A Najeriya ‘yan kasar na ci gaba da mayar da martani kan kisan da da ‘yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir Isa Muhammad Bawa, bayan da ya shafe kusan wata guda a hannunsu.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin mai shekara 72, wanda ya yi fiye da shekara 40 yana sarauta, tare da dansa da kuma wani dan’uwansa.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana matukar kaduwarsa game da kisan da aka yi masa, wanda ya bayyana a matsayin “mummuna dabbancin ba zai wuce ba tare da kakkausan martani ba,” in ji wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar ranar Laraba da daddare.
Shi kuwa tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban Nijeriya a 2023 a jam’iyyar adawa ta PDP, ya soki gwamnatin Nijeriya kan sakaci wurin kubutar da sarkin, kamar yadda ya wallafa a sakon ta’aziyyarsa a shafin X.
“Babu shakka gazawar gwamnati wajen nuna damuwa ko daukar matakan tsaro masu kwari sun taimaka wurin ta’azzarar rashin tsaro a baya bayan nan,” in ji Atiku Abubakar.
Shi ma Peter Obi, dan takarar shugaban Nijeriya a 2023 a jam’iyyar adawa ta LP, ya bayyana damuwa game da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa Sarki Bawa, yana mai cewa “wannan lamari ya sake fito da irin ta’azzarar da rashin tsaro ya yi a Nijeriya, inda mutane masu daraja kamar Sarki za su fuskanci irin wannan wulakanci.”