Turkiyya ta bayyana wani shiri na kasashen Musulmi kusan ashirin na hadin guiwa a game da matsayin Masallacin Kudus.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da keta alfarmar masallacin duk da fishin da kasashen Musulmi ke nunawa game da hakan.
Fraministan Turkiyya Hakan Fidan ya sake nanata rawar da Jordan ta taka a tarihi da kuma ta shari’a a matsayin mai kula da wurare masu tsarki a Gabashin Kudus da aka mamaye kuma ya ce Türkiye ta dauki Masallacin Al-Aqsa a matsayin daya daga cikin wuraren ibada nata.
Mista Hakan ya ce kusan kasashen Musulunci 20 sun tattauna “matakan hadin gwiwa” kan keta haddin Masallacin da Isra’ila ke yi na baya-bayan nan a lokacin wani taron ministoci a birnin Amman, yana mai jaddada cewa bai kamata rikicin yankin ya dauke hankalin duniya daga abubuwan da ke faruwa a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ba.
“A yau, mun halarci wani taro mai tarihi a Amman,” in ji Fidan, yana mai cewa: “An yi musayar ra’ayoyi masu mahimmanci.
Kasashe masu daraja na duniyar Musulunci sun bayyana damuwarsu da kuma fushinsu, yayin da suka kuma tattauna matakan da suka dace, na diflomasiyya da sauran matakan da ya kamata a dauka.”
Ya ce yakin da ke ci gaba da faruwa a yankin Tekun Fasha, da kuma sauyin da aka samu a duniya bai karkatar da hankalin mahalarta daga “matsalar Falasdinu, Masallacin Al-Aqsa, Gaza da Yammacin Kogin Jordan ba.”
“Domin mun san cewa idan aka karkatar da hankalinmu zuwa ga yakin, Isra’ila za ta ga ya fi sauki ta aiwatar da abin da take so a Gaza, a Masallacin Al-Aqsa, da kuma a Yammacin Kogin Jordan,” in ji shi.
Ya kara da cewa Turkiyya da Jordan sun isar da sakon hadin kai ga Kudus da Al-Aqsa a lokacin taron.
Fidan ya kuma ce ya halarci taron ministoci na biyar na “Rukunin kasashen Saudiyya, Turkiyya, Masar da Pakistan, inda ministocin suka tattauna abubuwan da ke faruwa a Gaza da kuma kokarin aiwatar da shirin zaman lafiya.