Iran Da Burkina Faso Sun Sha Alwashin Fadada Alaka Ta Fuskar Kafafen Yada Labarai

Burkina Faso ta bukaci ganin ta karfafa alaka da kasar Iran ta fuskar musayar labarai da raya al’adu na kasashen biyu. Wannan bayanin ya fito bayan ganawar data hada Jakadan kasar ta Burkina Faso Hamadi Kabore da shugaban sashen gidajen talabijin da Radiyo na Iran Dakta Nourusi, a ranar Litini. Sun tattauna kan yadda zasu […]
HKI Tana Cikin Tsaka Mai Wuya Duk Tare Da Goyon Bayan Da Take Samu Daga Kasashen Yamma

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa a halin yanzu HKI bata da karfin kare mutanen kasarta, saboda makaman makiya suna isa har tsakiyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kan’ani yana fadar haka a safiyar yau Litinin, ya kuma kara da cewa hare-haren da dakarun Hizbullah […]
Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 39 A Kudu Maso Yammacin Kasar Pakistan

Yan ta’adda sun kashe mutane akalla 39 a yankin kudu maso yammacin kasar Pakisatan, inda mayakan kungiyar ‘yentar da kabilar baloch’ ko ‘Baloch Liberation Army’ (BLA) na kasar Pakistan ta dauki alhakin aiwatar da ayyukan ta’addancin a yau Litinin. Kamfanin dillancin labaran AFP na kasarn Faransa ya nakalto Shahid Rind kakakin lardin Balochistan yana fadar […]
Malasiya: Babu Bukatar Kasashen Yamma Su Koyawa Musulmi Menene Kare Hakkin Bil’adama Ko Demokradiyya

Farai ministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim ya bayyana cewa kasashen musulmi basa bukatar kasashen yamma su koya masu me ake nufi da demokradiyya ko kare hakkin bil’adama. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Anwar Ibrahim yana fadar haka a bikin bude wani masallaci a birnin Kwalalampo na kasar, ya kuma bayyana yadda […]
Dakarun Al-Kassam Sun Sami Nasarar Halaka Sojojin HKI A Kudancin Gaza

Mayakan dakarun Izzuddin Kasam rahen soje na kungiyar Hamas sun bada sanarwan halaka sojojin HKI a kudancin Gaza, a wani tarkon mayakan da suka fada ciki. Kamfanin dillancin labaran SAMA ya nakalto wani bayanin da dakarun Izzudden Kassam suka fitar a safiyar yau Litinin na cewa, a wannan takon sun halaka ko raunata akalla sojojin […]
Shugaban Kasar Iran Zai Je Kasar Iraki A Tafiyarsa Ta Farko Zuwa Wajen Kasar Tun Bayan Ya Zama Shugaban Kasa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan zai yi tafiyarsa ta farko zuwa kasat Iraki wanda kuma shine tafiyarsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan ya zama shugaban kasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa shugaban zai je kasar ta Irakin ne bisa gayyatar tokwaransa na kasar Abdul-Lateef Rashid. Kafin haka […]
Kissoshin Rayuwa 34: Kissar Fatimah Azzahra(s) Diyar Manzon Allah (s)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa. Shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin ‘Dastane Rastan’ na Shahid Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin mathanwai na Maulana Jalaluddeen […]
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Yaki Tsakanin Gaskiya Da Bata Ba Zai Kare Ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Yaki tsakanin gaskiya da karya ba zai taba karewa ba har abada A yayin da ya karbi tawagar dalibai da sukaziyarce shi domin gabatar masa da ta’aziyyar yuyayin ranar Arba’in ta Imam Husaini jikan manzon Allah {s.a.w} a ranar Laraba da ta gabata: Jagoran juyin juya halin […]
Babban Sakataren Hizbullahi Ya Ce: Juyayin Arba’in Yana Da Alaka Da Juyayin Kisan Gilla Ga Fouad Shukr

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa: Juyayin ranar Arba’in na gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} yana da alaka da kisan gillar da aka yi wa Fouad Shukr Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya tabbatar da cewa: Tunawa da ranar Arba’in ta Imam Husaini {a.s}, alama ce ta sadaukarwa, kin zalunci, […]
Mahukuntan Masar Sun Ce An Kawo Karshen Tattaunawar Tsagaita Wuta A Gaza Babu Cimma Matsaya

Gwamnatin Masar ta sanar da cewa: An kawo karshen zaman tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ba tare da cimma matsaya ba Majiyoyin tsaron Masar sun sanar a cikin daren jiya Lahadi wayewar safiyar yau Litinin cewa: An kawo karshen zaman tattaunawan da aka yi a birnin Alkahira dangane da tsagaita bude wuta a Gaza. Kafofin […]
‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Harba Makami Mai Linzami Kan Birnin Tel Aviv

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa sun harbi wani nau’in makami mai linzami zuwa birnin Tel Aviv da aka kasa kakkabo shi Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun kaddamar da wani hari na ban mamaki da nau’in makami mai linzami na M90 a jiya Lahadi kan birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar […]
Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Sudan Ya Ce: Aiwatar Da Yarjejeniyar Jedddah Ita Ce Mafitar Kasarsa

Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan kuma babban hafsan hafsoshin sojin kasar ya bayyana makomar yakin Sudan Kwamandan sojojin Sudan Janar Abdul Fattah al-Burhan, ya tabbatar da cewa: Yakin Sudan zai ci gaba da gudana har sai an aiwatar da bukatun sojojin Sudan kasar, yana mai cewa, sakamakon zaman dandalin birnin Jeddah na kasar […]
Jagora: Bayanin sirrin yunkurin Imam Husaini a kan bangaren Yazidu ba shi da iyaka

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira gangamin da aka yi tsakanin dakarun Husaini da na Yazidu a matsayin ci gaba da ma’auni a cikin zaman makokin dalibai na ranar Arba’in Hosseini tare da jaddada cewa: Juyin juya halin Musulunci na Iran ya bude wani fage mai fadi da dama a gaban matasa, kuma ya […]
Shaikh Zakzaky: Taro a kan hanyar Karbala hujja ce ta nasarar yunkurin Imam Hussain (a.s.)

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya jaddada cewa duk wani matsayi na goyon bayan Palastinu ya samo asali ne daga tafarkin koyarwa ta Imam Hussain (a.s) . Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya bayyana hakan ne a yayin taron rufe tattakin da aka yi wa taken ‘Kiran Al- Aqsa’ a kan hanyar masu ziyara […]
Nasrallah: Mun Samu Babbar Nasara A Harin Martani Kan Isra’ila

Sakatare-Janar na Hezbollah Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana cewa sun mayar da martani kan Isra’ila dangane da hare-haren da ta kai a yankin kudancin Beirut wanda ya yi sanadin shahadar babban kwamanda a kungiyar Fouad Shokor. Babban makasudin harin na jiya wanda aka kaddamar a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da aka yiwa […]
Iran, Saudiyya Sun Bukaci A Rubanya Kokari Wajen Kawo Karshen Laifukan Isra’ila A Gaza

Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Saudiyya sun amince da cewa, akwai bukatar dakatar da laifukan da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa da kuma kai kayan agaji ga al’ummar zirin Gaza da aka yi wa kawanya. A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Lahadi, Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da takwaransa […]
Mutane miliyan 21.48 ne suka halarci tarukan Arba’in a Karbala a wannan shekara

Miliyoyin Masu ziyara ne daga sassa daban-daban na duniya suka birnin Karbala na kasar Iraki a yayin gudanar da tarukan ziyarar Arba’in na wannan shekara, kamar yadda hukumomi a karbala suka sanar. Wani babban jigo daga cikin masu kula da Hubbaren Sayyiduna Abbas a Karbala ya tabbatarwa gidan talabijin na Press TV cewa, akalla mutane […]
Yan Ta’addan Boko Haram Sun Sace Matafiya Tara A Iyakar Najeriya Da Nijar

Wasu rahotanni sun bayyana cewar mayakan Boko Haram sun sace wasu matafiya a yankin Kumadouku da ke kan iyakar Najeriya da Nijar. Masanin kan harkar tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagàzola Makama ne, ya bayyana hakan inda ya ce lamarin ya faru a ranar 22 ga watan Agusta, 2024. Ta ce ’yan ta’addan su shida […]
Isra’ila Ta Kashe Falastinawa Sama Da 70 A Cikin Kasa Da Sa’oi 24

Falasdinawa fiye da 70 ne suka yi shahada a cikin kasa da sa’oi 24 ad suka gabata, sakamakon hare-haren kisan kare dangin da Isra’ila take kan al’ummar Gaza, kamar yadda majiyoyin kiwon lafiya suka tabbatar. Wani hari ta sama ya faɗa kan wani rukunin gida a unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin Gaza, ya yi […]