuma mai Magana, wanda Ziya rya bashi dinari 200 don rufe bakinsa kuma ya amince Abdurrahman dan Marwan Dan Hama, da sauransu.
Sannan mun fara Magana a kan Ma’aikatan Mu’awiya dan Abusufyan , wadanda suka kama masa ayyukan shugabanci a garuruwa daban daban. Daga cikin mun fara maganar Samrata dan Jundubin. Wannan sahabin manzon Allah (s) amma wanda yayi masa rashin ladabi, har saida manzon Allah (s) yayi fushi da shi/
Mun bayyana rashin ladabin da yayi masa kann cewa, wani mutumin Madina wato Ansar ya kai karar Samrata a gaban manzon Allah (s) kan yana shigar gonarsa ba tare da izini ba saboda wata itaciyar dabinonsa guda wacce take kusa da gonansa.
Manzon Allah (s) ya kira Samrata dan Jundubin y ace masa ya sayarwa mutumin Ansar itaciyar dabinonsa ya karbi kudinsa. Sai Sameata y ace ba zai Sayar ba, sai Manzon Allah(s) yace masa to shi ya sayi gonan mutumin Ansar ya bashi kudinsa shi ma Samrata yace ba zai saya ba. Sai manzon Allah (s) yace masa Ka bani dabinon ni kuma na yi maka lamunin zaka sami Aljannah shi ma Samrata ya ce ba za iyi ba. A nan sai manzon Allah (s) yayi fushi da shi ya kuma fadawa mutumin ansar kan cewa yaje ya sare itacen dabinon saboda bai da hakki a kuma a kanta.
A wannan hadisin mun ji yadda Samrata dan Jundubin yayi rashin labadi ga manzon Allah (s), sannan ya ki amincewa da hatta al-jannan da yayi masa al-kawali kan iyaciyar dabino guda. Sannan manzon Allah(s) ya ce a sare dabinon ba tare da an biyashi ba kome ba kuma ya rasa al-janna.
Daga nan zamu Fahinci cewa Samrata dan Jundubin munafuki ne, wanda baya ganin manzon Allah (s) da mutunci. To wannan mutum yana daga cikin wadanda mu’awiya ya dauka a matsayin gwamnoninsa a lokacin sarautarsa.
Wato abinda ya faru ne, da farko Mu’awiya ya tura Ziyad dan Sumayya a matsayin walinsa ko gwamnansa a Basra na kasar Iraki, daga baya ya hada masa, Basra da Kufa gaba daya. A lokacinda Ziyar zai bar Basra ya koma Kufa da zama sai ya nada Samrata dan Jundubin a matsayin Walin Basra. A nan ne Samrata ya nuna keshasewar zuciya na kashe Shiar Aliyu dan Abitalin ko shi’ar iyalan gidan manzon Allah (s) duk don neman Yardar Ziyad da kuma Mu’awiya dan Abusufyan.
Daga karshe mun bayyana cewa Samrata dan Jundubin yana daga cikin sojojin da Ubaidullahi dan Ziyad ya tura zuwa Karbala inda suka yaki Imam Al-Hussain jakan manzon Allah (s) suka kashe shi da shi da Sahabbansa kima 72 a ranar 10 ga watan Muharram na shekara ta 61 bayan hijira.
Kafin haka malaman tarihi sun bayyana cewa Samrata dan jundubin ya kasance yana saida giya bayan an haramtata. Labari ya kaiwa khalifa na biyu Umar dan Khaddab, a lokaci, sai yace Allah ya la’ani Samrata. Manzon Allah (s) yace: An haramtawa yahudu kitse sai suka saida ita, kamar yadda Ahmad bin Hambal ya kawo a cikin musnadinsa JZ na 1 sH 25.
A cikin ruwayar Zamakhashari yace: Allah ya la’ani yahudu an haramta masu kitse sai suka kawatata suka saida ita) wato sai suka narkar da kitsen suka saida ita. Amma a lokacinda Mu’awiya dan Abusufyan ya karbi iko da daular musulunci, sai ya sanya Ziyad dan Sumayya a matsayin walin Basra, sai ya sake hada masa da Kufa, sai Ziyad ya sanya samrata dan Jundubin a matsayin wakilinsa a kan Basra, shi kuma ya koma Kufa.
A lokacinda samrata ya sami iko da Basra ya kashe bayin Allah da dama. Mohammad dan Sulaim yace: Na tambayi Anas dan Sirin Al-Ansari, kan cewa shin Samrata dan Jundubin ya kashe wani a lokacinda ya samu iko da Basra?, Sai Anas ya zabura a cikin fushi yana cewa ‘shin akwai wanda zai iya iyakance yawan mutanen da Samrata ya kashe?.
Anas ya ci gaba da cewa: A lokacinda Ziyad ya sanya shi wakilinsa a Basra, ya kashe mutane kimani 8000, sai wata rana Ziyad ya tambaye shi, shin (samrata) kana jin tsoron a cikin wadanda ka kashe, ka kashe wani wanda bai cancanci kisa ba? Sai amsa da cewa: Ai ko da na kara kashe wasu kamarsu ba zan ji tsoron kome ba.) wannan kamar yadda ya zo a cikin Al-Kamil Fittarikh na JZ 3 Sh183. Da kuma Tarikhul Umam Walmuluk JZ 6 SH 132.
Abu Sawwar Al-Adwi yace: Samrata ya kashe mutane 47 daga cikin mutane na duk sun haddace Alkur’ani a rana guda. Har’ila yau Auf yana fadar laifuffukan Samrata, sai yace. Wata rana samrata ya fito daga Madina da tawagarsa, sai ya bi ta gidajen Banu Asad, sai wani mutum daga cikin banu Asad ya fito kan titi sai wani mutum daga cikin tawagar samrata na gaba-gaba, ya buge shi da wani Makami, a lokacin Samrata ya isa wurin ya ga mutumin cikin jininsa sai yace: Menen wannan? Sai aka ce ma tawagar Amir ne ta gaba gaba ce ta ji masa ciwo. Sai yace: Idan kun ji labarin muna tahowa ku kaucewa kan masummu. Sai ya wace. Wannan kamar yadda a cikin Alkamil Fittarikh JZ 3 Sh 183. Sannan sharafuddeen ya kawo shi a cikin Fusulul Muhimmah SH 122.
Wata rana an tambayi Samrata me za fadawa Ubangijinka a gobe, kiyamah, a kawo maka mutum a ce maka shi ba Kharijene ne, sai ka ce a kasheshi? Sannan a zo maka da wani a ce maka wanda ka kashe din ba bakharije ne ba, mun kuskure, amma ga wannan wanda muka kawo a yanzu shi ne bakharije, sai shim aka ce a kasheshi. ?
Sai samrata ya bude bakinsa yace: Menene laifi a cikinsa? Idan shi dan Aljanna ne ya wuce zuwa Al-janna, idan kuma dan wuta ne shi ma ya wuce zuwa wuta.
Wannan yana nuna yadda yake keshe mutanen da aka kawo masa ba tare da bincike ko kadan ba.
Sannan wata rana Hassan Albasri ya ce: Wani mutum daga lardin Khurasan ya zo basra ya je ya bada zakkan dukiyansa da yake cikin baitul Mali sannan ya karbi takarda daga ma’aikatan baitul Mali kan cewa shi ba bakharije ne ba. Sai ya shiga masallaci ya yi raka’o’I biyu. Sai jami’an Samrata suka kama shi tare da tuhumarsa da cewa shi Bakharije ne, sai Samrata ya bada umurni aka kashe shi. Sai daga baya aka ga takardan da ya karbo daga baitul mali kan cewa ya baranta daga Khawarijawa, Samrata ya rika ya kashe shi.
Sai Abubakrata dan uwan Ziyad dan Sumayya wanda muka yi maganarsa a baya, ya dauki takardan barrantar mutumin ya je wajen Samrata y ace masa: Ya kai samrata baka ji abinda Allah yake cewa ba? {Hakika wanda ya bada zakka ya rabauta?. Kuma ya ambaci sunan ubangijinsa sannan yayi sallah?} sai Samrata yace, (Dan uwanka (Ziyad) ne ya umurce ni in yi haka.).
Wannan mujrimin ya luzumci Ziyad, a lokacinda ya halaka, sannan dansa Ubaidullahi ya karbi shugabancin Kufa karkashin Yazid dan Mu’awiya, wanda shima ya halaka. Sai Samrata dan Jundubin ya zama shugaban yansandan Ubaidullahi dan Ziyad, kuma yayi tarayyar da shi wajen aiki mafi munin sabo a tarihin bil’adama, wanda kuma shi ne kashe baban Aubdullahi Imam Al-Hussain Jikan manzon Allah(s) dan Fatimah (s) a ranar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira.
Samrata ya kasance yana kodaitar da mutane wajen yakar Imam Hussain (a) da kuma kashe shi.
Daga karshe an yi wani lokacinda aka kawowa Samrata mutane musulmi, sai ya tambayesu, menene addinanka, sai yace: La’ilaha Illahhahu, kuma na baranta daga haruriyya (wato Khawarijawa) amma ya bada umurni a kasheshi. Sai ya kashe mutane 20 a zama guda.
Daga karshe bayan da Mu’awiya dan Abusufyan ya tubashi daga kan shugabancin Basra sai samrata yace: Allah ya la’ani Mu’awiyah, wallah da na yi wa Ubangiji biyayya irin wacce na yi wa mu’awiya da ba zai azabtara da ni ba har abada) Kamar yadda ya zo a cikin littafin Sana’i-ulkafiyah SH.54.
Wannan kadan kenen daga ayyukan ma’aikatan Mu’awiya dan Abu sufyan. Dukkan ma’aikatansa masu busassun zuciya ne kamar tasa. Musamman a kan mabiyan Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a), da kuma sauran iyalan gidan manzon Allah (s).
02-Sai kuma Ziyad dan Sumayya, shi ne wali ko ma’aikacin Mu’awiya mafi muni, wanda ya karfafa mulkinsa da cin zarafin mutane da zubar da jininsu. Shi ne ya fara daukar sandar karfe a gaban Mu’awiya ya kuma zare takobi don kare mulkinsa. Shi ne mutum na farko wanya ya kashe mutane a kan zato, kamar yadda Mu’awiya ya umuecesu.
Saboda matsayinsa a wajen Mu’awiya ya kara masa fadin yankunan da yake iko da su, daga Basra ya hada masa da kufa, sannan Sajistan, sannan Farisa sannan Assand sannan indiya. Kamar yadda yazo cikin tarikhin umamma wal-muluk. JZ 6 SH 134.