Search
Close this search box.

Kissoshin Rayuwa 34: Kissar Fatimah Azzahra(s) Diyar Manzon Allah (s)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa. Shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa. Shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin ‘Dastane Rastan’ na Shahid Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin mathanwai na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma dai ciki wasu liattafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahar (s) diyar manzon All..(s) kuma mahaifiyar Alhassan da Alhussan (a) da muke kawo maku, mun tsaya inda muka fara magana dangane da iliminta (s).

Mun bayyana cewa ta sha ilmi daga mabubbukarsa ta farko, wato daga mahaifinta (s), wanda Mala’ika jibirilu yake sauko masa da ilma daga wajen All..T kai tsaye.

Banda haka, mun san cewa ita wani bangare ne na babanta, don haka All..ya bata fahinta irin nasa, a duk lokacinda aka sanar da ita wani abu, to kwakwalwanta da fahintar da All..ya yi mata, yana kara bude mata kofofin wasu ilmin daga abinda aka sanar da ita.

Mun kuma bayyana cewa ta rasu ko ta yi shahada ta bar wannan duniyar bata kai shekaru 20 a duniya ba. Da kuma All..ya bata tsawon rai zuwa shekaru 50 ko 60 tare da damar watsa ilmin da take da shi, da ta cika duniya da nau’o’in ilmi wadanda ta samu daga mahaifinta mabubbukan ilmin wahayi.

Wannan banda ilhamin da All..yake mata kai tsaye daga wajensa, kamar yadda zamu gani a nan gaba. Kuma mun yi magana kan yadda Mala’ika Jibril yake zuwa wajenta bayan wafatin mahaifinta(s) yana fada mata wasu al-amura da suke da dangantaka ta al-ummarsa har zuwa tashin kiyama.  

Amma saboda karancin shekarunta a lokacinda ta bar duniya, ilmi kadan ne masulmi suka samu daga wajenta, ko suka karbo daga wajenta na ilmin da take da shi.

An karbo daga Jabir dan Abdullahil Ansari daga daga manzon All..(s) yana cewa: Lalle All..T ya sanya Aliyu da Matarsa, da yayansa hujjojin All..a kan halittunsa, su kofofin ilmi ne a cikin al-ummata, wanda ya nemi shiriya da su, zai sami shiriya zuwa ga tafarki madaidaiciya.

Kamar yadda manzon All..(s) ya fada a ciki  wannan hadisin, a fili yake tana daga cikin kofofin ilmi a cikin wannan al-umma, amma abin bakin ciki abinda aka ruwaito daga wajenta kadan ne sosai, gashi kuma bata dade ba bayan mahaifinta sai tayi shahada.

Abinda malaman tarihi suka bayyana dangane da ilmin Zahra (s) shi ne cewa, sau biyu ne kacal ta sami damar magana a cikin al-ummar kakanta bayan wafatin mahaifinta(s). Na farko a masallacin manzon All..(s) bayan wafatin mahaifinta inda ta je don kare hakkin mijinta na shugabancin al-ummar musulmi, al-ummar babanta, da kuma neman hakkinta da aka kwace na Fadak da gadonta.

Na biuyu kuma a lokacinda mata a madina suka ziyarceta jim kadan kafin shahadarta.

An dauko daga Tafsir na Imam Askari (a) inda yake cewa: Wata mata ta zo wajen Assidika Fatimah Azzara(s) ta ce mata: Mahaiyata ta tsufa, kuma tana samun matsalolin a cikin sallarta, don haka ta aikoni zuwa wajenki da tambayoyi. Sai Fatimah (s) ta amsa mata tambayoyin fgarko, sai ta sake zuwa karo na biyu, na ukku, har sai da ta kai sau goma. Sai ta ji kunya,ta ce ba zata sake zuwa ba, tace bana son in takura maki ya diyar manzon All..(s).

Sai Fatimah (s) tace: Ki kawo tambayoyinki, ki tambayi abinda kika ga dama. A ganinka wanda aka yi jingarsa, a rana guda don ya dauki kaya mai nauyi zuwa saman gini, amma ladarsa dinari dubu 100 ne, shin zai yi masa wuya?

Sai matan ta ce: Aa’aa. Sai (s) ta ce: An dauki jingata a kan amma duk wata matsala,  da abinda ya fi abinda zai cika kasa zuwa Al-arshi na lulu’u, don haka abinda ya fi dacewa shi ne kada hakan ya yi mani nauyi. Na ji babana (s) yana cewa: Lalle malamai masu goyon bayammu za’a tada su ranar kiyama a sanya masu kawa, na darajoji gwagwadon yawan ilminsu, da kuma kokarinsu wajen shiryatar da bayi, wani daga cikinsu za’a kawatashi da haske dubu sau dunu (wato miliyon guda), sannan wani mai kira daga Ubangiji zai yi kira, ya ce: Ya ku wadanda kuke kula da marayu daga iyalan gidan manzon All…(s)…..har zuwa inda take cewa:

Ya baiwar All..Lalle zare daya daga cikin wadannan abubuwan kawa, ya fi abinda rana ta haska a kansa a nan duniya sau dubu sau dubu (wato miliyon).

A wani hadisin wanda Da’awatu Rawandi ya karbo daga Suwaid dan Gaflata, Ya ce:Ali (a) ya gamu da rashin kudi a wani lokaci, sai Fatima (s) ta je gidan manzon All..(s) ta kwankwasa kofa, sai manzon All..(s) ya ce, ina jin kanshin masoyiyata a kofa, ya ke Ummu Aimanu ki je ki duba, sai ta je ta bude mata kofa, ta shigo. Sai ce mata: Kin zo mana a lokacinda baki saba zuwa ba. Sai Tace: Ya manzon All..(s) menen abincin Mala’iku awajen Ubangijimmu, sai yace: Godewa All..sai tace menene abincimmu?

Sai manzon All..(s) yace: na rantse da wanda raina ke hannunsa, ba’a taba kunna wutan girki a gidan iyalan gidan muhammadu (s) na wata ba, kuma zan sanar da ke, kalmomi 5 wadanda Jibrilu(a) ya sanar da ni.

Sai tace: Ya manzon All..(s) menene kalmomin biyar? Sai ya ce: Ya ubangijin mutanen farko da na karshe, kuma ya mafi alkhairin na farko da na karshe, kuma ya ma’abucin karfi mai tsanani, kuma ya mai jinkan miskinai, kuma ya mafi jinkan masu jin kai.

Sai ta koma gida, a lokacinda Aliyu(a), ya ganta, sai ya ce, iyayena fansarki, me ki ka zo da shi ya Fatimah? Sai ta ce: Na je don duniya sai na dawo da abin lahira. Sai Aliyu (a) yace: Alkhairi na gabanki, alkhairi na gabanki,

Ya zo cikin littafin Kafi daga Imam Sadik (a) yana cewa: Fatima (s) ta zo wajen manzon All..(s) tana bayyana masa wasu daga cikin damuwarta, sai manzon All..(s) ya bada  wata takardan da aka yi ta daga rassan itacen dabino, sai ya ce mata: Ka karanta abinda yake cikinta.  Sai ga shi an rubuta a cikinta: Duk wanda yayi Imani da All..da ranar lahira to kada ya cutar da makwobcinsa, kuma duk wanda yayi imani da All..da ranar lahiri to ya girmama bakwansa kuma wanda yayi imani da All..da ranar lahira ya fada alkhairi ko ya yi shiru.

Fatima (s) tana cewa: Duk wanda ya kusanci All..T, tare da tsarkaka bautarsa don shi kadai, All..zai sauko masa mafi kyau daga cikin maslaharsa.

An karbo hadisi daga Fatima (s) diyar manzon All..(s) ta na cewa: na ji babana manzon All..(s) ya na fada a cikin rashin lafiyarsa ta karshe, a lokacin dai sahabbansa sune cike da dakinsa, yace: Ya ku mutane an kusan daukar raina da dauki, kuma na yi maku magana don sauke uzuri daga gareku, ku saurara !, lalle ni ina barin a bayana littafin Ubangijinku (mai girma da daukaka) da dengina iyalan gidana. Sannan ya riki hannun Aliyu(a),  sannan yace: Ga wannan Aliyu ne tare da Alkur’ani.  Alkur’ani ya na tare da shi, ba zasu rabu ba har sai sun riske ni a tabki, sai in tambayeku yadda kuka yi dasu a bayana.

Alkanduzi Alhanafi, ya ce sahabban manzon All..(s) 30 ne suka ruwaito wannan hadisin, kuma lalle da dama daga cikinsu, suna da sanadi ingantacce, ko mai kyau.   A wani hadisin ta na fada (s): Manzon All..(s) ya ce: wanda yayi zobe da Akik ba zai gushe zai yi ta ganin alkairi.

A wani hadisin daga Fatima (s) diyar manzon All..(s) ta ce: Menena amfanin azubi, idan mai azumin bai kiyaye harshensa da jinsa da ganinsa da kuma gabbansa ba?.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments